← Book details Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 90

Sashe 34

Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Labarin nan da Baffa ya bani na yadda sukai da kishiyata Shatu, sai na fadi, ban kara sanin inda kai na ya ke ba. Tun daga ranar yau ciwo gobe lafiya amma ban kara rayuwa mai dadi ba. Jike-jiken saiwoyi babu irin wanda ba’a mun a rugar mu amma ciwo kullum kaman ana kara iza shi, sai dai a kwantar a tayar.

Cikin wannan halin Allah ya aikowa rugar mu farin rashin ruwa, tumaki da shanun mu suka shiga mutuwa, gonaki da koramun mu suka bushe kyamas, hatta ciyayin mu da shanu ke ci sun bushe kyamas kamar ba’a taba amfana da su ba, wanda hakan ya kara taimakawa wajen kashe dabbobin.

Aka dage da Addu’ar rokon ruwa ko ma fita daga wanan masifa sai Allah ya aiko da wani irin kakkarfan ruwan sama hade da cida mai karfin gaske. Ya yaye bukkokin mu, ya kashe tsoffi da marassa karfin cikin mu, ya tafi da kayan amfaninmu, marassa karfi ciki har da Yafendo na da mahaifiyata! Baffana kuwa garin gudu yumbu ya tade shi ya fadi ko shurawa bai yi ba. Ni da kanwata Hajjo kadai muka kubuta, inda Hajjo ta goye ni, tana gudu da ni, Hajjo ta sha faduwa tana tashi duk gwiwoyinta sun kwaile, hawaye take cikin ruwan tamkar wadda ake zarewa ciwo har ta fiddo mu bakin titi.

Ni kam ban san ma me ake ba don tuni na suma. A nan bakin titin da zai kai ka gidan Hakimin Shanono mutane suka gan mu, aka je a ka gayawa Hakimi, yasa aka dauko mu, ni aka kai ni asibiti, Hajjo kuma ta rakasu rugar mu washegari suka ga inda Allah ke ikon sa, har ruwa da cabi ya rufe wasu, tumaki da shanun mu mafi yawa sun mutu, kalilan sun tsere, aka dauko gawar mamatan aka yi masu suttura aka kaisu gidan su na gaskiya.

Hakimi ya cigaba da kula da lafiyata a asibiti Hajjo kuma na tare da ni, bata iya barci bata rungume ni ba mun yi barcin tare, tana wanke mun jikki tana kuka tana kiran Innar mu, domin Hajjo yarinya ce karama ‘yar kimanin shekaru goma sha biyu a lokacin, a yayin da ni kuma na ke da sha biyar, kin san girman jeji akwai karfi shi yasa har ta iya ta goye ni zuwa waje mai nisa haka.

Wata na guda a asibiti ina jinya kamin in sami kaina. Hakimi ya tausaya mana kwarai da gaske yace mu zauna nan a gidan sa har zuwa sanda Allah zai bamu mazaje yayi mana aure.

Kwamfa, matan Hakimi hudu suka ce dawa Allah ya hada su ba da mu ba? Haka kawai zai dauko ‘yan mata tsala-tala ya aje masu to zaman me za mu yi banda muyi masu bauta? Daga ranar duk uban girkin gidan Hakimi mu muke yinsa safe, rana da dare.

Shara, wanke-wanke ke har wankin kayan su dana ‘ya’yan su, surfen masara da dawa da tatar koko kuwa wannan kananan ayyukan ne. Cikin wata guda kacal sai ga kanta ribda-ribda a hannun Hajjo cikin farar tsokar hannun ta sabida surfe. Farin mu ya dushe sai idandunan da karan hancin kadai. Suttura sai in yaran su sun yar mu ke samu mu dauka mu saka. Hajjo da wuya ta isheta ta ce mu gudu, mu tsirar da kuruciyar mu. Nace da ita darajar bawan Allahn nan Hakimi zata diba, ya dauke mu kamar ‘ya’yan cikin sa duk wata kulawa da ta dace uba na kwarai ya yiwa ‘ya’yan sa Hakimi yana yi mana, duk abinda ake mana cikin gidan bai sani ba.

Ni kuwa dama tuntuni Allah bai daura min yawan magana ba balle tsegumin da har zan yi tunanin gaya mashi, wannan sai Hajjo, to amma ita ma surutun nata na tsoron Inna Kwaire, haka muke wuni ba mu ce da kowa ko ‘umh� illa in sun ce mu zo mu yi masu kaza mu tashi jiki na rawa mu yi masu don mu kwana lafiya. Hakanan nace da ita.

“Hajjo in mun gudu ina zamu? Mun san irin hannun da zamu fada a gaba? Kada ki guji mutanen da kika taras da farko domin irin su ne zaki taras a gaba�.

Shekarun mu biyu a gidan Hakimi muna bauta. Ba zan taba mancewa da ranar da Basheer kanin Hakimi ya dawo daga jami’ar Nsukka inda ya ke karatu ba.

Basheer shakikin Hakimi ne da Hakimi ya rike tun yana karami bayan rasuwar iyayen su. A nan garin yayi firamare ya ci makarantar kwana ta FGC da ke Kano ya je ya kammala da sakamako mai ban mamaki. Hakimi ya danka mai gadon iyayen su da ke hannun shi ya ce ya je yayi ta karatun har ya gaji sabida hazakar shi. Tun da Basheer ya wulwula kudu ba’a kara jin duriyar shi ba sai ranar nan. Gabadayan karatun Basheer yayi shi ne a kan (Diplomacy), tun da ya bar Shanono bai dawo ba sai ranar da ya hado digirin shi na biyu, ya watsa takardun neman aiki a (Nigerian–Embassy) na kasashe har ukku sabida International Studies ya danganci aiki da kasashen ketare ne.

Ranar kwatsam sai ga Bashir, ‘ya’yan Hakimi da matan shi duka suka debi murna babu babba ba yaro kowa baki a washe har muma da ba’a san da mu ba muna ta dariya, kasancewar Bashir mai faram-faram da barkwanci kowa son shi ya ke a gidan. Ban taba ganin Hakimi na far’a, irin wadda ya rika yi a ranar da Bashir ya dawo ba.

Rannan ina shara Bashir ya zo wucewa dakin amaryar Hakimi, ban ga tahowarsa ba na sharo mai sharar da na sharo a kafa cikin wasa yace,

“ke ‘yar fillo, ba kya gani ne? Koda yake na gane wayonki, don in rasa mata ne, to ai ni kyakkyawa ne a Nsukka kar kiso kiga yadda ‘yammata ke bibiya na, ni nan da kike gani ‘yammata jaka-jaka gare ni�.

Hajjo da ke gefe tana wanke-wanke ta ce

“ka yi hankuri, bata sani ba ne�. Ya kai duban shi gareta domin da fari bai lura da kasancewarta wurin ba, sannan ya dube ni, a kidime yace

“ikon Allah, ke Hussainarta ce ko, koko ‘identical twins� kuke?� Duk sai muka yi murmushi a tare, kumatunan mu suka lollotsa gwanin sha’awa. Bishir ya bushe a tsaye, yace “ku ‘ya’yan makota ne?�

Hajjo da ya ke Allah ya zuba mata magana, a komai ma da ba’a tambaye ta ba balle wannan mai dalili? Wani zubin surutu har tsunkulin ta yake, ko ni aka tambaya abu in har tana wurin ita ke aran baki na ta ci mun albasa, tayi narai-narai da ido ta rausayar da kai gefe ta ce ,

“ai mu marayu ne, Uwa da Uban mu duk sun mutu, ruwa ya tafi da Yafendon mu, Baffan mu kuwa garin gudu yumbu ya kayar shi ko shurawa bai yi ba…� sai ta koma kukan da ta ke kwana da wuni ta na yi.

Bashir ya matsa gare ta ya russuna a gaban ta cike da tausayi yace “ayya kanwata! Duk wani mai rai mamaci ne, muma nan duk zaman jiran ta muke.

Nima Bashir tamkar ku din nake, har gara ku kun san Innar ku har kun yi rayuwa mai dadi tare da ita, ni ko tana haifana ko fuskana bata gani ba ta tafi ta bar ni. Bani da kowa a fadin duniyar nan sai Allah, sai Yaya na, amma ba na kuka, don haka kema ki daina kuka. Daga yau na zame maku Yaya, kin ji?�

Hajjo ta gyada kai alamun ta ji abinda ya ce. Ya sanya hannu cikin aljihu ya fiddo hankici fari sol da shi ya mika mata yace � share hawayen ki maza-maza, zani cikin gida yanzu zan dawo�.

A wurin uwar gida Kwaire ya nemi jin labarin mu tace “haka kawai ya je ya kwaso mana masifa rana tsaka, don sun gudo daga daji, ka gansu nan in ban da bauta ba abinda suke mana, kaima in kayan ka sun yi datti, ka dinga dankara masu har gugar takalmi daga yau kar ka kara yi, tsuntsu ne Allah ya kawo mana daga sama gasashshe�.

Da Hakimi ya shigo gidan bayan sallar lisha Bishir ya ke tambaye shi labarin mu. Hakimi ya kwashe komi ya gaya mishi har ciwon da nayi kamar ba zan rayu ba. Ya kare da cewa “ni kam don Allah ni ke rike da yaran nan, na kuma san sakamako na na gareshi. Duk ma mai cutar su cikin mata na ai ita da Allah, Allah yana kyale hakkin maraya ne?�

Sai da Bashir ya fiddo hawaye don tausayin mu ya kuma ce da Hakimi zai aure ni koda bamu da iyaye balle muna da su. Hakimi ya sa mai albarka mai yawa amma sai ya ce tunda shi saurayi ne ya auri Hajjo ita ce budurwa, amma ni na gaya mishi na taba aure har na haihu mijin ne ya mutu aka kuma sace diyar. Bishir yace shi ba budurwa ta dame shi ba, hakannan tun da ya ganni ya ji bai iya rayuwa ba tare da ni ba, Hajjo kuwa zai rike yadda zai rike diyar cikin shi har zuwa sanda itama Allah zai bata miji ya yi mata aure.

Ya roki Hakimi da ya bar sirrin nan a tsakanin su ko muma kada ya bari mu ji bare matan shi da ke kin mu tamkar mutuwar su, har zuwa sanda takardun shi na aiki zasu fito, kamin nan yana so ya ja ra’ayinmu mu saba da shi musamman ni da ya ga ko magana bana yi da kowa.
Chapter 34 · 0% Book details