← Book details Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 90

Sashe 1

Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummi Tandama: ________________
»SIRADIN RAYUWAâœ

*@Takori*

Da Karfe Shidda Na Yamma Agogon Garin Miami

Dr. Al’ameen Bello Makarfi, ke kwance cikin sofa mai juyawa dama zuwa hagu, idanun shi a rufe suke tamkar mai barci, amma a zahiri ba barcin yake ba, shi kadai ya san hakikanin abin da ke damunsa. Alal hakika rigimar matar shi IHSAN ne ya ishe shi a yau. Shi kam tun barin sa kasar haihuwar shi bai sake waiwayar ta ba balle ya tuna ta da sunan zama na din-din-din ba.

America, ta bude wani shafin rayuwa mai dimbin tarihi da nasarori a tare da shi, ta maida shi wane, ta zamo silar dukkanin nasarorinsa a rayuwa ta warkar da bakin cikin kuruciyar da ya zo Miami da shi ta kuma shafe rayuwar shi ta baya, ta wanke tsanar kan shi da yake a da can, shin a kan me zai bar ta?

Sai dai wani bangaren na zuciyarshi sam, ya ki amince mai da hakan. Idan ya yi hakan ya tabbata hakkin yarinyar kadai na iya wargaza masa farin cikin da yake takamar ya samu a Miami; Shekaru goma kenan cif da rabuwarta da iyayenta, shi kuma goma sha biyar cif in har lissafin da yake daidai ne bai rage ba, sun turo ta karatu sun sarke da soyayyar da har ta kai su ga aure ba tare da sanin iyayen ko dayan su ba.

Ta jure rashin soyayyar nan ta iyaye a tare da ita tsayin shekarun nan wadda ta fi komai dadi da muhimmanci ga dan adam, idan shi namiji ya iya ya jure, ita Ihsan mace ce, ya kuma tabbatar ta yi hakuri kan hakuri ba don komai ba sai don masifaffen son da take masa. To shi don me ba zai nemo mata wannan soyayyar ba, ko don albarkacin wadda take masa? Shi kansa ya san a yanzun zuciyarsa ta yi sanyi da takaicin kuruciyarsa ta gida.

Tunanin Daddy din shi ya addabe shi, ko an harbe shi? Ko har yanzu yana kulle a kurkuku (Prison)? Zuciyarsa ke bijiro masa da cewa, yanzu ne ya dace ya je ya tallafi mahaifiyarsa da ‘yan uwansa duk da ya san a kowanne hali mahaifiyarsu za ta iya kula da su, kasancewarta mace mai dumbin arziki. Yana ganin yanzu ne ya dace Hajiyarsu ta huta da guminsa, shi a yanzu ya san Allah ya yi masa ludufi da nasibi ta kowanne fanni a rayuwa;

Bar ta kasancewarsa mamallakin shahararren asibitin kwakwalwa wato “MERITIME� da ke cikin birnin Miami, hakan nan shi ne babban likita a sashen kwakwalwa (consultant) a babban asibitin garin Miami (Jackson Memorial) da ke Florida. Har ila yau, Dr. M.A.B (Senior lecturer) ne da ke daukar daliban “Medical Psychology� a jami’ar da ya yi karatu (University of Miami), kuma masani a kan duk wata larura da ta shafi kwakwalwa. Don haka kasar America ke ji da shi, suna lailayar shi da ruwan arziki kasar su na amfana da dumbin baiwa da fasaharshi. Baya ko tuna kasar shi ta haihuwa (Nigeria) balle iyayen shi da ya tafi da niyyar barin su har bada, don yana ganin ba abin da zai masu, ‘ya’ya irinsa ba abin bukata ba ne, don haka bashi da amfani a gare su. Ga ingantacciyar kauna da kulawa daga matarshi abin kaunar shi Ihsan, yalwataccen gida a Miami, motocin hawan da ko a U.S. sai wane da wane.

Kenan duk wani buri da dan adam zai iya ciwa rayuwar duniya, ya samu. To amma zai so ya mutu ba tare da sanin halin da iyayen shi ke ciki ba? Ba tare da ya kara sa wani jinin shi a idanun shi ba? Bai sake sanin halin da kanwarsa SARATU-INTISAR ke ciki ba, shakikiyarsa kuma kanwarsa da ya NAKASTA?

Mafarke-mafarken da yake na Daddy a dan tsukin kadai na tayar masa da hankali, ya kasa nutsuwa kwata-kwata wanda hakan ya janyo masa yi wa wani mara lafiya (Patient) rubutun magungunan da ba su dace da lalurarsa ba, ba don Ihsan ta lura ba da an yi mamakin shi M.A.B ne da wannan danyen aikin. To haka ko rubutu yake yana daburcewa ya rasa me zai rubuta?

Gaba daya hankalinsa ya yi gida ya kuma tabbatar kwanciyar hankalinsa kadai ya bude ido ya gan shi a gida.

Baya jin zai sake samun nutsuwa bai baro Turai haka nan ba. Anya ma kuwa babu hakkin Dady din shi a kan shi? Mutumin da ya wanzar da ran shi da lafiyar shi cikin wahala, domin nema masu farin ciki, anya ya cancanci hukuncin da ya yanke masa?

Bar ta so da gatan da yake nuna masa throughout sauran kannensa to haka Hajiyarsa, ya tuno yadda a kullum take gaya masa ba ta son ya yi nisa da ita, ya fiye mata duk sauran ‘ya’ya taran da ta haifa a duniya! Sai ya ji kansa ya yi wani irin gingiringim, idanuwansa sun yi mai nauyi, baya ko iya bude su. Ya lumshe ido cikin wani sabon yanayi a tare da shi. Allah kadai ya san halin da zuciyarsa ke ciki.

Ihsan ta karaso rike da tambulan mai garai-garai cike da danyar madarar shanu mai sanyi (fresh) wadda shan ta ya zamewa likita Ameenu lazim a duk yammaci, a gida ne ko ofis. Sanye take cikin fararen kayan wanka (bikini), gashin kanta ke digar da ruwa tabbacin daga wanka ta fito. Ganin yanayin da Al’ameen ke ciki sai ta ja dan karamin tebur da ke gabansa ta ajiye kofin.

Sannu a hankali ta kwanta jikin Al’amin sannan ta marairaice kamar za ta yi kuka ta ce, “Ameenu isn’t this enough? America is not our motherland�. Don Allah mu koma gida…� Sai kuka.

Shiru ya yi cikin tunani, shi kam bai san ma abin da zai ce mata ba ma. Zuwa gida? Ai shi ne mai cewa a je ba ita ba yanzun. Bai ce komai ba, baya ga dora hannu cikin gashin kanta, don in ta soma yi mai wannan rigimar ta “a dawo gida…� da kyar yake iya samun kanta. Hakika tana ba shi tausayi, dole su baro MIAMI a wannan watan.

*****

1 GA WATAN SAFAR (HIJRIYYAH)

Jirgin American Airways ya sauke su a birnin Ikko da karfe tara daidai na safe. Sai da kowa ya fita amma Al’ameen da Ihsan ba su ko motsa daga “seat� dinsu ba. Gaba dayansu jikkunan su sun yi sanyi, domin a take zazzafan zazzabi ya rufe Ihsan, ba su san da fuskokin da za su aro su dubi iyayensu ba.

Sai da wata ma’aikaciyar jirgin ta yi masu magana cewa za a rufe jirgin, sannan ne Al’ameen ya tuna cewa shi fa namiji ne, ya rungume matarsa da hannunshi na dama a yayin da na hagun ke rike da ‘yar kyakkyawar jakarta ‘Japanese� a haka suka soma tako matattakalar jirgin cikin nutsuwa har suka taka kasarmu mai dimbin albarka.

Dole idan ka kalle su sai ka maimaita su kuma yi bala’in ba ka sha’awa. Kwarjini da cikar zati irin na Al’ameen da ke sanye cikin edpensive Italian suit, kalar baki da ratsin fari sol sun taimaka ainun wurin kara fiddo ilhama da cikar zatin shi, ya saya kwayar idon shi cikin bakin dark-spaces da ganinsa dai ka ga bakon Ba’amurke. To haka itama Ihsan din tamkar aljana take don kyau, baby face gareta mai dauke da kayatattun idanu tare da kyakkyawan dogon karan hanci da gassun gira mai tsari. Yarinya ce ‘yar gajeriya mai jiki kuvul-kuvul, kamar na tarwada saboda tsabar hutu tamkar ba bakar fata ba, domin tun fil’azal ita brown ce, sai kuma zaman kasar sanyi da jin dadin samun gwarzon miji irin Al’ameen Bello, da suka kara wanke ta tas.

Dr. M.A.B zai yi wuya ka fassara daga kabilar da ya fito a lokaci daya, kamannin shi na da ruda tunani da sanya shakku, bi-ma’ana (by appearance) ba za ka kira shi Bahaushe ba sam-sam duk da cewa ya fi son yin magana da harshen Hausa a kodayaushe fiye da duk wani harshe da ake magana da shi a duniya. Hakan nan ba za ka ce shi din Balarabe ba ne, domin baya da tarin nannadaddiyar suma irin tasu kullum kansa cikin saisaye yake, amma ya bar siririn saje a gefen fuskarshi abin nan da ake kira Man’s pride. Mutum ne dogo siriri, don tsayi har ya rankwafa, wanda mutane da dama ke (kuskuren tsammanin) cewa yanayi ne don kwalisa, amma Al’ameen Bello komai nashi natural ne babu artificial. Idanun shi abin so ne, ba ga mata kadai ba har maza ‘yan uwansa will not keep wishing they were like him (Ba za su bar fatan ina ma a ce sune shi ba).

Idanuwa ne manya kuma lumsassu, tamkar kuma an diga masu zaiba har wani maiko-maiko suke. Bai kama da Turawan ma sam-sam shi dai kawai Al’Ameen ne, haka Allah ya yi sa.

Da wuya ka karanci zuciyar Al’ameen Bello, ko matar shi ba ta iya gane wasu al’amuran shi. Mutum ne murdadde mai yin komai straight forward (kansa tsaye) ba tare da tunanin illar da abin zai haifar ba, mai tsayawa a kan mgana daya, ba kankanin abu ke sa shi canza ra’ayi ba. Kuma mutum mai tausayi da masifaffar kyauta. Ya sha sauka daga mota in ya ga wani a gefen titi yana jiran bus a Miami, ya kira shi ya danka mai mukullin ya ce, “Tafi.� Shi kuma ya sayi wata.

Tun Ihsan na masifa har ta gaji ta kyale shi don ta lura abin a cikin jinin shi ne. Ita kanta ba karamar barna yake wa kayan ta ba wurin baiwa masu karamin karfi dake tareda su. Sau tari, tana kwance a mike ya kan dafa mata abinci, ya dauko ya kawo mata yana sanya mata a baki, yana mai lallashinta ta ci sosai.

Cewa yake wannan hakkinshi ne ya ciyar da matarshi, tunda a Alkur’ani mai tsarki babu inda aka ce mace ta ciyar da mijinta hakan nan bai son mata suke wahala, domin su ne uwayen al’umma duk wata wahala a wuyan su take. Idan suna nakuda ji yake kamar ya taya su.
Chapter 1 · 0% Book details