← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 75

Sashe 9

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Girgiza kanta Haseena tayi tace, "ke ba ki san irin ƙaunar da nake mishi ba, bazan iya rabuwa dashi ba, SHAREEF wani ɓangare ne na jikina, koma in ce ya zama jinin jikina, bazan iya rabuwa dashi ba, nawa ne shi Ni kaɗai, kuma bazan taɓa bari wata ta same shi ba bayan ni, ina da auren sa a kaina yanzu kinga dole in ɗauke sa ya dawo gare Ni na har abada, ina son ya so ni Ni kaɗai ya manta ɓacin ran da na sanya mishi, zan iya aikata hakan ko?"

Wani kallo Nana ta watsa mata da cewa, "No bazai yiwu ba, domin akwai sharaɗi a tsakanin mu, Haseena, you still don't know how much I love you, right? Idan ya dawo gare ki zai yi mana katanga a tsakani, don haka bamu buƙatar sa a nan, ki manta da zancen sa in har soyayyarki ce ke kaɗai ce a zuciyarsa, daga ke bazai sake son wata Mace ba bayan ke, zuciyarsa zamu mallaka, kuma duk abun da kike so shi zai yi miki babu gardama, bazai sake miki musu ba ko ya ga laifin ki."

Murmushi Haseena tayi tace, "yeah, ina son haka, Of course, if you do this to me, you're done for me. ina son in mallake shi gaba É—aya ko aina yake bazai so wata Mace ba bayan Ni, domin shi nawa ne, ina sonsa da gaskiya, rasa sa kamar na rasa raina ne."

"Kar ki damu babyna, ki bamu lokaci komai zai sauya, kar ki sake damuwa dashi zai biyo ki duk inda kike so, yanzu lokacina ne, ki shirya mu fita We will meet them Herin, there is a party to go to."

Then they got up and went into the bath together, bayan sun shirya suka fita a motan Nana.
***

_____Gaba ɗaya SHAREEF ji yake yi zuciyarsa na masa zafi da abun da Haseena tayi masa, tabbas Haseena ta dena sonshi yanzu, har shi zai kira wayanta but basu gama magana ba ta kashe? Abun da bata taɓa masa bane, and shima ya kashe bata biyo baya ba, ransa yayi ƙololuwar ɓaci wanda yasa ya kasa ci gaba da aikin, illa ma ɗaura kansa da yayi a saman teburin yana sauke numfashi a kai-a kai, tun ba yau ba ya kula Haseena ta sauya masa, meyasa to? Me yayi mata?
And ita ce ma tayi masa laifi amma take ƙoƙarin ɗaura masa laifin; tare da nuna kamar ba abun da ya faru, wane ne wannan a cikin rayuwarta? Tabbas in ya gano wane ne sai yayi masa mummunar hukunci tunda har yayi ƙoƙarin shiga tsakanin sa da farin cikin sa

Tsawon lokaci ya kasa yin komai sai saƙe-saƙe da yake yi a cikin ransa, kansa ya ɗauki zafi da tunani, ji yake yi tamkar ya dauki waya ya kira ta but ya kasa, ba ƙaramin fushi yayi da ita ba amma zuciyarsa na azalzalan sa, kuma idan yace zai sake kiranta wlh sai ya ɓata mata ranta, shi kuma ba haka yake so ba, a duniya abun da ya tsana shine ya ɓata wa Haseena rai, domin ji yake yi sai ya fi ta shiga tashin hankali da damuwa, Allah ya ɗaura masa soyayyarta da bai san ya zai yi da rayuwarsa ba in ta guje sa

Yana nan kwance da kai a table, har PA ya zo ya sanar mishi lokacin tashi yayi, amma ya kasa tashi, ƙarshe da ya dame shi sai ya daka masa tsawa a kan, "ya bar sa."

Jiki na rawa PA ya fice yana rufo masa ƙofa,
Amma bai tafi ba tunda ya san dole shi zai rufe office É—in,
Yana nan a zagaye a wurin har Hanif ya zo shiga office É—in,
Suka gaisa yana tambayarsa SHAREEF É—in?
"Yana ciki sir bai fito ba."

"Ok." Yace dashi yana duba agogon hannunsa, tare da nufan office din ya shige,
A yanda PA ya bar sa a haka shima ya zo ya tarar da shi,
Da mamaki yake duban sa don ya san babu lafiya tunda ya gansa a haka, bai ma samu zama ba ya soma tambayarsa da lafiya?

Sai lokacin SHAREEF ya É—ago kai yana duban sa, duba É—aya yayi masa ya É—auke idanunsa a kansa

Shi kuma Hanif hakan ya ƙara saka shi a ruɗani sabida ganin yanayin idanuwansa da suka canza launi, shiyasa da sauri ya sake tambayarsa yana cewa, "wai lafiya Bro, me ya faru ne?"

Haɗa kayansa ya soma yi bai amsa mishi ba, don yadda zuciyarsa take zafi da tuƙuƙi ba ya jin zai iya buɗe baki yayi magana

"Don Allah ka faÉ—a min mai ke faruwa ne? Ka saka Ni cikin wani yanayi sabida halin da na ganka, Please Bro tell what's wrong?"

"Bai da wani amfani sanar da kai. Mu je kawai."

Jin hakan ya san cewa bazai faÉ—a mishi ba in har a yanzu ne, sai lokacin da ya mula don kansa,
That's why bai takura masa ba ya miƙe suka fita a tare,
A Mota ɗaya suka zo tunda yawanci hakan suke yi gaskiya, dole in har tare zasu zo Motan Hanif zai shiga ya tuƙa su, don shi bazai yi tuƙi ba,
Kai tsaye gida suka nufa babu mai magana a cikin su, kowa da abun da ya dame sa.
[31/03, 4:32 AM] نفيسة OumƊahira: 🌱🌱🌱🌱🌱

       *SHAREEF*
           _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱

_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*Littafina na kuÉ—i ne, ki biya ki karanta, zaku iya samu na a kan wannan numban wayan. 07065334256.*

__________
*BOOK2*
_______________*PAGE6*
_____Tun daga ranan SHAREEF ya so ya share Haseena daga ransa har sai ta kira sa don kanta, tunda da ita yake kwana da ita yake tashi amma tsaban haushin ta da baƙin cikin abun da tayi masa; shiyasa shima ya so ya share ta gaba daya har sai ta gane kuskuren ta,
Amma inaa; abu kamar wasa zuciyarsa ta kasa sukuni da tunaninta, ga wani irin azalzala da take mishi a kanta, wani irin sabon ƙaunarta yake ji wanda yana jin ko me tayi masa bazai iya fushi da ita ba tsawon lokaci, dole ya ɗauki waya ya kira ta don kansa, kuma a ƙarshe shi ya ƙare da bata haƙuri,
Don yanda take mishi shan ƙamshi tana nuna alamun tayi fushi, duk ya rikice kamar zai yi kuka don yanda ya shiga damuwa, ɗakyar ya shawo kanta don har so yayi ya je Austaraliyan amma ta hana sa

Dama tayi haka ne don ta gwada irin yanda suka kama zuciyarsa kamar yanda ta sha alwashin mallakar sa, yanzu ta gane SHAREEF ya zama nata gaba É—aya, bata da wata matsala kuma shiyasa suka É—aura da soyayyarsu kamar yanda suka saba

Yanda SHAREEF yake jin Haseena a ransa komai zai iya yi sabida ita, abubuwan da suka faru tuni ya manta da komai sai zallan ƙaunarta a rai, ba shi da aiki sai waya da ita ko video calls, a yanda SHAREEF yake matuƙar buƙatar Matarsa a kusa but hakan ya gagara, domin duk sanda ya nuna zai je wurin ta ba ta yarda, ga shi ba ya son ɓacin ranta ko kaɗan,
Sun É—auki tsawon lokaci yana magiyan tabar sa ya zo,
Sai da ta mula sannan ta amince masa, domin a wurin ta zuwan nasa bai da amfani tunda ba abin da zai tsinana mata sai takura,
Ilai kuwa hakan ce ta kasance, duk yanda SHAREEF ya so da samun biyan buƙatar sa a wurin Haseena abun ya faskara, kusan kuka yayi mata a ranan a kan ta amince masa, amma ta ƙi, don kwata-kwata bata da sha'awarsa ko kaɗan, idan ma yana naniƙe mata mugun haushin sa take ji kamar ta kashe shi haka take ji, but idan yana nesa sai ta ji tarin ƙaunarsa, sam ta ƙi basa haɗin kai ko ɗan romancing ɗin da yake samu ya ji dad'i wannan karon bai samu ba, tunda shi kaɗai yake kiɗan sa yake rawansa ba ta taya sa,
Amma babu yanda zai yi tunda already yanda yake jin ta a rai bazai iya ganin ɓacin ranta ba,
Haka nan ya dawo ƙasar babu biyan buƙata, sai na ciwo da ya kwaso wa kansa,
A taƙaice dai; dole ya nemi magani a asibiti ya soma amfani dashi tunda bazai iya zama da cuta yana wahalar da kansa ba, wacce kuma yake so da ƙauna ta hana sa abun da yake so,
Shi yasa duk a kwanakin SHAREEF bai da wani natsuwa ya rame sabida damuwar da ke tare dashi

Hanif ne kaɗai ya san halin da yake ciki tunda shi suke kwana tare, already bai ɓoye mishi komai ba duk abun da ke faruwa ya sani, abun yana baƙanta masa rai a yanda ya ga SHAREEF ɗin ya mutu a ƙaunar Haseena, amma take wahalar da shi ba ta son farin cikin sa, ya sha faɗa masa, "idan da tana son farin cikinsa kuma tana ƙaunarsa; ko mene ne zata iya yi don ta faranta mishi, amma abun da ba haramci zasu aikata ba since ta zama Matarsa, amma take masa wulaƙanci a kai, don haka idan ma zai farka daga wannan barcin nasa da bai da amfani; yana liƙe mata babu biyan buƙata, gwara ya farka ya san inda ya dafa, shi a ganinsa Haseena ba ta ƙaunarsa wlh, idan kuma ba haka ba zai iya kashe kansa a banza a hofi tunda yana zaune da lalura yana biye mata ya kasa amsar haƙƙinsa."

Idan yana wannan maganar kallonsa kawai SHAREEF yake yi, idan ma ya cika sa da zancen sai ya nuna rashin kyautawar sa a kan abun da yake faɗa, domin shi a ganinsa Haseena tana sonsa tana ƙaunarsa, don bata ba shi hakkinsa ba; ba hakan shi zai nuna ba ta sonshi ba, ya san cewa wata rana komai zai wuce da zaran ta gama karatun ta

Murmushin takaici Hanif yake yi, yace, "wlh ko ka so ko kar ka so yarinyar nan ba ta tausaya maka Bro, gwara ka nemi mafita tunda ba ita kaÉ—ai bace Mace a duniya, in fact ma ba ita kaÉ—ai kake aure ba a yanzu, Maryam zata yi maka amfani before ka kashe kanka."
Chapter 9 · 0% Book details