← Book details Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 90

Sashe 46

Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya girgiza kai, “Ba wai kudin ne babu ba Saratu. America kasa ce mai girman gaske, (It’s the greatest country of the world). Abin takaicin shine yana birnin Miami yana buya a cikin Florida kar mu gan shi ko kar mu san inda yake. In banda adireshin sa na e-mail ban san komi game da shi ba a yanzu.

Kuma ke a tunanin ki yaron da ya watsar da iyayen sa akan kansa, bai son ganin su kina ganin ya dace iyayen su zubar da darajar da Allah yai masu ta iyaye su nemeshi?

Ai har kullum da ke neman albarkar iyaye ba iyaye ke neman albarkar da ba.

Yaran yanzu ne ka haife su amma baka haifi halin su ba. Duk in da uba ya kai ga gwada masu kauna da nema masu farin ciki su sai sun sashi kuka. Ba zan nemi Al’amin ba koda zan mutu ne ban gan shi ba, koda na mutu, Saratu ki gayawa Yayanku Aminu, son nan da nake mishi tun yana gudan jininsa, ina zumudin a haife shi in samu magaji, da kasancewar shi buri na ba abin da ya canza har gobe sai ma abinda ya karu.

Kuma har cikin raina na yafe mashi kuncin daya dasa mani na shekara da shekaru.�

Sai ta rufe bakin Baban su da tafukan hannun ta, kamar tace wayyo Allah! Sabida bakin cikin Al’ameen da mutuwa da Daddyn ke ambatawa kansa.

Ta ce, “Insha Allahu Daddy ni da kai, zamu gayawa Ya Ameenu wannan. Daga yau zan fara Addu’a duk inda Al’ameen yake, Allah ya karkato da hankalin shi gida Daddy.�

*****

Wani muhimmin abin farin ciki daya samesu bayan kubutar Daddy da ‘yan watanni shine bayyanar matashin ciki jikin Anty Saratu, farin cikin Inteesar a wannan dan tsukin kema kin san ba sai an fada ba. Daddy don farin-ciki makullin mota KIA ya danka mata fara sol ta fara zuwa sabon aikin da ta samu da (Afri-Bank). Gabadaya sun kirayi shekarar da watan Jumada-Awwal; ‘Cikar Burin Shekara Da Shekaru.�

Dukkan Farin-Ciki Na Tafiya Ne Da Bakin-Ciki

Laraba/Ashirin Ga Watan Jumada-Thani
Ranar wata laraba, da saratu ta kira LARABGANA a gareta, ya kama ranar girkin Antinne don haka tayi mata sallama ta nufi sassan Daddy, duk ranar girkin ta haka suke wa juna, babu zancen kunya tsakanin Saratu da diyarta Saratu.

A lokacin cikin ta ya shiga watanni uku duk wasu alamomin mace mai juna biyu sun gama bayyana a jikin ta. To bayan fitar Antin har goma na dare Inteesar na falo kwance cikin (rest-chair) dake falon tana sauraron labarun ‘network� daga gwanin ta Cyril Stober da Hawwa Baba Ahmed bata san sanda barci mai nauyi ya dauke ta ba, sabida a yau wuni sukai girke-girken Daddy ita da Mamarta ko na minti biyu ba su huta ba.

Ba ita ta farka ba sai karfe ukku na sulusin dare shima sakamakon masifafffen sanyin da taji yana hurata ne, ta yayibi bargo ta ji wayam. Ta mike taga yadda ta bar komi a kunne ta kashe talbijin da ke ta shuuu! Da sauran kayan wutar da ke falon.

Ta daga labule da niyyar kashe fitilun falon ta je ta kwanta kenan taji motsin ana taba kofa. Cikin ta ya hautsina ji kake kulululuuuu! Musamman data tuna bata rufe ko kofa daya ba bayan fitar anti, a guje ta shige bayan labule ta sandare ko kwakkwaran numfashi ta kasa shaka balle ta fesar.

Ba abinda ta kawo wa ranta a lokacin face gaggan ‘yan fashi ne suka kawo masu ziyara, amma wannan ba karamin abin mamaki bane in akayi la’akari da irin sojojin da ke gadin gidan Bello Makarfi tuni ta soma hawaye, a lokaci guda kuma fitsari ya kulle mata mara.

Bata san sanda ta sakeshi daga tsayen ba.Tsoron ta Allah, tsoron ta kada su taba lafiyar Daddyn ta. Ko wannan shine dalilin yin zancen mutuwa da Daddyn yayi mata a kwanakin baya?

Daga inda take rakube a bayan labule, tana iya hangen kofar shigowa falon su kasancewar labulen shara-shara, kuma dakin gauraye yake da hasken da Allah bai bata ikon kashewa ba.

Tana ganin sanda aka turo kofar falon cikin nutsuwa da sanda, ba abinda ‘yan idanun ta basu gane mata ba kasancewar akwai wadatar hasken kyandir kamar safiya. Sanye da bakar zulumbuwar riga, kanta a tsefe, tana rike da bakar kwarya a hannun ta na dama, wata bakar tsuntsuwa ce da ake kira mujiya matacciya rike a hannunta na hagu; Hajiya Nafi ce.

Kanta tsaye ta murda kofar dakin barcin Antin ta shiga, tafi karfin awa daya kamin ta fito, tuni numfashin Intisar ya dauke. Ashe bata gama razana da mamaki ba?

Da ta fito daga dakin Antin dakin Intisar din ta afka gaba-gadi. Ji tayi kamar tayi ihu amma sautin ya dauke kakaf.

Me wannan baiwar Allah ke yi masu haka a dakuna cikin irin wannan talatainin dare?

Nan ma tafi awa biyu kamin ta fito. Ta diba gabas, yamma, kudu da arewa bata ga kowa ba, sai kurum ta fice ta jawo kofar. Daga kwaryar har tsuntsuwar, sun bace bat.

Wai a wauta irin tata, sai ta sheko da gudu ta lelleka dakunan ko zata ga in da ta aje masu kwaryar da mujiyar? Tunaninnika iri-iri ke shigar ta. Mafi rinjaye shine Hajiya na bakin ciki da cikin da Anty Saratu ke dauke da shi, shine tazo tayi mata wani mugun abu?

Ta sha jin ana cewa Anti Suwaiba aminiyar Hajiya matsafiya ce ta kuma dade tana son sanya Hajiya a turbar tsafe-tsafe Hajiyar na ki, don ita Hajiya na daga cikin irin matan nan da basu yarda cewa asiri shi zai kwato masu miji ba sai power din su da kaifin bakin su.

Wato yanzu cikin Anti yasa ta bi layi kenan? Har aka yi kiran assalatu tana rakabe a bayan labule cike da tunani da tsoro.

Ba ita ta fito ba sai karfe biyar na asuba a lokacin da ta ji masallacin da ke makwabtaka da su ya kira sallah, jikin ta ba inda baya rawa ta shiga toilet din dakinta ta dauro alwalar sallar asuba, ta fara da raka’atainil fajr kamin ta bada farali. Ta kara da nafilfili na musammam tana mai rokon Allah ya kare su daga duk wani mai nufin su da mugun abu. Ta cigaba da karanta Suratul Kahfi har zuwa wayewar gari. Nan akan sallayar barci mai nauyi ya sureta.

Da safe ta fita baiwa ‘yan aikin su umurnin abinda zasu hadawa Daddy da Anti karin kumallo, sai ta jiyo motsin Antin a daki, kamar tace wayyo Allah! Taso ta gayawa Antin abinda ya faru a daren jiya tun kamin ta shiga dakin gashi ta riga ta shiga.

Tayi tunanin fadar ma bashi da amfani tunda yake ita din ma ai ta shiga, ko ta fada sai dai kurum ta tayar mata da hankali a zo a bata tara daya bata gyaru ba, don tasan halin Mamarta sarai cewa za tai sai anyi abinda za’ayi a gidan kuma kenan ita ta tayar da tarzoma ana zaune lafiya?

Ta amince ta kuma hakkake cewa a duniya babu wanda ya isa yayi masu abinda Allah bai masu ba, to akan me zata dami kanta? Sai kawai tayi watsi da al’amarin.

Sati daya da faruwar wannan rannan Daddy na sassan su, a lokacin tana kwance a dakin ta tana nazarin wani tsohon littafin larabci na Alfu-Lailah (Dare Dubu Daya), kamar a mafarki, sai ta jiyo Daddy na zagin Anty Saratu yana cewa,

“Ke har kin isa ki gaya mun magana, naki in maidata makarantar, ko an gaya maku tono kudin nake?

Idan bazaki maidata FGC Kazauren ba da kudin ki, kar Allah ya sa ta je, an gaya maki na damu da harkar ku ne matsiyatan banza da baku san ku taimakawa mutum ba koda kwandala sai dai ya baku, mts!� Ya ja wani dogon tsaki ya fice a fusace.

Kirjin ta ya wani irin buga, jikake dammm! Me kunnen ta ya jiyo mata haka? Daddy ne yake cewa bai damu da su ba balle karatunta? Kai, wannan mafarki ne it’s only a bad dream (mugun mafarki ne kadai) bazata taba amincewa da abinda kunnuwanta suka jiyo mata a yau ba. Tayi saurin yasar da zancen shiyasa akace sauraron hirar mutane ba kyau, don wata rana bazaka jiyo wa kanka alkhairi ba.

To Allah ya gani dai ita ba saurara tayi ba shi Daddyn ne yake yi da karfi. Ta kudurce daga yau koma waye yake magana da karfi, in har ba da ita yake ba to zata toshe kunnuwan tane.

To sai me? Ta hadawa daddy abincin rana na Dolmah Stuff Cabbage, Fried Beef da Stuff Atomy a washegarin ranar. Duk gidan ya karade da kamshi a lokacin yana sassan Hajiya, to ta saba inda duk yake nan take kai mai abincin duk ranar girkin Antin in tayi ko antin tayi.

Daddy da Hajiya na bisa tebur suna cin abinci, tayi sallama amma ba wanda ya amsa bata kawo komi a ranta ba cikin dariya tace “ayya Daddy, nayi latti ko?�

Dai-dai sanda ta aje tray din a gabansa. Wani uban kallon tsiya da ya bi tangarayen da shi ya tsoratata ya ce,

“Ke daga yau ke da uwar ki kada ku sake wahal da kanku wurin dafa min abinci, don na gaji da gishirin da kuke cika min, right?�

Idanun ta suka ciko da kwallah, gwiwoyin ta suka sage, ta tuna tun tashin ta kullum ta yiwa Daddy abinci yabawa yake ya sa mata albarka, haka anti Saratu. Dai-dai da rana daya bai taba cewa ga abinda bai mishi ba a girkin su sai girkin Hajiya.

Rannan ya ce inda ba’a kan idon shi anti Saratu ta karanci ‘Insurance� ba da ya ce nutritionist ce, ko yaushe suke cika gishirin oho! Abinda ta ji kwanaki ke neman zama gaskiya.

A tsukin ta lura kwata-kwata Daddy ya dauke kafar sa daga sassan su haka Aunty Saratu ta daina girki amma dai-dai da rana daya bata taba nuna mata hakan a fuska ba.

Data gaya mata abinda yace kwanaki game da girkin su sai tace wai itace tayi kuskure ta sanya mishi gishiri (3-spoon) kwanaki a dankali. To amma me?
Chapter 46 · 0% Book details