← Book details Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 90

Sashe 30

Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A tsahirta da karatun a ga abin da Allah ya shirya a gaba. Ku zauna ku ci abinci, ba tare da kun zubda mutuncinku ta hanyar roko a idon kowa ba, balle a samu abin goranta maku. Na san yanzu an sa ido ne a ga kasawar ku. Amma in kun kame mutuncin ku baku kuma je neman taimako wurin kowa ba, ban da Allah, babu wanda zai wulakanta ku.

A yau neman taimakon ya zamewa talaka abin wulakanci, don haka ku tashi ku je ku kwanta, gobe in Allah ya kai mu ki koma dakin mijin ki, ku ci gaba da addu’a, Allah ya kawo mana dauki da gaggawa.�

Washe gari suka kamo hanyar Abuja cikin bus din haya kamar yadda suka zo, zuciyoyin su cike da taraddadin wannan masifa. Ko a mafarki Saratu ba ta taba kawowa iyayen ta da ita kanta za su taba fadawa irin wannan SIRADIN RAYUWAR ba. Saratu ta yi kuskure, babu wanda ya ke sama da jarrabawar Ubangiji. A yau ta tuno da wata waka da ta kan ji a bakin kawarta Hidayah, da haka kawai in tana wani abun za su ji tana waka tana cewa:

“The rich also cries�.� Ma’ana: ‘Mai kudi ma yana yin kuka.�

Lallai Uba, shi ne jigon rayuwar ‘yan adam. Uba shi ne farin cikin iyali, shi ne bango abin jinginar su, shi ne rufin asirin su, in ba shi rayuwar iyali abin tausayi ne.

Wani abu da ya ba su mamaki da suka iso Khalil ke gaya masu Hajiya da Mama Suwaiba sun tafi Johannesburgh (Saro gold dinsu). Madadin zaman hakan nan ta samawa Intisar makarantar koyon na’ura mai kwakwalwa a layin su inda za ta yi (DIT) ta kuma dauko daya cikin dakin Brigadier ta aje mata bisa tebirin karatun dakin ta sannan ta hada mata Internet, duk don ta debe mata kewa duk da yarinyar ko kadan bata nuna mata wata damuwar ta ba sam. Ita ce ma mai karfafa Antin da ta saki ranta, in don makaranta ne ko nan da shekaru biyar in Allah ya ce za ta koma ne a cikin yardarsa.

Ta dage da fafutukar neman aiki da kafafunta. Saratu ta share komai ta maida hankali kan koyon kwamfutar ta, cikin watan ta na farko da farawar Diplomarta ta kware sosai.

Yammacin wata ranar Juma’a zaune take bisa kujerar na’urar ta, tana zanawa kawarta Raadhah sakon yadda al’amuran rayuwa suka cude mata, suka yi sanadiyar rashin dawowarta makaranta.

How much do you like this story?
5/8/22, 09:59 - Ummi Tandama😇: _____________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book two

*@Takori*

Page5ï¸âƒ£

Sanye ta ke cikin danyar atamfa Super English, ruwan kwai da aka yi wa ratsi da shudi da jaja-jaja, atamfar ta yi matukar amsar dan kyakkyawan jikin ta, an yi mata dinki zani da riga fitted kanta babu kallabi, maimakon haka ta daura shi ne a kan cinyar ta, gashin kanta wanda yake curl a sake yake bisa dogon wuyan ta, sanyin air-condition ya kara taimakawa ainun wurin kara kwantar da shi lub-lub a wuyan ta kamar ba abin da ya dame ta.

Sai dai ta yi ‘yar rama wanda hakan ya kara mata kyau, fuskar ta fes, da ruwan hoda chiristian dior da take amfani. Sai kawai ta ji an rufe mata ido daga baya, ta lumshe ido ta yi ajiyar zuciya ba ta bari a kasa ba ta ce,

“Daga jin kamshin 5000 Doller na san Ya Faisal ne, wani Bayarabe mazaunin Illorin.�

Faisal ya yi dariya, ya dube ta gaba daya yana kiyasta adadin ramar da ta yi, hannuwan shi a cikin aljihun wandon shi, ya ajiye gwiwoyinsa a carpet ya zaro hannun shi daga aljihu ya tallabi habar ta ya ce, ‘Baby, are you still� still at home?�

Hawayen da take ta tattali ne suka kubce sharrr! Haushi ya ba ta kamar ta doke shi, ta kai hannu ta sauke hannun shi a habarta ta maida hankali ga abin da takeyi. Ta tabbatar sakon ta ya tafi ga Raadha, tana yi tana share hawayen da suka jika mata kundukuki da yatsun hannun ta.

Ba wanda take tunani a wannan lokacin sai Daddy. To bata san kuma me za ta ce da Faisal ba, ba za ta iya gaya masa mai dadi ba, shirun shi ne mafi amfani.

Ai ko albarkacin makwabtaka, bar ta kasancewar ta kanwar ubansu, ba ma na uban da ya hada su a gidan ba, sa dinga taimakon Aunty Saratu.

Su ‘ya’yan Hajiya uwar su mai gwal, don haka duk suka koma makaranta suna batar da kobo yadda ransu ke so, turaren Faisal kadai ya isa su shekara suna cin abinci ita da uwar ta.

Ba a maganar agogon diamond da ke daure cikin lafiyayyar fatar hannun shi wanda ya isa ya maida ta Riyadh har da canji!

Su ko Allah Sarki, ko abinci sai sun je kasuwa da kansu sun sayo. Amma shi ne wai don rainin hankali yake tambayar ta har yanzu tana gida? To sun ba su wani abu ne ko da cikin dukiyoyin Daddyn da Hajiya ta tattare ta boye?

Tasa dankwalin atamfar da ke bisa cinyar ta ta share ido, a sanda ta jiyo Najib na gaisawa da Aunty, wai ga buhun shinkafa nan za a shigo mata da shi, tana jiyo sanda Antin ta ce cikin fara’a, “Lah! Ku bar shi kawai, don can da yara muku nan mu biyu ne kacal, ba zamu rasa abin da za mu ci ba don ba Alhaji.�

Ta sake tunzura, ta mike ta kashe kwamfutar ta yi daki fuuu! Har tana tuntube da kujera. Ita dukkanin su ba ta son ganin ko daya duk selfishes take ganin su wato masu son kansu kadai. Faisal ya zamo wani irin pale (Mara kuzari) tamkar ya mtu, ya kasa motsa ko da dan yatsansa, da kyar muyarsa ta fita can kasan makoshi.

“Intisar na so ki tsaya ki fahimci ba wai…�

Tuni ta fice. Faisal bai yi wa kowa sallama ba a ranar ya koma Ilorin. Bai ko ji tsoron tafiya mai nisa haka cikin daren ba, a hanya ya kwana, kar ki so ki tona zuciyar wannan aminin Intisar.

An sanar da Anti tana da baki sati biyu bayan faruwar wannan. Ta sha lullubi ta iske su a sassan baki su biyu duka maza, ta sha mamaki da ta ga Larabawa ne na usil bakin nata.

To an yi sa’a ita ma ta dan iya larabcin a bakin Intisar, nan suke gaya mata su shuwagabannin shashen da diyar ta ke karatu ne a Kingston da ke Riyadh.

Sun zo Nigeria ne musamman don abu biyu, na daya kafa reshen makarantar su tare da Jami’ar Bayero da ke Kano, na biyu, sun yi amfani da adireshin su Saratu don su zo su ji ko lafiya, suka katsewa hazikar yarinya kamar Sarah da ake wa hangen great achiever a gaba karatu? Ya kare da cewa.

“Saratu in ta kammala karatu, ba ma nufin kasar Saudiyyah ta amfana da ita, face kasar ku da za ta sami dumbin amfani daga gare ta.�

Aunty Saratu ta gode masu, for their concern kan al’amarin diyar ta, kuma hakika ta ji dadi, sai ta ce, da su ko Saratu za ta koma Riyadh to ba yanzu ba, saboda ba za ta iya affording cost, din ba. Babanta yana kulle. suka nuna matukar juyayi, dayan ya ce shi da Saratu tamkar diya da ubanta suke a makaranta, shi ne Dr. Alhassan As-Sayyid malamin Chemistry din su, don haka zai ci gaba da daukar nauyin karatun Saratu daga sakandire har jami’a amma fa in sun amince.

Aunty Saratu ta dade da daukar wata wasiyya ta mahaifinta kan ‘dogaro da kai, shi ne babbar siyasa�, amma bata nuna masu ba.

A karo na farko ta yi sha’awar gwada hankalin Saratu, sai ta yi ta yi masu godiya ta ce amma bari ta je ta ji ta bakin Saratun tukunna, don bai yiwuwa ta ari bakin ta ta ci mata albasa, suka ce alright.

Inteesar kwance tsakiyar ni’imtaccen gadon ta tana mai fuskantar ceiling idanunta a rufe ruf kamar mai barci, zuciyar ta cike da kuncin Ya Faisal da Najib. Aunty ta tsaya a kanta ta yi murmushi ta ce, “Har yanzun haushin Faisal din ne? Alhalin sam ba shi da laifi Saratu, kudi fa uwarsa ke da su ba shi ba, a kan me za ki dauki laifin duniya ki dora masa? Sata kike so ya je ya yo ya maida ki makarantar ko me? Bayan ma Allah ya yi mana ludufi?�

Ta juyo ta dube ta cikin ido,

“Daddy ya fito?� Ta fadi da wata irin shanyayyar murya.

‘Tukunnah, ki san wani Dr. Alhassan a makarantar ku?� Ta zabura ta zauna daidai, ‘Chemistry teacher na da nake ba ki labari mai yi min wakar Saratu is doing research, kin tuna? Ya kula da rayuwata sosai a duk zamana na shekaru biyar a Riyadh.�

“To shi ne ya zo yanzu tare da wani Abraham Shaikh, sun ce ki bi su ku koma makarantar zai ci gaba da daukar dawainiyar karatun ki har zuwa mu ga abin da Allah zai yi.�

Saratu ta yamutsa fuska ta ce, ‘Kash! Ya kawo taimako a sanda ba ni da bukatarsa. Dama dai ya ce zai taimaka ne a fiddo mana Daddy, Akbar min zalik (abobe all) Mamar mu ba zan iya tafiya in bar ki lonely cikin irin wannan halin da muke a yanzu ba, ba zan iya karatun ban san halin da Daddy ke ciki ba.

Don Allah Mamar mu ki ba malami na hakuri, ni wallahi ba zan bi su ba……�

Sai tasa mata kuka da baya mata wuya tun farkon faruwar al’amarin kamar sun ce za su ja ta ta karfi ne. Aunty Saratu ko so da kaunar Intisar ke kara tofo a zuci da gangar jikinta. Ta gode Allah da bai ba ta dan kanta ba, mai yiwuwa da ba zai ji kanta kamar ‘yar da ba ta san ko ta waye ba.
Chapter 30 · 0% Book details