← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 75

Sashe 48

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tsawon lokaci suna wannan yanayin wanda ba ƙaramin galabaitar da Maryamu ya soma yi ba,
Don abubuwan da yake mata hankalinta ya gaza dauka abun ya wuce tunaninta,
Tun tana iya enjoyed abun har takai ga ta soma tsorata sabida yanda SHAREEF yake sarrafa ta da zafin shi babu ragowa bare sarara mata,
Nan fa ta soma dawowa cikin hayyacinta; domin har ya soma ƙoƙarin zare mata wandon ta,
Da sauri ta kama wandon cikin tashin hankali tana girgiza masa kanta, domin a wannan lokacin baza ta iya magana ba

"Please ki bar Ni kar ki hana Ni, kar ki hana Ni zan mutu, don Allah ki taimaka min."
Abun da ya iya furta wa kenan kamar zai yi kuka yana shige mata tare da tusa kansa a ƙirjinta yana fitar da numfarfashi,
Hannunsa ɗaya yana saman wandonta yana ƙoƙarin cire mata shi dole

Amma Maryamu ta ƙi yarda, domin a wannan lokacin abubuwan da ya dinga mata suka soma dawowa cikin kunnuwan ta, sam SHAREEF ba abun a tausaya mishi bane, domin shima bai tausaya mata ba, ba ta shigo cikin gidan sa bane don ya same ta da sauƙi har haka ba, dole sai ta nuna mishi muhimmancin ta baza ta taɓa amince wa dashi ba sai ta sa yayi nadamar duk abubuwan da yayi mata, sai ya durƙusa a gabanta ya bata haƙuri sannan zata iya yafe mishi, ya cutar da ita ba kaɗan ba, wanda yasa take a nan hawaye suka soma zubo mata, jikinta ya soma rawa haka ma laɓɓanta da take ƙoƙarin yin magana amma ta kasa,
Tana son ta cire sa a jikinta amma ta kasa sabida ƙarfin ta ya gaza, shi kuma ya zame mata kamar maye tamkar ma kuzarin sa ne ya dawo fiye da na baya,
Ganin yana ƙoƙarin afka mata da ƙarfi da yaji don ya zare wandon nata saura pant,
Kuka ta fasa bata da wani zaɓi illa ta haukace masa nan take,
Lokaci guda ta fara ihu da bige-bige tana yakushin sa iya ƙarfin ta

Wanda tuni SHAREEF ya soma dawowa tunaninsa, domin yanda ya ga Maryamu ta haukace masa tana ihu da kururuwa, tana kai mishi duka ta ko'ina; azaban da yake ratsa shi tuni ya dawo hayyacinsa don har tulin gashin sa ta kama tana jan masa kamar zata tumɓuke mishi,
Da sauri ya soma ƙoƙarin ɗaga ta don gani yake yi kamar zata iya kashe sa,
Abun ya soma ba shi tsoro sabida ganin sosai take zabga uban ihu tana birgima kamar ba a cikin hayyacinta take ba,
Baya ya ja jikinsa na rawa hankalinsa a matukar tashe, don tsab ya gane Aljanunta ne suka tashi,
Ba karamin tsorata SHAREEF yayi a wannan lokacin ba, domin a yanda ya ga ta haukace ihunta yana ƙaruwa abun ya tsorata shi ba kaɗan ba,
Saurin miƙe wa yayi ya rasa abun yi sai dube-dube yake yi,
Da sauri kuma ya nufi hanyar kitchen ya je ya dawo batare da ya ɗauko komai ba, a yanda ya tsorata da halin da take ciki har jikinsa babu inda ba ya rawa, nan da nan ya haɗa gumi duk da babu kaya a jikinsa daga shi sai guntun wando, tunɓur-tunɓur haka yake yawo ya je nan ya je can ya rasa abun yi

Wanda Maryamu na kwance itama babu kayan daga pant sai hulan kanta da bai cire ba, a yanda take haukan da fitar da ƙara zaka ce gaske ne, nan kuwa tsab hankalin ta a jikinta yake,
Tana sane ta haukace tayi tamkar Aljanu ne a kanta sabida ta samu ta tsira,
Duk abun nan da take yi tana ganin yanda SHAREEF ya rikice yakai ya dawo yana yawo tuɓur-tuɓur, hakan ba ƙaramin bata dariya ya so yi ba, amma sai ta maze ta ci gaba da ihun har da kiran, "wayyo Allah Inna, wayyo ki zo ki taimake Ni zai kashe Ni, wlh zai kashe Ni, ga shi nan, ga shi nan."
Ta soma nuna inda SHAREEF É—in ke tsaye yana fitar da gumi

Da sauri ya tsayar da tafiyar da yake yi yana juya wa gare ta, a rikice yace, "ki yi haƙuri bazan sake ba, Ni ne? Ni ne ko? Na daina bazan sake ba. Don Allah ki yi hakuri. stop... Stop cry."
Ya rikice ma bai san mai yake furta wa ba,
Sai kuma ya juya da gudu ya nufi fridge ya É—auko ruwa,
Zuwa wurin ta yayi ganin ta soma rage ihun,
Yana tsaye a É—an nesa da ita yana tunanin abun da zai yi mata,
Shi ba addu'a ya iya sosai ba balle yayi mata ta warke,
Amma haka nan kuma ya bude ruwan ya zuba a hannunsa, yana ƙoƙarin tofa addu'a cikin hannun,
Wai a hakan ne zai yi addu'ar a cikin ruwan,
Amma ruwan tuni ya zirare ya zube

Dariya ya so ƙwace wa Maryamu, sai kuma ta koma ci gaba da birgima ta je nan ta je can

Da gudu ya koma ya sake É—auko cup ya dawo, jikinsa sai rawa yake yi haka yayi ta maza ya tofa addu'o'in a cikin ruwan ya watsa mata

Daga nan ne Maryamu ta soma barin abun da take yi, ihun ma ta dena ta koma sauke numfashin azaba, don ita kanta ta gwagwatu; duk ta gama ƙwale kai,
Shiru tayi ta rufe idanunta tayi kamar mai barci

Sai lokacin fa SHAREEF ya ji sauƙi a ransa, ya durƙushe ƙasa yana faman sauke numfashi hannunsa a saman ƙirjinsa, tabbas ba ƙaramin tsorata yayi ba, domin ba kaɗan ba aljanun nata sun girgiza shi, shi dai bai taɓa ganin tashin aljanu ba amma a ransa yana jin tsoron su tunda yana yawan jin labaran su, a baya lokacin da take ciwo yana ganin yanda Momy take fama da ita, a lokacin bai taɓa jin tausayinta ba kuma bai taɓa zuwa wurin da take ba, sai dai ya ja jiki ya koma ɗaki don ba ya son ma ya gansa kusa da ita,
Sai ga shi yau sun tashi a gabansa, sai yanzu yake dana-sanin ƙin kiran Momy, ai da ta taimaka masa,
Amma kuma ya ji daɗi da suka sauka da wuri, sai kallonta yake yi yana son ya je gare ta but babu hali, ga abincin sa da yake marari yana kallonta babu kaya breasts ɗin ta sun yi cirko-cirko suna tsole mishi ido, but babu halin mayar da kwaɗayi, sai faman haɗiyar yawu yake yi yana ci gaba da ƙare mata kallo amma ya kasa isa inda take,
Sun jima a haka kamar yabar ta a haka yayi ta kallo ya samu Tv,
Amma kuma haka nan ya daure ya nufe ta tare da É—aukar ta ya manna ta a jikinsa, É—akin ta yakaita ya ajiye ta a saman gadonta,
Ya jima yana faman kallonta tamkar ya É—aura hannu a abubuwan da suka tsole mishi ido, but yana tsoron ta farka,
Blanket ya janyo ya rufe mata jiki sannan ya juya a sanyaye ya fice

Tana jin ya rufo ƙofan; ta fashe da mahaukaciyar dariya har da tiƙo wa ƙasa tana shaƙe wa, yau ba ƙaramin muguwar dariya SHAREEF ya bata ba, a yanda ya rikice ya tsorata hakan ba ƙaramin nishadi ya sanya ta, dariya ta dinga yi har da riƙe ciki,
"Oh! Yau nayi maganin wannan Bawa naka, ina ma da mai taya Ni ganin wannan draman? Hohoho Ni Maryamu."
Sai ta sake kecewa da dariya tana miƙe wa tsaye,
Bakin ƙofan ta koma ta saka key sannan ta dawo ta dinga tiƙa rawa tana dariya; farin ciki ya gama cika ta,
"Wlh kaÉ—an ma ka gani, na gode Allah da ya nuna min tsoron ka a fili, ai kuwa na dinga maka haka kenan; sai na rama duk abubuwan da kayi min."
Sai ta kama kumatun ta da dukka hannayenta, "nan gaba har da mari zan kwaÉ—a maka kaji inda daÉ—i."
FaÉ—a wa kan gadon tayi ta kwanta tana rufe kanta,
Cike da nishaÉ—i Maryamu a wannan lokacin tayi barci, barcin farin cikin da ya kwashe ta bata shirya mishi ba, har da murmushi a kan fuskarta.
[26/04, 1:24 PM] نفيسة OumƊahira: 🌱🌱🌱🌱🌱

       *SHAREEF*
           _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱

_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*Littafina na kuÉ—i ne, ki biya ki karanta, zaku iya samu na a kan wannan numban wayan. 07065334256.*
Chapter 48 · 0% Book details