← Book details Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 90

Sashe 45

Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anti tayi jugum, kallo daya zaka yi mata ka tabbatar tafiyar Faisal ya taba zuciyar ta, fiye da zaton Hajiya, ya takaita farin cikinta, fiye da yadda Hajiyar ta kintata a zuciyar ta, ta ce,

“Oh ni Saratu! Ban da abun Faisal maiyasa ba zai fadi ba, sai ya bar kasar? Bana jin ko diyar wanene a garin nan da Babanku ba zai iya aura mishi ba. Allah to ya sa hakan shine mafi alkhairi.�

Da daddare tayi shirin kwanciyar barci kamar yadda ta saba amma me? Idanuwanta sun ce basu san wannan ba. Tayi kukan ta mai isar ta, da ta kasa gane musabbabin sa.

Ba zata ce son Faisal take ba, don bata san ma hakikanin menene son ba. Amma da tayi tsam da ranta ta fahimci kishin yarinyar da ta sa Faisal barin Nijeriya ne!

Haushin tafiyar sa ya shafe kewar sa, mafi rinjaye shine irin matukar sabon da su kai da juna.

Akwai wani kebantaccen al’amari game da Faisal a tare da ita, da ita kanta bata san menene ba. Abinda zata iya cewa shine Faisal, wani mutum ne precious wato (mai darajja) da kima agareta da muhimmancin sa da kimar sa ya zarta na kowa in ka dauke Daddy da Mamarta. Kenan mancewa da shi a tarihin rayuwar ta ko barin tunanin sa, wani abu ne da ba zai taba kasancewa ba!!!

Mu karasa a littafi na uku, Takorin ku ce.

Wa billahi taufeek!

How much do you like this story?
5/9/22, 21:00 - Ummi Tandama😇: ____________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book three

*@Takori*

Page1ï¸âƒ£

Lahadi/Jumada-Awwal
Watanni Biyu Bayan Barin Faisal

Satin Daddyn kwata-kwata biyu da fitowa ya shiga sabon ofis din sa a gidan shugaban kasa. Cikin watanni biyu rak arziki ya ci uban nada, rayuwa a gidan Brigadier Makarfi ta dawo sabuwa ful arziki wane shekarun baya.

Sai da hankali ya natsa aka mance komi Aunty Saratu ta farkewa Daddyn gaskiyar Saratu bata kammala karatu ba.

Daddy yayi ta fada har yana haki kan don me tuntuni bata gaya masa ba, da yanzu bata yi zangon karatun ta na farko a aji shidda ba, gashi shekara ta zo tsakiya tilas abarwa sabuwar shekara mai kamawa in Allah yayi tsawon rai. Amma kam ran shi ya matukar baci inda ya dauki duk laifin ya daura akan Anti Saratu.

Ranar Lahadi, cikin sabon watan Jumada Awwal, ta shirya cikin wani lallausar material baki wuluk mai yarfen jajayen furanni. Curarraren gashin kanta ta nade shi tsaf cikin dankwalin kayan ta yadda baka ganin ko sili daya, kafar ta sanye cikin (bed-shoe) watau takalmin bakin gado, sannu a hankali take sauka daga benen sassansu tana bin matattakala cikin nutsuwa da yaukin ta na musamman da Allah ya hore mata.

Tayi amfani da sassanyan turare (Week-End Burberry) sanyin kamshin na tashi daga jikin ta kadan-kadan inda duk ta gifta har ta iso falon hutawar Daddyn, da yake ranar Lahadi ce, ya kan kasance ne a falon yana ‘browsing� tun safe har bayan karfe hudu na yamma baya zuwa ko’ina.

Ta sakko ne musamman da niyyar bashi labarin Hidayah da Hunainah Bashir Sambo, kawayen ta na makaranta da suka shaku, bata taba yi mai zancen su ba, shi ko Daddyn komi nashi ita yake fara gayamawa kafin kowa a gidan har matan sa kuwa, tana ganin Daddyn zai taimaka ya binciko mata inda suka koma a Korea da adireshin su, kullum da tunanin da take kwana take tashi kenan, don dai hankalin su bai kwanta bane sai ko yanzun da take ganin ya dace Daddyn ya san da su Hidayah, har abada bazata taba mancewa da su ba.

Yaran Sun zauna cikin kwakwalwar ta (like the screen saver of her imagination) Musamman Hunainah, kauna ce mai karfi take masu da har ta kan tambayi kanta, da su da Ya Faisal, wa ta fi kauna?

Ta same shi da ‘laptop� din shi ne kamar yadda tayi tsammani, sai ta ja kujerar da ke fuskantar shi ta zauna, suka dubi juna suka yi murmushi ta ce,

“Daddy an tashi lafiya?�

Ya ce, “Tunda ki ka ganni a nan ai zance ya kare, kin san tambayarki itace amsarki Saratu�.�

Magana yake amman hankalinta baya tare da shi, yana ga allon kwamfutar. Wani kayataccen rubutu ne Daddyn yayi, yayi mai ‘design� mai kyau, da gani yayi ne don ado kawai cikin kwanfutar ba don ya aikawa wani ba, kalolin da aka kawata rubutun da su masu daukar ido ya dubesu ne koda bai yi niyya ba.

A gurguje ta shiga bin rubutun bata sani ba ma a fili takeyi ba.

“Although he refused to assist me when I needed his assistance most, I should, however, forgive him wholeheartedly.�

Ma’ana “Duk da cewa ya ki taimakamin a sanda nake tsananin bukatar taimakon sa, duk da haka zan yafe mai da zuciya daya�.

Cikin ‘yar karamar muryar ta ta ce, “Daddy waye wannan?�

Yace “Yayan ku Al’ameen ko kin manta shi?�

Ta kai hannu ta zare gilashin ta a hankali ta ce, “Al’amin kuma? Waye haka?� Cikin tsananin mamaki, zaka iya karantar hakan karara cikin abnormal (marassa lafiyan) idanun ta.

“Muna da wani Yaya ne Aminu Daddy ko dai cikin dangi ne ta Makarfi?� Mamaki ya kama Daddy, ya ce,

“Sanda Aminu ya bar kasar nan bakiyi wayau ba, Aminu ne ya janyo maki laluran ido, har da shi muka kaiki asibiti a Jeddah ba mamaki da baki san shi ba, abin mamakin shine ko sunan shi baki sani ba?�

Ta ce, “Kwata-kwata ban taba ji a bakin kowa ba, ba wanda yake zancen shi daga Ya Faisal, Ya Najib har su Mamar mu ban taba ji ba.�

Yayi murmushi ya ce,

“Su Najib ai haushin sa suke ji, sunce sun fidda shi a layin ‘yan gidannan.� Abinda ta lura da shi shine idanun Daddynsu cike suke da kaunar dan shi Al’ameen da bege mai tsanani. Ta gyara zama ta ce,

“Daddy a bani labarin Ya Ameenu?� Ai kamar mai jira ta tambaye shi, ya shiga bata labarin Al’ameen tun daga rayuwar shi ta kwaleji, hazakar shi irin nata, da yanayin mu’amalar shi da mutane. Ya ce,

“Mutane da dama na mai mummunar fahimtar girman kai da wulakanci, amma ni nasan Al’ameen dina (gentle) ne kawai. A ‘ya’ya na ba mutun irin Al’ameen Saratu, domin shi din genius ne (mai madaukakiyar iyawa).

Al’ameen nawa, yana kaunata sosai Intisar, ban taba zaton jin dadin turai da kyale-kyalen ta zasu sa ya mance ni ba balle…� Bai iya ya karasa ba sakamakon hawaye da suka shimfido mai a guje.

Ya juyar da kai don bai son Sartun ta gani amma ta ganin. Tuni itama nata idanun suka cika da kwallah, tayi azamar mai da gilashinta tasa tissue tana share hawaye ta kasan gilashin. Tsana da haushin wannan Yaya Al’ameen ya dirammata tunda kuwa har zai sa Daddy kuka da azabar kewar shi, bata san sanda bakin ta yayi subul da cewa

“Daddy maiyasa kake son Al’amin har haka?�

Yayi murmushi ya ce, “biyayyar sa.

Ban taba ganin yaro mai gudun bacin ran iyaye a duniya irin Al’ameen ba. Yana jin maganata yana yi mun biyayya, ban taba cewa ya bar abu yaki bari ba sai a kanki.

Ya gaya mun sabida nadamar abinda ya aikata gareki ne ya bar mu kwata-kwata don aganin shi bashi da amfani a gareni…�

Ya kwashe labarin komi ya gaya mata, bata yi wani mamaki ba, tunda kuwa dan Hajiya Nafi ne, ba illata ta ba, ta tabbata ko konata ne Hajiya zata iya sawa a yi.

To amma albarkacin wannan son da ta ga Daddy na yiwa Al’ameen sai taji itama tana son shi, bata kullace shi ba ko kadan.

Tabbas a lokacin zai kasance yana yaro ne cikin gigin kuruciya, tana da tabbacin da zai zo a yanzun he’ll be a caring brother (dan uwa mai nuna kulawa). Tace

“Kaayi hakuri Daddy, ni na tabbata Al’amin zai dawo a lokacin da bamu zata ba.� Ya ce, “Kayya Intisar, Aminu fa har gaya mai akai an kulle ni, akan laifin da ya tabbatar ba zan taba iya aikatawa ba, amman yace wai zaman Amurka ya fiye mai kwanciyar hankali bazai dawo ba.

Koma menene laifi na ne da tun farko na amince mai ya tafi.

Ban taba kuka akan son dan da na haifa ba sai a kan Al’ameen. Ameenu yaro ne mai matukar shiga rai don haka fidda tunanin shi a lokaci guda, abu ne da bazai yiwu ba.

Tunanin sa na azabtar da ni Saratu Ina kokari ina dannewa ne kawai don bana son kuma ku shiga damuwa�.

Inteesar tayi zuruuu tana sauraren Daddyn duk tausayin sa ya nannadeta, amma a ranta cewa take Allah ya isa tsakanin ta da wannan Ameenun, kuma wannan Al’ameen anyi tsinanne, tunda kuwa har zai iya sanya rayuwar Daddyn su a wani hali bayan wanda ya fito, kuma akan sanin kansa, suna murna duk wata matsala ta kare?

Shin shi Ya Al’amin din nan bai tsoron hakkin Daddy ya hana shi kwanciyar kabari?�

Ta tausasa halshen ta ta dukar da kai cikin matsanancin takaici ta ce,

“Ba dai biyayya Al’ameen yake maka ba Daddyn mu? To na yi alkawari tsakanina da Sarki Allah zanyi ma biyayya Daddy irin wadda Al’ameen bai taba yi maka ba! Zan maye maka gurbin Al’ameen.

Zan wanzar da rayuwa ta a biyayyar ka, zan dauwama a cikin umarnin ka in har bai sabawa mahalicci ba, bazaka taba sani abu in ki yi ba koda ya fi karfin lafiya, rai da abinda na `mallaka; sai dai in mutu a cikin umarnin ka Daddy!�

Kalamun ta sun matukar bashi mamaki, hakannan sun girgiza shi amma bai nuna ba, sai yai murmushi ya shafi kanta da hannun shi na dama. Shi kansa ya san hakan a tun ranar da ya daukota cikin tsumman goyonta a dokar daji. Ya ga alamun hakuri, biyayya, kyautayi da jin kai tattare da ita.

Yana kaunar ta, kaunar da baya yiwa daya cikin ‘ya’yan sa bayan Al’ameen. Ta ce “Wai shin ba’a bin sawun Yaya Aminu ne?�
Chapter 45 · 0% Book details