← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 75

Sashe 43

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

__________
*BOOK2*
_______________*PAGE22*
_____Maryamu ta ji daɗin zuwan danginta, musamman da ta ga har da Innarsu, shiyasa ta maƙale musu suna tare,
Dayake daƙunan ƙasa aka basu a nan suka yaɗa zango,
Ire-iren ƴan mata sa'annin Maryamu da su Aakifah, suna ɗakin Maryamun ne su a nan suka kwana ƴan uwan su Momy, har Bintu itama tana cikin su tunda ta ga akwai Maryamu, ga ɗanta da yayi wayon gunun ban sha'awa, sauran cousin ɗin sai mamakin ta suke yi ganin ta ƙarama har da aurenta da Yaron ta, duk da itama auren yasa tayi girma yanzu ta zama Uwa, har ta fi Maryamu tsawon gaɓɓai a yanzu

Maryamu a wurin Bintun ma ta soma jin maganar tarewan ta, lokacin suna zaune a É—akinta suna hira, sauran Æ´an Matan suna yi da Bintun har suna cewa, "ai ta huta tayi auren ta yanzu ta huta abun ta."
Ana dai ta magana ana raha,
Sai Bintun ta raÉ—a wa Maryamun a kunne tana faÉ—a mata, "saura ita, nan da gobe zasu kaita É—akin ta."

Kasancewar Maryamu bata da labarin maganar shiyasa bata É—auki maganar nata da serious ba, sai ma hararanta da tayi tana cewa, "kar ta kawo mata maganar banza, ita da ta zauna a É—akin Miji sai ta haÉ—a degree É—in ta na farko."

Su Aakifah suka kwashe da dariya kasancewar sun san halin ta a gida, domin ta sha haÉ—uwa da Samari idan sun yi mata zancen soyayya ta balbale su da masifa tana gaggaya musu maganganu,
A nan fa zancen su Yusaira ya koma kan maganar nata suna bama Bintu labari

Bintu tace, "ashe har yanzu halin ta yana nan? Wlh haka take yi lokacin tana ƙauyenmu, ai Samarin garin mu sun sha wulaƙanci, sai ga shi Allah ya cika mata burinta rabon Yaya SHAREEF ne."

"Wai wanne Yaya SHAREEF É—in?"
A cewar Yusaira tana gyara zama saboda su har yanzu basu san da auren SHAREEF a kanta ba

Dalilin da yasa sauran Æ´an matan da suke nasu hiran daban, hankulan su ya soma dawowa wurin su kenan

Ita kuma Bintu kamar an buÉ—e bakin ta tace, "au.. baku da labarin Maryamu tana da aure? Cab É—ijam, to wlh ta riga Ni aure, tun lokacin da aka kawo ta nan da auren ta a kanta, sai da Kawu ya haÉ—a su aure da Yaya SHAREEF sannan aka taho da ita."
Ai nan ta ci gaba da zayyane musu labarin komai tun daga Farko har ƙarshe

Mamaki da farin ciki ne ya cika su Aakifah; bakin su har ya ƙi rufuwa,
While sauran Æ´an matan suma mamakin ne a kan fuskokinsu wannan ya kalli wannan; wancan ta kalli wannan

Mubeena wacce take ɗaya daga cikin masu ƙaunar SHAREEF ɗin, sam maganar bai mata dad'i ba, don haka ta riga kowa yin magana tana cewa, "dalla ja can, wacce maganar banza da hofi kike faɗa mana a nan? bayan mun san cewa Yaya SHAREEF yana da Matarsa wacce take zaune a can ƙasar waje; shine za ki haɗa shi da wannan? Kin zauna kina mana tatsuniyar ƙarya mai zai yi da rainon ƙauye."
Ta nuna Maryamu sama da ƙasa ranta a ɓace, har da ƙara wa da faɗin, "ko Mata sun ƙare ai Yaya SHAREEF bazai kalle ta ba balle ma ya ɗauke ta a matsayin Mace."

Shewa suka saka sauran waɗanda suke baƙin ciki da jin zancen, har suna ƙara wa da faɗin, "faɗa musu dai Mubee, su je wata ƙaryan ba wannan ba, don ta zo tana cin arziki a inuwar su ba hakan yake nufin zata haɗa kanta da su ba, ai na gaba yayi gaba wlh."

Ran Maryamu yayi mugun ɓaci musamman maganganun Mubeenan, har ta buɗe baki da ninyar yin magana; sai Yusaira ta riga ta yin maganar

"Ai baku sani ba, abun ba daga nan take ba, kun san koda goma ta lallace ta fi biyar albarka, ku dubi Maryam sama da ƙasa takai Macen da Yaya SHAREEF zai iya kalla har ya ƙyasa wlh, ai bai fi ƙarfin yace yana sonta ba shima."

Miƙe wa Maryamu tayi a saman kan gadon, tana kallonsu rai a ɓace tace, "bari ku ji da kyau, shi wanda kuke ganin sa wani abu har kuke taƙamar ya fi karfin irina; a wurin ku shine Sarki, amma a wurina ko Bawa bai kai ba bare har ya samu muhimmancin da Maryamu zata zauna tana ɓata lokaci a kansa, ajina da sauran Mata ya sha bamban bare local irin ku masu tunanin shi wani ne a wurin ku, kuma duk ƴar iskan da tace zata gaya min magana a nan wurin; wlh summa tallahi bazan ɗauka ba, tsab zan ci wa kowacce shegiya Uwa a nan, ba a yi dani kuma baku isa ku zauna a gabana kuna maganata ba."

Yanda take maganar cikin isa da gadara a kuma fusace, tana girgiza jiki idanu a ware kamar zata cinye su,
Sai duk suka shiga taitayin su don har ga Allah ta É—an basu tsoro

Bare ita Bintu ta san halin Maryamu wurin faɗa, yanzu sai ta nemi a ba wa hammata iska don tsab zata iya cewa zata yi faɗa dasu, bata san cewa halin ta yana nan har yanzu ba, shiyasa da sauri ta miƙe tana janyo hannun Maryamun tana bata haƙuri ita da su Aakifah

Amma sam Maryamu ta ƙi zama sai girgiza take yi tana ƙara furta, "ku bar Ni don Allah, ai na ga rashin mutuncin nasu a kaina zai ƙare, wani tsiya ne a wurin SHAREEF ɗin da kuke tunanin kowa ma irin ku ne? To ke Bintu ki ƙara maimaita musu da kyau su san cewa akwai auren shi a kaina inga uban da ya isa yace ban kai ba, kuma zan juya shi yadda raina ke so, ko kuma in kun isa ku zo ku kwance auren Ni ce matar SHAREEF, akwai auren sa a kaina ko akwai abun yi?"

Itama Mubeenan tuni ta hayayyaƙo mata, musamman yadda Maryamun take mayar musu da martani tana zagin su, tace, "ki tsaya dai a Matsayin ki amma Yaya SHAREEF ya fi ƙarfin ki, a cikin mu babu mai tsoron ki balle ki tsaya kina zagin mu muyi shiru, ko mu da muke rayuwar Hutu da jin dadi; manyan Mata kuma ƴan uwansa na jini, mun fi ki aji da wayewa, kuɗi, nasaba, bai kalle mu ba bare ke wacce a ƙauye ta taso rayuwar ƴan wahala kuma kucakar yarinya."

Dirowa Maryamu tayi a kan gadon, tayi kukan Kura sai ga ta a gaban Mubeena, hannu tasa ta shaƙo mata wuya cikin bala'i da masifa; ranta a matuƙar ɓace tace, "don kutmar kan ubanki waye suke rayuwar ƴan wahalar? Bari in bambance miki rayuwar ƙauye da Birni."

Kafin ka ce me; faɗa ya kaure an kasa ɓanɓare hannun Maryamu a jikin Mubeena don ba ƙaramin shaƙa tayi mata ba,
Sai zage-zage take yi tana dukan duk wanda ya taho ƙwatan Mubeena a hannunta

Ai da gudu sauran suka je suka kirawo su Aunty Salma, nan da nan aka cika ɗakin daƙyar aka ƙwace Maryamu har lokacin zage-zage take yi a cewar ta, "a barta ta ci kan uwarta."

Aunty Salma da ranta ya ɓaci itama tace, "don ubanki ta fi ƙarfin ki ci kan uwarta, don Ni uwarta sai dai a mayar da ke ƙauyenku da ƙasusuwa a karye. Dama tun farko yarinyar nan ina da cikin ta wlh, to yanzu zan yi miki dukan tsiya in ga uban da ya tsaya miki, mu ba Sa'an yin ki bane."

"Haba don Allah aunty Salma, ke da za ki raba su mene ne kuma na zage-zagen nan? Kin san abun da ya haÉ—a su ne?"
In ji Aunty Zainab tana janye Maryamu da ke ta faman haki tana muzurai tamkar wacce iskokanta suka tashi

Su Momy ne suka shigo a lokacin don suma yanzu labarin yakai musu ana faÉ—an, a tare suka shigo da Aunty Najwa suka ji Aunty Salma tana maganganun tana zagin Maryamu

Aunty Najwa tace, "wai maimakon ki raba su shine kuma kika zauna kina zagin ta ita kadai? Wannan wanne irin abu ne?"

"Nima abun da nake faÉ—a mata kenan."

Rai a ɓace Aunty Salma tace, "eh dayake ba ƴaƴanku aka taɓa ba, ji be yanda ta shaƙe min ƴa tana son kashe min yarinya, to wlh bazan yarda ba idan ta kuma taɓa ta sai na ɗauki mataki a kanta nayi mata dukan tsiya a nan wurin."

Momy riƙo hannun Maryamu tayi ganin har yanzu tana cika tana batse wa tana zazzare ido, hankalin ta ya soma tashi kar kuma a ce ciwon ta ne zai tashi, shiyasa tayi saurin jan ta suka fita batare da ta furta komai ba, tabar su nan suna ta cece-kuce,
Kai tsaye sama ta haura da ita

While Bintu itama tuni ta zame jiki ta je ta sanar da su Umman su abun da ke faruwa,
But a cikin su babu wadda ta fito sun yi shiru suna jin hayaniyar ƙasa-ƙasa

Su Asabe Matar Yaya Faisal su ne suka fice suka je wurin fadan, amma koda suka je babu Maryamun sai su Aunty Zainab suke ta maganar, Aunty Salma na yi suna tanka ta suna gaya mata, "abun da tayi bai dace ba, ai kamata yayi ta tsaya ta ji ba'asin maganar."

Lokacin da Ammee ta zo wurin ne ma su Aakifah suke gaya mata dalilin faÉ—an,
Ai kuwa buÉ—an bakin ta tace, "to ai kuwa maganar gaskiya ce tunda Maryam da auren SHAREEF a kanta, kuma Insha Allahu gobe uwar haka za a kaita É—akin Mijinta, wannan taron da ku ka gani har da tariyan ta za a yi."

Ai kuwa jin magana ta fito da gaske ne, sai fa rikici ya ƙara ɓarke wa, su Aunty Salma da su Aunty Hidaya waɗanda suka haɗa ƴan uba da su Momy, maganar ta sosa musu rai, a cewar su, "tunda ba a ɗauke su a bakin komai ba, ai ba a faɗa musu ba sai yau ake nuna musu basu da matsayi."
Surutu dai kala-kala abun kamar zai zamar musu faÉ—a da su aunty Najwa
Chapter 43 · 0% Book details