← Book details Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 90

Sashe 69

Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A da, na rantse na daina shiga alamarin ki da iyalinki, domin dai kin girma, amma zuciyarki ta yara ce. Shin wannan so ne kike wa Alameen ko kiyayya ce? Wannan ba so ba ne. Ba soyayya ce ta uwa ga dan ta ba. Na tabbatar miki in baki yi hankali da rayuwar duniya ba za ki yi nadama, a lokacin da bata da amfani!

Son kan ki yayi yawa Nafisa. Ita uwa har kullum hakuri take da son ranta ta barwa dan ta. Ba don a kan idona kika yi rainon cikin Aminu, kika kuma haife sa a hannu na ba, da sai in ce, ke ba uwar sa ba ce!

Daga haka ta juya ta fita. Hajiya Nafi, ta dago sannu a hankali ta dubi Alameen, ta hadiyi wani daddatan miyau daya makale a makoshinta. Haka sheshshekar kukan Alameen ko daya bai sa zuciyarta ta russuna ba. Ya ce,

“Wallahi Hajiya in kika hanani zan hanu, in kika yanke min hukunci bazan tsallake shi ba komi tsaurinshi. Na rantse da Allah wannan hukuncin da kika yanke a gareni na yin fushi dani ya fi komi tsauri da hatsari agare ni, fiye da rashin soyayyar Intisar!

Ban san me na fada wanda ya bata miki rai ba, ban san laifi na gareki cikin alamarin nan ba. Idan kika ce in barta, daga yau na bar ta har abada! Ko hanyar da ta bi bazan kara bi ba, zan je in lallashi zuciya ta in runguni kaddara, in roki Allah ya cire min kaunarta, in rokeshi gafarar hawayen da kika zubar adalilina. Ni dai fatana ki yafe ni, ki daina fushi da ni, don Allah Hajiya. Ya karasa cikin rishin kuka.�

Ta bude bakinta cikin kakkausar murya tace

“Ameenu! Wane alkawari ka yi mun a dawowar ka daga Miami?�

Ya dago cikin razana da dimaucewa ya ce,

“Eye, naam, wane alkawari ne? Hajiya wallahi na manta.�

Ta yi murmushi ta ce,

“Ka je ka tuna, in ka tuna kazo ka gaya mun sannan ne zaka ji hukuncin da na yanke kan bukatar ka. Ya bude baki zai yi magana ta daga hannu ta daura bisa labbanta ta tace Shhhhhh, bana magana biyu. Na farko dai bazan hana ka aurenta ba akan-kaina, tunda sanda ka je inda take har kuka kulla soyayyar, ina cikin gidan baka yi shawara da ni ba.

Dama kuma daga ku har ubanku ba ku dauke ni a bakin komi ba, baku dauke ni a cikakkar mai hankali ba. Na tabbata ba don ta bijire maka ba sai a yi auren ba da yawu na ba, sai dai a debo yayan shegiya a dire mini, a ce ga jikokina, in yaso ko in mutu, ko in yi rai, ba abinda ya dame ku bane. To a kan me zance ban yarda ba?

rashin yardar tawa baya nufin komi tunda kuwa Bello Makarfi zai aura maka ko na yarda ko ban yarda ba? Saratu zata maye maka gurbina ko na dawo ko ban dawo ba? Ta yi shiru cikin matsanancin takaicin da ba zai fassaru ba, tana zukar numfarfashi da kyar tana fesarwa da kyar. Ya dago idonsa jike da hawaye yace wallahi wallahi Hajiya, bani da wadda ta fiki, bani da wanda zai maye mani gurbinki, bani da kamarki kuma ban taba kwatanta matsayinki da na kowa a zuciyata ba! Ni dai burina ki yafe mini laifinda na yi miki, wanda na sani da wanda ban sani ba. Tunda kuwa ba kya son Intisar daga yau nima zan daina sonta zan daina kaunar ta. Ki yafe mani ki sa mani albarka. Ki taya ni rokon Allah ya sa na fi karfin zuciya ta kuma ya yaye mun kaunarta.

Ita kanta bata san sanda hawaye ya zubo mata ba, tayi saurin dauke su da yan yatsunta tun kamin ya gani. Ta mike tana nufin fita yayinda shi kuma ya bita da kallo, cikin rashin sanin abin yi kuma. Kamin ta kai bakin kofa ta ce,

“Allah ya yafe mana baki daya, ka tashi ka tafi wurin matarka haka zaka tayar mata da hankali. Kuma ka yi kokari ka tuno shin wane alkawari ka yi mun a ranar da ka dawo daga Miami? Bana nufin in tursasaka bisa raayi na, illah in tserar da kai daga tozarta alkawari!�

How much do you like this story?
5/14/22, 09:27 - Ummi Tandama😇: _____________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book four

*@Takori*

Page2ï¸âƒ£

Tafe yake a mota amma hankalin sa baya jikin sa. Kuka yake kashirban kaman karamin yaro. Duk da zuciyar sa tayi sanyi da yafiyar da ya samu daga gareta wannan bai hanashi kukan tashin hankalin da kalamanta suka tsomashi ba. Wane alkawari ne yai mata? Ya kasa tunawa.

Hajiya kin ce in koma ga matata, to ai gara in dawwama a nan kina azabtar dani daga hukunce-hukuncen ki, domin in na koma gareta bani da wani sauran amfani a gareta, me zan yi mata? Me zan ce mata? Rayuwata ta zamo impotent ba zata kara moruwa da ni ba, kowa ma ba zai kara moruwa da ni ba including Inteesar!

Na dauka zaki fahimce ni, na dauka zaki ji kai na ki ji tausayi na, na dauka zakiyi tunanin soyayyar da nake yi mata bata shafi kiyayyar da kike mata ba, na dauka zaki yi min alfarma irin wadda ba ki taba yi mun ba, na dauka zaki ce je ka Aminu ka auri Intisar, Allah yayi maku albarka, ya sa hakan shine mafi alkhairi a gare mu bakidaya., amma kamar ba kya tausayi na, me zan yi miki ki fahimci ni mai gudun bacin ran ki da fushin ki ne? Ban zaci zaki yafe mun ba tunda na yi sanadiyyar zubar hawaye daga idanuwanki.

Bana nufin in tursasa ka bisa raayi na, illa in tserar da kai daga tozarta alkawari ya tuno kalamanta na karshe. A lokacin zuciyarsa ta tariyo masa ranar da ya dawo, da kuma maganganun da sukayi shi da ita a dakin Faisal. “alkawari daya zan iya yi miki hajiya na, ba zan taba son ta irin son da Faisal ke mata ba!�

Amsar da ya bata kenan a wancan lokacin, maganar ta cigaba da amo har cikin kwakwalwarsa, ta bi har cikin jijiyoyi da tsokar jikin sa, ta zagayo ta fito daga bakin sa. Eh nayi maki wannan alkawarin kam, nayi Hajiya na, kina da hujjar hukuntani da alkawari na. na gode. To amma ba kiyi tunanin komi ya faru a bisa rashin sani ne ba? Ban san Intisar ce diyar Anti Amarya ba. Na so ta a Halimar ta, baa Inteesar ba, Ban san san sanda zuciya ta rinjayeni ga son nata ba.

Karar karon motoci sama da goma, tare da wuntsilawar da motar Alameen ta yi ta shiga katantanwa bisa titin, haka murje ta da wata kotuwar DAF mai cike da Hatsi tayi bisa titin da zai shiga da kai garin Minna kafin ya sadaka da Abuja, ya janyo hankalin alummar da ke wajen bakidaya suka ambaci. Inna lillahi wa inna ilaihi raji oun!

Cikin dan lokaci jamian tsaro suka cika wajen tare da motocin ambulance abin dai babu kyawun gani.

*****

UWA, MAHAIFIYA!!!

Tunda ya fita ta kasa sukuni, ta rasa me ke mata dadi, ta rasa inda zata tsoma ran ta ta ji sanyi. Ta kai gwauro ta kai mari a tsakiyar kayataccen falon, can kuma ta isa ga taga tana lekensa, har ya tada mota ya fita daga harabar gidan idanuwan sa basu bar tsiyayar da hawaye ba.

Ta koma cikin kujera ta zauna cikin mutuwa jiki, ji tayi tamkar ta zauna a cikin kaya, ta yi tagumi, zuciyar uwa! Haka kawai taji hawaye na zuba mata sharr-sharr. Ta san duk cikin yayanta babu mai son ta tare da yi mata biyyayyah tamkar Alameen, anya hukuncinda ta yanke a kansa tayi masa adalci?

Gaskiyar Innar ta ne son kanta yayi yawa, kuma wannan ba so bane! Ita uwa kullum hakuri take da abu koda tana so ta barwa danta, ya roke ta, ya kaskantar da kansa gareta irin yadda wani cikin yayanta bai taba yi mata ba.

Ya nuna mata fifiko akan bukatar shi. Ya ce alfarma ce ya ke nema irin wadda bai taba nema daga gareta ba! Ya zubar da hawaye irin wanda bai taba zubarwa a duniya ba, sabida tashin hankalin fushinta a gareshi. Koda sanda yake kankani bata taba ganin shi yayi kuka haka ba.

Ya nemi jin kanta da tausayi amma bata nuna ko daya ba, duk da cewa ba hakan ba ne zahiri a zuciyarta.

Ta nuna masa damuwar shi bata dameta ba, kiyayyar da ke zuciyar ta kadai ta sani, koda hakan zai zama ajalinsa bata amince masa ba, shin ita din wace irin mahaifiya ce?

Ta kai tunaninta ga yarinyarda aka kira da suna Saratu-Intisar. A iya saninta da yarinyar, shekaru goma sha takwas da suka gabata, tun tana jaririya kawo girmanta, bata taba daga ido ta yi mata koda kallon banza ba, bata taba bude dukkan idanun ta tangaras ta dubeta ba, sabida tsananin girman ta da kimar ta da take gani. Bata taba fada mata abu tace da ita ba haka ba. Bata taba yin musu da ita ba balle ta kai ga zaginta, duk kuwa da irin kyara, tsangwama, ukuba da rashin kyautatawar da take mata.

Ta dauki yayanta tamkar yan uwanta na jini, bata kula yayan kowa a duniya sai nata, sune ta mayar abokanta, yayyunta, kawayenta, abin gani ta ji farin-ciki kuma abin alfaharinta. Bata hada kaunar yayan ta da na kowa a zuciyarta. Bata dauki kanta a bakin komi ba face kaskantacciyar baiwa a gareta, duk da yakinin da ta ke da shi na cewa ita din diya ce ga Bello Makarfi.
Chapter 69 · 0% Book details