← Book details Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 90

Sashe 48

Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sannu a hankali ta kai hannun ta ga goshin ta wanda take ji yayi mata matukar nauyi, to ba abin mamaki bane da taji shi ya haye yayi suntum sakamakon watsota da Hajiya tayi dakin da ka.

Ta motsa da kyar, kasusuwan ta suka bada wata matsiyaciyar kara a sa’ilin ne ta fahimci a dandaryar marbles take kwance kasancewar ciki da wajen gidan Brigadier da marbles aka yi shi.

Lokaci guda zuciyarta ta shiga tariyo mata abubuwan da suka faru tamkar a majigi. Ta tabbata kyakkyawar rayuwar su ta da ta zama tarihi kenan. Ta rabu da MAMAR TA, bata kuma da halin tadda ita, hakannan Daddy ya juya masu baya tamkar bai taba sanin su ba tsayin rayuwar sa.

Daddy ya dankata a hannun Hajiya, matsayin ‘YAR AIKIN TA ba shi kuma da bukatar ganin ta kwata-kwata. Zata so kwarai ta ga Aunty Saratu a wannan lokacin, su rungumi juna su koka abinda ya same su. Ita kadai zata iya fassara zuciyar Antin a yanzu, ta tabbata tana cikin kunci ninkin ba ninkin wanda ta ke ji.

Bata taba tsammanin zasu kuma gamuwa da wani bakin-ciki ba a rayuwar su bayan na kulle Daddyn su, ita wai me yasa rayuwar ta ke da SIRADI iri-iri ne?

Ta tuna yadda tun tana mitsitsiyar ta Hajiya ta tsaneta, take fadi a gaban kowa ta tsaneta take gaya mata gaba da gaba cewa ta tsaneta fiye da kowa a duniya to balle yanzun da ta dawo karkashinta, karkashin ikon ta, matsayin bolar daddy ta san ita kam tata ta kare.

Dama dai Faisal na nan ne ta san bata da kaico. Yau ne ta ji kewar Faisal fiye da kowacce rana ta kuma ji haushin sa duka lokaci daya don tana ganin kamar dama ya riga ya san duk abinda zai faru da su a gaba shiyasa yayi tafiyar sa ya bar masu kasar su karata su kadai tun kamin faruwar abin.

Tayi tunani iyaka tunani me suka yi wa Daddy haka da zafi ya sanya su cikin irin wannan ukuba? Iyaka tunanin ta bata gani ba domin a kullum cikin tattashi da tattalin Daddy su ke, da aikata duka abinda yake so da gujewa bacin ransa ita da Anty Saratu.

Dai-dai da rana daya bai taba cewa sun bata masa ko sun yi masa ba dai-dai ba in ban da jinkirta maganar karatun ta da Antin ta yi bayan fitowar sa inda duk ya daura mata laifi.

Bayan wannan bata san wani ba. Ta ji matukar haushin Maman kan rashin kunya da cin fuskar da tayi-tayiwa Daddy har ranshi yayi bacin da ya gwammace yanke masu wannan hukuncin, amma da tayi wani zuzzurfan tunani sai bata ga laifin ta ba don itama yayi matukar bata mata kuma shi bacin rai ba abinda bai sawa�

Tunanin ta bai kare ba taji an murdo marikin kofar dakin an shigo. A hankali ta cira kai ta dubeta, Hajiya ce.

Sanye cikin tsalelen lesi ‘jackard� in banda wani masifaffen kamshi ba abinda ke tashi jikin ta, ke da gani kinsan anyi wa maigida kwalliyan dare ne sai taunar cingam take kas-kas-kas kamar wata budurwa. Ta ja kunshin kayan Dela ta zauna sosai ta dubeta ‘thoroughly� tana murmushi ta ce,

“Saratu mai sunan Saratu, jikar Goggo Jummai!�

Idan kunshin kayan da take zaune a kai ya amsa, to itama Saratun ta amsa, ba kuma don komi ba sai don wani masifaffen tsoron Hajiya da ya kara cikata. Jikin ta ya soma kyarma amma bata ce komi ba. Hajiya ta ce,

“Karkade jajayen kunnuwan ki ki ji ni don kalma daya ta subuce maki cikin wadanda zan furta, kikayi watsi da ita, kamar kin yi watsi da lafiyar ki ne.

Kin ji dai yadda babanki yayi da ke, ba don ma ya roke ni alfarmar kada in gaya maki wani sirri da zai narkar maki da zuciya farat daya ba dana gaya maki ko don in samu zuciyar ta buga ki mace kowa ya huta don banga amfanin rayuwar ki ba a halin yanzu, bata da maraba da ta gawar da ta ki rami, to amma duk ranar da kika kawo ni bango zan farke miki ne yadda bakin-ciki zai kayar da ke in tura ki ramin koda ta karfi da yaji ne.

Na rasa dalilin da ya sa kika shiga rayuwata kika yi kane-kane a zuciyar ‘ya’ya na, bayan ni na tsane ki don haka dole nima in shiga taku in kacaccalata in dai-daita ta, yadda kika dai-daita min ta iyali na kasa jin dumin su, kema kin bar jin dumin uwar ki kenan har abada.

Naga abinda Aminu ya rubutowa Alhaji, cewa nadamar abinda ya aikata gareki ne yasa ya nisance ni, na kuma fahimci Faisal ma don ke ya bar ni. Kodayake bana bakin-cikin wannan tunda ko ko ba komi, na tabbata kin dandani bakin-cikin tafiyar sa fiye da ni, ni ko mai farin-ciki ce da duk wani bakin cikin ki Saratou! Saboda haka ina mai tayaki murnar wannan sabuwar rayuwar da kika shigo, kin san sunanta?�

Ta dubeta sosai tana murmushi ta kanne ido daya ta sunkuyo dai-dai kunnen ta ta ce, “SIRADIN RAYUWA!

Daga tsallake siradi sai me? Sai makoma. Kin san makomar ki Saratu? (ta nuna can cikin kasa da dan yatsan ta), ba kuma kashe ki zanyi ba, don bana kisa, ko kyankyaso ban taba gwada kashewa ba, wani daddatan labari ne kunshe a dan bakinnan nawa zan baki, shine gubar ki, kina sha zaki mace, don nasan rarraunar zuciyar nan taki da Daddy da Mama suka yi kane-kane a ciki, bazata iya jurar sa ba.

Ba wannan ne makasudin zuwa na ba, na zo ne in tsara maki sabon zaman gidan Daddy Makarfi. Da farko dai dama can kin san na tsaneki Allah abin haka yake har gobe na tsaneki Intisar, kin san wannan farin sani ba sai na maimaita ba, to balle yanzun da Allah ya kawon tsuntsun daga sama gasashshe, ba sai in yaga ba son raina, ko ya kika gani?�

Ta kafeta da dara-daran idanun ta, bata san sanda ta ce “haka ne Hajiya� ba.

Tayi murmushi ta cigaba tana irgawa da ‘yan yatsun ta daki-daki.

“Da farko a kullum in kin tashi da Asuba ba bu zancen komawa barci sai kuma na washegari in Allah ya kaimu, zaki dauki tsintsiya da injin shara ki share falullukan da dakunan hutawa da na barcin gidannan gabadaya ciki da bai din su, banda na Daddy, daga yau ba ruwanki da rayuwarsa, abin nufi, manta kin taba sanin wani Daddy a rayuwarki ya zama tarihi! Ko gaisuwa tsakanin ku ta kare!!

Ki share dakin baki da garejin motoci, sai ki tattara kayan abinci ki wanke ki hada mana karin kumallo, duk gidan cin mu da shan mu ya dawo wuyanki, Allah ya so takaita miki wahala yarana duk suna kudu sai ‘yan biyu na da dan auta da girkin gidan kadai ya kashe ki, dama gaki nan a fige ya kazar mayu ‘ya’yan mutsiyatan kauye kawai, ki gyara dakunan su Khalil da sauran kusufa-kusufa da sako-sako na gidannan, ki kula da ‘kitchen� kar in ga komi (out of order).

Haka ‘dining� din gidannan in son ganin shi yana yana sheki da walkiya kamar kullum, ki kula da goge ‘sliding doors�, tagogi da kayayyakin wuta, idan naga kura ko yaya take wannan kinibabbiyar uwar taki ta kauye zan ci.

Bandakuna (toilets) din gidannan ina son a kullum su fi ki fari su kuma fi Faisal dina kamshi. Abinci kullum in ji shi da taste (dandano) irin wanda kika saba yi wa Alhaji a sanda yake Babanki, don cewa zan yi ni na yi, kin ga ai bai dace ya ji shi ba dandano ba ko?� Hawaye na mata lugulgude a fuska tace

“haka ne Hajiya�.

“Yauwa, ashe kina fahimta na. Wannan gilashin da kike mannawa safe da yamma, kina zama tamkar ‘yar India don kyau a fake da laluran ido, daga yau na kwashe su na farfasa na karkarya na zuba a masai. Ba makanta ba, buri na dama ki nakasa, to akan me zaki sami dan jagora ina ji ina gani?

Dama don karatu aka yi su, to karatu ke da shi sai ko a lahira in ana yi, kin ga kuwa ai ba su da amfani ko?� Cikin sheshshekar kuka tace “haka ne�.

Tayi murmushi “ka ji yarinya mai ‘chemistry� komi aka ce kya amsa, ko ba haka na ji tsohon Babanki na cewa kin kware akai ba?� Tace “shine Hajiya� ta tintsire da dariya tace “wai meyasa kike son ‘ya’ya na ne, bayan ni na tsaneki? Har kullum mutum kan yi nisa ne da jinin makiyin sa, ban da ke. Don naji an ce komi Faisal kike ambato, har kuka kika yi da ya bar kasar, yayi miki kama da ‘ya’yan mutsiyatan kauye ne?�

Ta girgiza kai cikin dimuwa. Hajiya ta ce “yauwa! Daga yau kika sake koda kallar min’ya’ya sai na sa wuka na tsokale wadannan lumsassun makafin idanun munafurcin, kina ji na?� Tace “ina jin ki Hajiya� a ranta ko cewa take

…ba Faisal ba, ba Najib ba, ba Khalil ba� duk wani jinin ki ma idan na sake daga ido na dubesa ba da kiyayya ba ki ce ni shegiya ce na amince.�

Hawayen da ke surtu bisa kundukukinta basu katse ba haka bugun bakin-cikin da zuciyarta ke yi bai tsagaita ba, ta dago ta dubi Hajiya Nafi, Hajiya Murmushi kawai ta ke tamkar gonar auduga

“karki manta da wanke ‘fridges� din gidannan dukkan su kullum ranar Allah, ki farke katon-katon na lemuka ki jera mana, randa naga kin sha ko daya sai na maida ke mummunar da babu wani da namiji da zai taba dubarki a duniya da sunan so. Daga rana mai kamar ta yau ko kofar gareji kada ki sake fita, ke sharar garejin ma na soketa, iyakacin ki cikin gidannan nan dakin Dela ga bandakin ta nan shine na amfaninki. Idan zaki shiga gyara cikin gida tabbata asuba ce, lokacin da ba wanda ya fito sai dai mu fito muga komi a kintse.
Chapter 48 · 0% Book details