Sashe 70
Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A duk iya fadin tunaninta, ta kasa tuno ranar da yarinyar ta kuskurota ko da sau daya, ta kasa tuno ranar da yarinyar ta yi mata ba dai-dai ba. Ta kasa tuno ranar da yarinyar ta hantari ko daya cikin yayanta, duk da fada mata da take tayi da babbar murya cewa ta fita harkar yayanta, domin ita din ta tsane ta. Ta kasa tuno inda yarinyar ta taba gayama wani abinda take mata koda da subutar baki ne kuwa, har kuwa mahaifiyar ta, bata jin ta gayawa Saratu irin rikon da tayi mata a bayan ta. Kai iyaka tunanin ta bata taba ganin yarinya mai hakuri da yakanah kamarta ba, shin maye laifinta don Aminu ya so ta?
A kan me bazai so ta ba? Tana da qualities da dama da zaa so ta a kan su, me tayi mata ta tsaneta?
Rashin iyaye? To ai kowa ma zai iya rasa iyayen sa, ko ita a yanzu mhaifinta ya rasu, da uwar ta take zaune, sai a tsaneta?
Shegiya ce? To in shegiyar ce ma ai ba ita tayi wa kanta ba, ba ita ta jawa kanta ba, itama hakan ta budi ido ta tsinci kanta, kuma ko yau ta mutu zata shiga Aljannah kamar sauran halattattun yaya in har ta yi aiki na kwarai. Ko a yanzu ta tabbata da yarinyar zata fadi ta mutu, to bata da kaico a rayuwa!
Uwar rikonta da uban rikon ta kullum cikin shi mata albarka suke, bata wasa da lokacin sallolinta guda biyar duk rintsi, duk gajiya, duk sanyi, duk ciwo sai ta ganta tana sallah da asubahi, sai ta ganta tana sallah akan lokaci har wani mulmule ne baki wuluk bisa goshinta sabida tsabar sujjadah, kullum Kaman ana kara tisa shi ya fito radas.
Bata taba jin ranar da harshen yariyar yayi ashar irin na su Khaleel ba koda da kuskure ne kuwa. Bata taba jin ranar da wani ya budi baki ya furta wani kalami ga yarinyar, wanda ba na yabo da alheri bane.
Zata rantse wannan yarinyar bata san meye iskanci da shaidanci na wannan zamanin ba, da yammata suka sa a gaba, batasan kallace- kallace da karance karancen banza na zamani ba, bata san bata lokacin ta a abinda bazai amfane ta ba, to meye laifin ta? Me ta yi mata?
Ta tsaneta domin Daddy Makarfi na son ta fiye da kowa cikin yayan sa? To amma in tayi tunani duk wani da mai hakuri da biyayyah ya kan samu mafificiyar kauna a zuciyar iyayen shi. Idan Bello Makarfi bai tausasa mata ba, ina zata je ta a tausasa mata? Ina zata je ta ji dadin rayuwar ta? Bata da kowa, sai su sai Allah da ya halicce ta, ya dace tayi wa Makarfi uzuri akan wannan, in haka ne to meye hujjar ta na tsana da tsangwamar wannan baiwar Allah?
Babu! Illa ita din mutum ce mai son kanta da yawa, mai biyewa sharrin shaidan da rudin zuciya, abinda Allah ya hore mata bai sa ta gode masa ta fuskanci abinda zai anfaneta ba, aah, ta wanzar da muhimmin lokacin ta wajen nuna tsana da kyara ga wata kankanuwar halittar Ubangiji da bata tare mata komi a rayuwa ba, ta biyewa sharrin kawaye da dukiyar da Allah ya hore mata, maimakon tayi aikin lada da su ko sadakatul jariyah, aah, sai ta bata su ga tsafe-tsafen banza, wanda aka ce gaskiyar mai shi ne domin a yau, babu ya wargaje! Ba abinda hakan ya kare su da shi, Allah ma kadai ya san irin farin cikin da Saratu da Saratu da Bello Makarfi suke ciki a yanzun.
Ga dai gidan tana gani, ta sha wucewa ba sau daya ba ba sau biyu ba ta gabansa, amma ya gagareta shiga. Bai sake ta ba. Ta tabbata a zahiri ba kishi ko zafin ranta ne ya hanata komawa gidan ba, illa ita din ji ta ke ta kaskanta, ta wulakanta, hakannan bata da idon da zata dubesu, ko ma tace kwata-kwata ji take gidan yafi karfinta. (To tun a duniya kenan wata shariar, sai a lahira)!
Shin ma anya ba hakkin su ne ya rikide ya dawo kan yayanta ba? Wannan soyayyah da Faisal da Ameenu ke wa Intisar, ta tabbata ba kadan ba ce, kwayar idanun su ya nuna, komai na jikin su ya nuna, ta tuna Almeen magana yake amma a zahiri fatar bakin shi ce kawai ke motsi, a sanda ya ke cewa zai daina sonta zai daina kaunarta, in har hakan zai sa ta yafe masa
Wasu hawaye suka kara zubo mata, wannan shi ake kira nadama mara amfani. Inama ba tayi ba, inama bata aikata duk wannan ba!
Wani bangare na zuciyarta ne ya tunatar da ita cewa ai akwai sauran lokaci, lokaci bai kure ba, da zaki gyara bayan ki, ki nemi gafarar kowannen su, dukkanninsu masu sanyi ne (musamman Alameen) tabbas zasu yafe miki, ba tare da wani jan rai ko bata lokaci ba, kuma hakika zasu yi farinciki dukkanin su, idan kika nemi afuwar Intisar din nasa zai yi farin ciki da hakan.
Wannan tunanin ne ya dan sanyaya mata, ta mike domin dauko wayar ta, ba wanda tayi tunanin fara kira sai Almeen tana mai saka irin tausasan kalaman da zata yi amfani dasu wajen bashi hakuri, tare da tabbatar masa da amincewarta 100% kan bukatarsa.
Kuma tace da shi a washagari yazo ya dauke ta ya maida ta dakin ta, ya danganata ga Intisar ta nemi gafararta ta sa mata albarka, ta nemi gafarar mijinta da abokiyar zamanta su koma zama na amana da aminci kamar yadda tun farko Saratu babba ke so su yi.
A yayinda ta kai hannunta ga wayar, a yayin ne zuciyarta ta yi wani irin mummunan bugu irin wanda bata taba yi ba a rayuwar ta. Lokaci guda yawun bakinta ya tsinke, hakannan tsigar jikin ta ya tashi yarrr! Dai-dai sanda agogon dake makale a bango ya ke kada karfe biyu na rana, cikin daddadan sautin da yafi mata kama da wakar Bankwana!
A Gidan Bello Makarfi
Dawowarsa kenan daga sallar Jumaa da sassarfar shi, cikin takun sa mai karfi ya doshi sassansa, to amma tun safe yau haka yake sukuku ba kuzari. Aunty Saratu ta karaso ta amshi brief-case daga hannun shi da bakar suit da ya ratayo a kafadun shi, lokaci guda kuma tana loosing tie din shi tare da yi mai sannu da zuwa.
Bai amsa ba hakannan dai ya wuce zuwa toilet, tayi zugudiii a falo da taguni da hannuwa bibbiyu, cike da tunanin me ke damun Daddy a yau ne?
Daga can gefe wayar shi dake cikin aljihun suit din shi da ta aje ke ta tsuwwa, ta fiddota da nufin mika masa toilet amma ganin sunan mutumin da ke kiran ya dan kadata, Commissioner of Police Adams Stacy, kawai sai ta amsa ba tare da wani tunani ba.
Ya fara ne da magana cikin nutsuwa cewa ta sada shi da Markarfi direct wato kai tsaye inda ita kuma ta nuna baya kusa, ya fada mata ko minene in ya fito zata fada masa, shi kuma ya dage kawai ta bashi Makarfi har ranta ya baci ta kashe wayar, ta cillata bisa kujera.
A dai-dai lokacin daya fito daga toilet din, ba kuma tare da ya tambaye ta ita da wa take magana a waya ba kawai ya hau darduma ya zauna, can kuma ya mike ya fuskanci gabas ya tada sallah da ba zata ce azahar ce ko laasar ce ba, don kuwa dawowarshi kenan daga sallahr jumaa, kai da alama bama ya son magana kwata-kwata kuma baya cikin hayyacin sa, ta tambayi kanta ko rashin nutsuwar sa na da alaka da kiran da aka yi masa yanzun? Oho!
A irin wadannan lokutan itama bata faya takura masa ba, baya-baya take da shi har zuwa lokacin da shi da kansa zai ware ya kulata, sai ta maida hankali bisa jera abinci bisa tebur.
A sannan ne wayar ta cigaba da kara ba kakkautawa amma bata ko dube ta ba, ta tabbata mutumin dazu ne, ta tsani mutum mara yarda da kafiya.
Sai da ya sallame sallar a lokacin wayar tayi burarin ta har ta gaji ta katse ta kama wani, ya mika hannu ya dauki wayar ya ce,
Hello?
Daga can bangaren mutumin ya ce,
Your excellency, Stacy Adams ke magana daga ofishin yan sanda da ke Minna yace na gane ai, akwai lambar ka a waje na, ina fatan dai lafiya?
Yayi dan jim, yayinda zuciyar Daddyn ta shiga harbawa da sauri da-sauri, ya tabbatar wannan shine sakamakon mugayen mafarke mafarken sa a dan tsukin, sai dai ya ambaci (Innalillahi) a zuciyar sa yafi sau talatin tun ma kafin ya ji mabbabin kiran. Yayi karfin hali ya ce ina sauraronka. Mutumin ya ce cikin tattausar murya
Your edcellency, muna tare da gawar dan ka Dr. Alameen Bello Makarfi, ya yi mummunan accident akan hanyarsa ta zuwa Abuja daga Kaduna, wanda bincike ya nuna yafi minti talatin da sakin sityarin motar shi wanda hakan ya janyo hatsarin motoci fiye da goma akan titin, babu wanda ya tsira a cikinsu.
So ku zo babban asibitin Minna ku karbe shi da kayayyakin da ke cikin motarsa da ke tare damu. Ina mai yi maka taaziyya, hakika rasa mutane irin su M.A.B, ba karamar asara ba ce, ba ga iyayen su kadai ba har ma ga alummar Nigeria bakidaya.
Hawaye na kwarara daga idanunsa, irin wadanda bai taba zubarwa ba, har kuwa lokacin da aka yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai da san da ya rasa iyayen sa! Ya ce,
“Daga Allah muke, kuma gareshi zamu koma. Alameen Allah ya ji kan ka, ya sa mutuwar ta zamo hutu a gareka, ya baka Aljannar Firdausi madaukakiya, ya yafe maka kurakuranka, ya inganta aiyukan ka na kwarai, ya shafe zunubanka, ya sa ka zamo Da mai ceto ga iyayen sa.�