← Book details Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 90

Sashe 18

Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba daya suka rude, kasancewar duk suna jin sa a tare, shi ma hakan handsfree.

“Nawa-nawa za ka fara amsawa Daddy.�

“To ku yi mun uzuri my dear soldiers, Antin ku ce ‘in labour�, so ku bari in ji da zuwan our newly born baby.�

“Eho!!! Daddy Anti amarya haihuwa za ta yi? Amman mace za a haifo mana ko?�

“Ga Sam nan na turo shi ya dawo da ku in kun zo kun gani.�

Ya rufe wayar ya dubi Saratu da ke ta faman lallashin baby ya bude mata hannuwan shi duka, ta tafi da sassarfa sai kuma ta kara da gudu-gudu ta shige, ya maida ya rufe su ruf, ita da babin ya shiga rada mata cikin kunnuwanta.

“A kullum shi yasa nake dada son ki Saratu, duk abin da ni ke so kina so. In an batamin sai ki shayar da ni farin cikin da ke mantar da ni ni tsoho ne. Allah ya yi miki albarka ya kuma sakawa Baffa Sani da ya yi tunanin hada mu aure da alkhairin duniya da lahira. Wannan yarinya Allah ne ya ba mu.�

Ya kwashe duk yadda ya tsinto babin gaba daya ya fada mata har yadda su ka yi da Hajiya kafin ya shigo sashin ta ya fada mata bai rage komai ba. Ta yi salati ta kara kankame jaririyar gaba daya ta ce, “Amman Hajiya ta yi wauta, da ai na kowa ne, kuma ba ka san wanne ne zai ji kan ka ba. Ni kam Allah bai nufe ni da haihuwa ba da kai Baban su Khalil, amma na gode masa da ya kawon ta inda ban tsammani ba.

Na yi alkawarin rike yarinayr nan tsakanina da Mahaliccina ba kuma zan taba nuna mata ba ni na haife ta ba.

Abin yi yanzu shi ne ka je ka rufe bakin wanda duk ya san al’amarin don gujewa bacin rai a gaba, sai in ce Ubangiji Allah ya taya mu riko da amana.�

Ya yi mata kyakkyawar sumba ta nuna kauna da yarda, hadi da godiya mai tarin yawa. Ko a yanzu kimar amaryar shi Saratu ya dadu a idanun shi, hakan nan ya kara ba ta wani matsayi na musamman a zuciyar shi.

“Ni za ni in biyewa shirmen su Furkan, sai ku je Mother’s Delight ki hado mata duk abin da za ta bukata. Daga naira daya zuwa million na yarje miki Saratu ki je ki hado a kawo min bill din.�

Ta yi murmushin da ya fidda siririyar wushiryar ta,

“Har yanzu ban ji sunan Baby na ba?�

“Ai yanka za ai Saratu sati mai zuwa idan Allah ya kai mu, haihuwa fa muka yi, kuma haihuwar ma na ‘ya mace da muke mafarkin samu a gidan nan, kenan dole a yi shagali ko don rufe bakin mutane?�

Ta yi ‘yar dariyar ta mai ban sha’awa ta ce,

“To ai kowa ya san ba ni da ciki, the worst part din ma yadda ku kai da Hajiyar su Aminu, yi tunani?�

Ya yi dan jim,

“Idan har za ta dagawa mutane hankali ne kan abin da aka yi domin neman mafificin lada a wurin Ubangiji, wallahi sai dai ta bar gidan nan, don ba ta isa ta sani ko ta hana ni ba.�

Ta girgiza kai ta yi daki rungume da babyn ta da ta samu barci.

*****

“Magana ce nake so mu yi?�

‘Ba ni da lokaci.�

“To ki aro, ki karkade kunnuwan ki ki ji ni. Dukkanin mu ba yaro a nan, kuma na yi zaton shekarun ki da tunanin ki ya isa ki zama mutum, amma kina halin dabbobi.�

Ta gwalo ido cikin mamaki, “Yau ni ka ke kira dabba Baban su Khalil, a kan tsintacciyar ‘yar ka?�

‘Ni ban ce miki dabba ba, na ce ne kina irin halin su na rashin tunani. To ki ji ba da wai ba, ranar da duk ki ka bude baki ki ka furtawa wani yarinyar nan ba ‘yata ba ce, tsinto ta na yi, babu igiyar aure ko daya a tsakanin mu.�

Ta fashe da kuka,

“Au! Ci min mutunci za a yi saboda ka je ta tsafe ka shi ne za a tozarta ni? Ba ka cewa ka sake nin kai tsaye?�

Ya juya zai fita ta sha gaban sa fuskar nan jage-jage da hawaye, “Na ji ba zan fada ba, amma ina fada ma gaskiya, ba ruwana da yarinyar nan, na tsane ta, Allah tun ranar da ka kawo ta, na fada na kara.�

‘Wannan kuma matsalar ki ce, gafara nan ban hanya in wuce tun ban babballa ki ba.�

‘Ai ban gama ba ne, mijin karuwa, kada shegiyar ‘yar ku ta sake ta shiga sabgar halatattun ‘ya’yana.� Ya nuna ta da dan manunin sa ya ce,

“Nafisa, ke Nafisa ki fitar min a ido in rufe. In ki ka kara kira min mata karuwa, za ki dandana kudar ki, karuwanci har aka fi ki? Ko ba kina karuwancin na aure ki ba?

‘Ya’ya kuwa ‘ya’yana ne babu fitinanniyar da ta isa ta raba mini kan su. Kin san tsintsiya ko? To haka zan maida su. Ki kiyaye zugugun bakin nan naki.�

To kwana biyu dai suna badakala da yin ta ba dadi da maigidan. Ta dai tabbatar Brigadier gab yake da ya guntile tsohon auren su a kan shegiyar jaririyar shi. Yinin ranar zungur kukan bakin ciki ta wuni yi musamman da ya kori ‘yar koren ta Asbi ya ce kuma ko gaisuwa ta sake yi da matar shi sai ya harbe ta ya ba ungulu naman ta, don ya lura sun kukkulla munafurcin su da suka saba. Sam direba da sauran sojojin da ke aiki a karkashin sa duk ya tura su Lagos ya dauko wasu sababbi daga Porthacourt. Brigadier Bello Makarfi kenan, namiji saura mazan jiya, hadari sa gaban ka, guguwa mai fyade wanda ta so, sojan arewa mai watsa shashashai. Wannan ne kirarin sa.

How much do you like this story?
5/7/22, 13:10 - Ummi Tandama😇: ____________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book one

*@Takori*

Page1ï¸âƒ£1ï¸âƒ£

Wane Ne Brigadier Bello Makarfi?

Bello Isyaku Makarfi, mutumin garin Makarfi ne ta jihar Kaduna, Bello ya tashi maraya gaba da baya hannun Baffan shi Mal. Sani ya girma. Lokacin da aka tura shi NDA garin Jos, shekarun shi ba su fi ashirin da biyar ba. Kwazo, himma da sadaukar da kai irin nasa ya kai shi matsayi iri-iri a soja cikin ‘yan shekaru kalilan.

Ya auri Nafisa diyar wani shahararren dan siyasa mai neman kujerar gwamnatin Kaduna na lokacin wai shi Magaji Doller ne tun auren saurayi da budurwa, don dukkansu so ne ya hada su lokacin tana ajin karshe a sakandire, sai bayan auren ne ya fahimci Nafi watsatstsiya ce, irin ‘ya’yan nan da iyaye suka jika da naira, babu kwaba babu hantara kasancewar ita kadai suka Haifa, sai daga baya ne Allah ya nufa ta zauna gidan auren, da taimakon kaunar da take masa.

Gidan iyayen ta yana nan a unguwar Kabala Cutain, cikin garin Kaduna wanda a halin yanzu mahaifiyar ta ce kadai a ciki (shekarun baya ne mahaifin ta ya rasu a hatsarin jirgin sama a kan hanyarsa ta zuwa birnin New York).

Wannan ya ba ta damar zama millionnaire domin daga ita sai mahaifiyar ta kadai suka gaje mahaukaciyar dukiyar da ya bari. Kusan Nafisa ta fi mijin ta kudi don shi ma’aikacin gwamnati ne na kasa, sai dai za a kira irin su top-millitary a yayin da ita kuma ke harkar cinikayyar gwalagwalai daga kasashen Africa daban-ban da sauran kasashen da ke ketaren mu.

Akwai babban shagon sayar da gwalagwalai nata na kashin kanta da ta bude a babbar kasuwar Kaduna, wanda ta sanya wa sunan first born din ta Al’ameen Jewellaries.

Akwai matsananciyar kauna tsakanin ta da babban danta Al’ameen wanda ya ci sunan marigayin mahaifinta ne. Hakan nan sun bude wani a Lagos sai dai na hadin gwiwa ne tsakanin ta da aminan ta Haj. Suwaiba matar gwamnan Kaduna na lokacin da Haj. Badi’a ministar kudi ta lokacin. Sun yi aure yana matsayin Laftanal-kanal a shekarar da suka haifi Mohd. Al’ameen, yana major din shi ta haifi Najib, Faisal da Yasir. Shekarar da mahaifin ta ya rasu ne ta haifi Nasir da Bello mai sunan Daddy da suke kira (Daddy Karami).

Daga Bello ta haifi Faruk sai ‘yan biyu duk maza Idris da Furkan. Dan ta na karshe shi ne Ibrahim Khalil da bai fi shekaru uku ba a lokacin. Kusan duk yaran sun fi shakuwa da Hajiya Saratu fiye da ita ba don komai ba sai don ba ta da lokacin su, harkar kasuwancin ta ya fiye mata komai muhimmanci, ke dai bar ta masifar son ‘ya’ya da kashe masu kudi, amma babu lokacin kula da tarbiyyantar da su.

Duk wata kulawa da ta dace uwa ta kwarai ta bai wa ‘ya’yanta yaran nan sun same ta ne daga Aunty Saratu, tana iya kokarin ta kwarai wajen ba su kulawa ta musamman da ingantacciyar tarbiyya, kai ba ka ce ba ita ta haife su ba, ba ta ko damuwa da habaicin da Hajiyar ke yada mata na “a ci a yi kashi kadai.�

Ita ko rurrutsa ma take wato kwanika, don duk shekara take haihuwa, sai daga kan Khalil ne haihuwar ta yanke mata, don haka kusan gaba daya yaran dukkansu daya, ba za ka iya bambance wa ko kani ba in har ba su suka gaya ma ba da bakin su.

Brigadier Bello kakkarfan mutum ne na sosai, wankan tarwada mai kyakkyawar sura. Da wuya ka yi masa kallo daya ba ka maimaita ba saboda cikar zati da kamala. Mutum ne mai tausayi da jin kai, ya sha fadawa hadarurruka iri-iri a zamanin kuruciyarsa irin dai na kowanne soja, amma juriya da maida kai irin nasa yasa har kullum cikin promotion kan promotion yake.

Bai damu ba don ya sadaukar da ransa kan cigaban kasar shi, Nigeria. Jaridu da mujallun Kaduna kan so buga abin da ya shafe shi saboda yadda jama’ar Kaduna da kewayen ta ke son shi. Ba shi Kaduna, ba shi a Lagos, kuma ba shi Abuja inda duk aiki ya wulla shi anan yake shi da iyalin sa, ayi ta famabn canjin makarantar yara.
Chapter 18 · 0% Book details