Sashe 19
Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da DPO ya nuna musu wurin zama sannan ya fara magana da faɗin, "to wadannan Yaran su ne waɗanda Hanif yasa aka kamo su bisa zuwan su gidan Matar nan suna ƙoƙarin cin zarafin su, koma in ce sun ci zarafin su har suka yi ƙoƙarin fasa mishi Mota, ASP ɗin da suka tafi kwaso su shi yayi min bayani, sannan har mun buɗe file a kansu, amma kuma sai Mahaifinsa yanzu ya zo mana yana kawo ƙaran shi Hanif ɗin a kan saka wa a kama mishi Yaro, kuma maganar da yayi a nan cewan shi Hanif yana neman lalata ƴar ɗan uwansa, wanda hakan ne yasa Yaronsa Jabir ya nemi ya ɗauki mataki tunda Budurwansa ce wacce zai aura, dalilin da yasa aka kama su kenan, to Ni kuma ganin Hanif shi ya fara shigar da ƙaran, dana bincika sai na gane ɗanka ne shiyasa nace to a kira min shi don a yi wannan zaman a samu maslaha, that's why ban bar maganar wurin ASP ba.
Yanzu ina son in ji na bakin kowa tunda ga yarinyar ga mahaifiyarta."
Sai ya dubi Amra yace, "ta kanki zan fara, mene ne tsakanin ki da shi Hanif É—in?"
Mama ne tayi saurin yin magana da faɗin, "Yallaɓoi ita kurma ce, amma zan iya faɗan abun da ke tsakanin su."
"Ayya, ok to. go ahead, ke za ki iya magana ai. Babu damuwa."
Sai da Mama ta kalli inda Baba Jafaru yake, sai faman muzurai yake yi yana tsuke fuska, cikin baƙin ciki da tsanarsa take cewa, "Yallaɓoi abun da ya faɗa mutumin nan ba gaskiya bane, domin kuwa da shi da ɗansa basu da wata alaƙa damu illa na kasancewarsa ɗan uwa wurin Mijina, kuma tun sanda ya rasu komai ya ƙare na alaƙar mu, dalilin kuwa da suke bibiyar mu ɗansa ne yake son wulaƙanta min yarinya, domin ya sha neman ta yana son lalata ta Allah bai ba shi nasara ba, ba tun yau ba na sha zuwa wurin mahaifinsa ina faɗa masa ya ja kunnen ɗansa amma ya ƙiya sabida yana goyon bayansa a cewar sa babu abin da dansa zai aikata,
Shi kuma Jabir koyaushe sai ya zo gidan mu yana cin mana mutunci, babu cin kashi da zagin da bai yi mana ba, to yau a gaban Hanif aka yi komai tunda ya zo ɗaukar ta su je wurin aiki, shine ya shiga tsakani ya hana sa aikata ƙudirin sa a kanta, domin so yayi ya tafi da ita ta ƙarfi da yaji, shi kuma Jabir ya dinga zagin sa kuma yace sai ya ɗauki mataki a kansa, hankalina ya tashi tunda na san Yaron bai da mutunci ɗan shaye-shaye ne komai zai iya yi tunda ya furta muggan kalamai a kan Hanif, to lokacin da suka dawo da Abokansa ashe shi ya kira ƴan sanda, shine suka tafi dasu,
Amma shi yayi komai ne don martaban ƴata, don Allah DPO a taimaka a ƙwatan ma ƴata ƴancin ta a raba ta da wadannan azzaluman mutanen, domin suna shiga hakkinta, Jabir ya takura mata, ya shiga rayuwarta da yawa har dukan ta yake yi don kawai yana ganin bamu da ƙarfin da zamu iya ja dashi, sannan yana da ɗaurin gindin mahaifinsa, amma wlh babu zancen aure a tsakanin su kawai mugunta ne da cin zarafin da yake mata a kan dole sai ya aure ta, kuma ita ba ta son shi."
Ta ƙare maganar tana hawaye
While itama Amra tuni ta kwantar da kanta a jikin Maman tana nata hawayen; har da su shashsheƙa
Dukka babu wanda bai ji tausayin su ba, musamman ma Hanif da ransa babu abin da yake yi sai suya da tafarfasa, zuciyarsa na masa zafi kamar ya miƙe ya shaƙo Jabir ɗin
SHAREEF kuwa yana zaune ne yana sauraron abun da ke faruwa, baza ka taɓa gane yanayin sa ba tunda shi mutum ne da ba ya shiga abun da ba ruwan sa, mamaki ma yake yi har yaushe Hanif ya san yarinyar da yake zuwa ɗaukan ta since bai taɓa sani ba, to meye haɗin sa da irin ƙasƙantattun mutanen nan; kuma Kurma ma?
Idanunsa a kan Jabir ne sai bin su da kallo yake yi ba ya ko ƙyafta wa
DPO ne yace, "Malam Jafar kaji abun da Mahaifiyar yarinyar ta faɗa, amma kuma kai ka bamu bayanan da ya saɓa haka, ko kana da bakin maganar da zaka kare kanka?"
Shi kansa bai san cewan hakan zata faru na kiran da DPO yayi musu ba, duk da kunyar ƙaryan da yayi amma hakan bai sa ya sauya daga maganar nasa ba, tare da furta, "tun farko ɗan uwansa Abubakar ya ba ɗansa auren amra, dama tun kafin ya rasu sun ajiye Maganar haɗa auren zumunci, sauran yan uwansa ma sun san da zancen. Amma yanzu ita Shafa tana son ƙaryata shi ta ci mishi mutunci don an zo gaban hukuma, yaran nan fa nawa ne ina da damar da zan iya amsar su a yanzu ma ba sai anjima ba, don haka muddin bata amince da maganar nan ba to zasu dawo hannuna tunda mu ne dolen su."
Girgiza kai Dady yayi sabida mamakin furucin Baba Jafaru, ga shi kamar babban Mutum amma ashe irin dattijan nan ne da basu san abun da yakamata ba,
Don haka ya riga yin magana da fadin, "Gaskiya ka bamu kunya, ga ka babban Mutum amma son zuciya yasa kana ƙoƙarin tauye musu hakkin su, kuma ƴaƴan yan uwanka fa, ko wani ka ga zai ci musu zarafi ai sai inda ƙarfin ka ya ƙare, shin ana so dole ne? Sannan idan ka raba uwa da ƴaƴanta mene ne riban hakan a gare ka?"
DPO yace, "to wanne riba kuwa ban da son zuciya irin na mutanen mu na wannan zamanin? Ai Alhaji irin wannan cases ɗin da yawa ana kawo mana su a offices, mutane dai son zuciya yayi musu yawa, abun tausayi ma ga ta yarinyar babu bakin magana; wacce abar a tausaya mata ne, amma yabar ɗansa irin wannan mara sa jin yana ƙoƙarin ɓata mata tarbiyya, bai ɗauki mataki ba tunda nasa kawai ya sani, ƴaƴan ɗan uwansa ba nasa bane, idan da ace mahaifinsu na nan kun isa ku ci musu mutunci irin haka? To gaskiya Malam Jafar a wannan wurin ku ne da laifi, don babu inda aka ce a yi wa yarinya auren dole don kawai kuna son haɗin zumunci, meyasa bazai nemi yardan ta ba amma sai ya nuna mata ta ƙarfi, kuma kana gani amma baka dauki mataki ba? Wlh ka bamu mamaki, don haka baza mu lamunci wannan abun ba, tunda mu ne masu ƙwato wa Al'umma mara su galihu kamar su haƙƙin su; daga yau tunda maganar ta zo gabanmu zan muku iyaka da su, ku ne dai dolen su tunda babu yanda za a yi a raba ku dasu, amma kar ku soma ku sake yunkurin musu auren dole in har bada amincewar su ba, sannan kai kuma."
Ya nuna Jabir da yake tsaye jere da sauran Abokansa suna zazzare ido da cije baki, "duk rashin kunyar ka a nan zamu gyara maka zama ne, in har ka sake ka ƙara laifin da aka kawo ka nan, wlh summa tallahi a cell zaka ƙarike rayuwarka, daga yau babu kai babu yarinyar nan tunda ta nuna ba ta sonka, in har suka kawo mana ƙara a kan ka sake shiga sha'anin su; zaka ga yanda zamu yi da kai, mutanen banza mutanen hofi, gaba ɗaya kun ɓata rayuwarku da shaye-shayen banza, kuna aikata abin da ba shine ba babu tsoron Allah a zuciyarku, ko kuyi hankali ko mu mu koya muku hankali.
Don haka Ni yanzu zan sallami kowa bisa sharaɗin kai Malam Jafar da ɗanka baza ku ƙara cin mutuncin wadannan bayin Allan ba, ku ƙyale su suyi rayuwarsu cikin salama, Ni dai bazan yanke alaƙar ku ba tunda ku ne dangin su, amma suna da right na zama a duk inda suke so, to kwana nawa ne ma yarinyar zatayi aure ta bar ku?"
"Gaskiya ne wannan maganar naka DPO, and Ni ina ga tunda abun ya zama haka, yawanci irin wannan abun yana faruwa ne a kan rabon gado ko wani abu da mahaifi ya tafi ya bar shi, tunda abun haka ne zan ba marayun nan gidan da zasu koma kyauta, halak malak; wanda ba sai sun kori mahaifiyar ko sun ci zarafin ta ba, sai ta koma can ta zauna hakan za a fi samun sauƙi."
Baki DPO ya washe yana cewa, "Masha Allah Alhaji, gaskiya idan ka yi hakan ka kyauta kuwa, Allah ya ƙara buɗi da lafiya, tabbas ka taimaki marayun nan, thank you so much!"
Nan fa itama Mama ta soma kwararo masa addu'o'in cikin tsananin farin ciki,
Daga ita har Amran bakin su a washe da hakan zai nuna sun ji daÉ—in kyautar da aka yi musu
Don shi kansa Hanif ba ƙaramin murna yayi ba, wanda ya san dama ba sabon abu bane wajen Dadyn su, yayi ma wasu banza ma bare waɗanda ya gansu a cikin matsala
Dady kuwa yayi hakan ne sabida ya tausaya musu matuƙa, tunda ya san matsalar irin waɗannan dangin Uban; duk abun da zaka ga suna yi duk saboda gado ne, domin shi yake jawo hakan, kamar yanda Baba Jafaru ya faɗa ne ya san cewa zasu iya koron Uwar su gaje gidansu da komai nasu har Yaran, amma idan ya tallafa musu da gida hakan ba ƙaramin taimaka musu zai yi ba, gwara su koma can da zama zai fi, shiyasa yayi maganar cewan, "Hanif zai kawo musu takardar gidan gobe sai su tashi su koma can, kar su jingirta ko kaɗan."
Mama ta amsa mishi da to cikin farin ciki har yanzu tana zubar da hawaye; wanda ya koma na farin ciki
Daga nan yayi musu sallama ya tafi,
Shima SHAREEF miƙewan yayi ya bi bayan Dadyn su tunda bai ga amfanin zaman shi a wurin ba,
Aka bar Hanif kaÉ—ai a wurin