← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 75

Sashe 15

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗan gyara zamanta tayi cikin yanga cike da kwarkwasa tace, "ai ba sai wajen Aunty Haseena zaka zo ba, ko wurina ai yakamata ka riƙa zuwa muna gaisa wa tunda dai yanzu an zama ɗaya."

ÆŠan waro ido yayi waje, sai dai bai ce komai ba yayi murmushi yana É—auke kai a kanta

Ita kuma sai ta canza maganar da faÉ—in, "amma zuwa jibi ai Aunty Haseena zata dawo, zaka iya ganin mu a gidan ku at any time, but Ni dai zuwan domin ka zan yi tunda kai baza ka iya zuwa domina ba."

Dubanta yayi, sai dai yanayin yanda take mishi wani kallo tana murmusawa, sai ya ɗauke kai yana ɗan taɓe baki da cewan, "Haajara, ai ni ba abun da zai sake kawo Ni gidan ku sai dai in Brother, shine yake da damar zuwa ba Ni ba."

"Haba kai kuwa, kana Ƙaninsa kuma ka ce babu abin da zai kawo ka? Gaskiya ban ji daɗin maganar ka ba don gani nake yi kamar baka damu da mu ba, but Ni gani na zo duba ku sabida na san ku nawa ne. Gaskiya ba na son alaƙar mu ta tsaya a haka Yaya Hanif, zan so mu ƙulla Abota ko ba don Aunty Haseena ba."

"Ayya, Ni kuma ba na Abota da Mace, zan dai iya ɗaukar ki a matsayin Ƙanwata, hakan yayi miki?"

Murmushi tayi duk da bata ji dad'i ba, sai ta margaya kanta da faÉ—in, "eh yayi, na ji dad'i a hakan ma."

Shiru ya É—an ratsa saboda ya ci gaba da aikin sa bai sake mata magana ba,
Jin tayi shiru kamar ruwa ya ci ta sai ya É—ago yana kallon ta, da mamakin sa gani yayi ta zuba mishi ido kamar zata cinye sa,
Amma sai kawai ya basar yana cewa, "ba yanzu za ki tafi bane?"

Maƙe kafaɗa tayi tace, "No ba yanzu ba, ina son in ɗan ƙara lokaci a nan muna hira, hakan zai fi faranta min rai."

Shiru yayi mata duk da yana son fahimtar mai take nufi a yanda take masa kwarkwasan nan, ba tun yau ba tun a ranan auren su SHAREEF ya soma fahimtar take-taken ta wajen shige masa

"Yaya Hanif, idan baza ka damu ba zan so in samu numban ka sabida mu riƙa gaisa wa."

Kamar bazai bata ba, sai ya ga hakan kuma bai dace ba, shiyasa yace mata, "to mai zai hana? Bari in karanto miki."

Cikin jin dad'i ta soma latsa wayan nata tana rubuta numban nasa, ta ji dad'i yanda bai ce mata a'a ba, sai da ta gama tayi save before ta kalle shi tace, "please Yaya Hanif a ɗan kawo min wani abu na sha mana, sabida ƙishi nake ji."

"I'm sorry na manta ne wlh, ga fridge can za ki iya daukar duk abin da kike so, inyaso sai ki koma waÉ—ancan kujerun zai fi miki daÉ—in zama."

Haajara tace, "a'a nan ma ya isa, Ni da zan taya ka hira."

Murmushi kawai yayi mata yana ɗaukar wayansa tare da latso numban Amra, ya shiga ya rubuta saƙon yana neman ta yanzu

Ita kuma Haajara bata kai ga tashi ba wayanta ta soma ring, hakan ne yasa ta dakata tana É—aukar wayan.
***

_____Just like seconds sai ga ta ta buɗo ƙofan ta shigo; hannun ta ɗaya sanye a saman wuyanta tana gyara wa Hijabin ta zama,
Idanunta ƙyam a kansa, ganin kallon da Hanif yake mata yana faman doka mata murmushi, shiyasa itama ta sakar masa tattausan murmushin ta tana ƙarisa wa wurin da suke

Kallon da Hanif yake yi wa Amra ne ya jawo hankalin Haajara gare sa, dama ta gama wayan shiyasa ta katse tana bin sa da kallo tare da mayar da idanunta a kan Amran,
Ganin yanda suka zuba wa juna ido sai da wani abu ya É—arsu a zuciyarta, musamman yanda ta ga yana zuba mata murmushi da irin wannan kallon da sam hankali da tunanin ta ya gaza É—auka, take ta soma jin wani iri tare da jin haushin Amran kamar ta make ta,
Baki ta buÉ—e da ninyar yin magana, but sai Hanif ya riga ta yana yi wa Amran magana

Tambayarta yake yi, "ta gama aikin da ya bata?"

Tayi saurin É—aga masa kai fuskarta a washe

Sai ya ciro wasu files guda biyu yana mata alamun ta matso kusa dashi

Babu musu ta zagaya ta side din sa tana matso wa dab dashi,
Yayinda ta dubi files É—in da yake nuna mata don ganin bayanin da yake mata

Ita kuma hakan ya ƙara sanya Haajara cikin baƙin ciki, zuciyarta nan da nan ta soma hassala sabida kishin ganin su a haka gab da juna, idanu ta zuba musu sam ba ta jin abun da suke furta wa illa baƙin cikin da ya tokare mata wuya, ji take yi kamar ta je ta shaƙo wuyan Amra tayi jifa da ita sabida ganin yanda ta sake kusanci da Hanif ɗin sosai da yake mata bayani tana duban files ɗin gabansa, wanda hakan kamar zasu haɗe don har nimfashin junan su suke ji

Dalilin da yasa Hanif ya shiga wani yanayi kenan, tare da muskuta zaman shi yana mata kallon soyayya, face É—in sa É—auke da murmushi yake duban ta da faÉ—in, "kin gane ko? Za ki iya?"

Murmushi tayi masa, sai dai bata yi ƙoƙarin amsa masa tambayar nasa ba sai da ta ɗan ja da baya sabida ganin kamar fuskokinsu zai haɗe don kusancin su, wanda fuskantar ta da yayi ne yasa ta ji wani iri zuciyarta ta hautsine, lokaci guda ta kasa jure wa ta ɗan ja da baya tana gyaɗa masa kanta

Smile yayi shi kuma yana sake faÉ—in, "in dai baza ki iya ba sai in ba Secretaryna yayi min."

Hannu ta É—aga mishi tana masa bayanin zata iya

Ya fahimce ta shiyasa ya rufe files ɗin ya miƙa mata yace, "ok, ki je ki fara, idan kin gama sai ki kawo min zamu yi maganar da nace."

Kai ta gyaÉ—a masa tana juyawa zata bar wurin

Haajara da tsananin kishi ya cika ta har idanunta sun soma yin ja sabida jin ƙwalla na taruwan mata, ko ba a faɗa mata ba ta ga soyayya a idanun Hanif, tabbas akwai wani abu a tsakanin mutanen nan biyu, wanda a zahiri abun yake dole wanda ya gansu a haka ya fahimci akwai ƙauna mai ƙarfi a tsakaninsu,
Da idanu ta bi amra da ke ƙoƙarin fice wa a cikin office ɗin, bata san sanda ta daka mata tsawa da faɗin, "kee zo nan."

Da mamaki Hanif ya bi Haajaran yana kallo sabida jin abun da tace

Yayinda itama amran da sauri ta juya tana kallon Haajara wacce ta tsare ta da idanunta da suka soma sauya launi,
Ta nuna kanta da yatsa alamun ita take kira?

"Ke nake kira, ko kinga wata a nan ne?"
Tayi maganar a gadarance tana tsatstsare ta da ido

Hanif yace, "lafiya dai Haajara? Me zata yi miki kike mata wannan kiran?"

Dubansa tayi tana yatsina fuska, sai kuma ta tura baki cike da son burge sa, a shagwaɓe tace, "Kai Yaya Hanif, ruwa fa zata dauko min, na ga ai ƴar aikin ka ne that's why zan buƙaci ta dauko min ruwan a fridge."

Mamaki ne sosai ya bayyana a kan face É—in Hanif,
Ba shi kaÉ—ai ba har amra da tayi tsimi tana kallon Haajaran ta kasa motsa wa

Ita kuma Haajaran ko a jikinta; ta sake kallon Amra tana wulla mata harara da kallon ƙasƙanci tace, "ki dauko min drinks a fridge Malama."

"No, stop Amrah."
Yayi saurin furta wa sabida ganin zata nufi wurin fridge É—in,
Sai ya kalli Haajara fuskarsa a tsuke yace, "wannan ba ƴar aiki na bane, itama aiki take yi a Companin nan, za ki iya zuwa da kanki ki ɗauko abun da kike buƙata."

"To meye laifi don nace ita ta dauko min? Ni fa baƙuwa ce fa, kuma koda ba ƴar aiki bace a ƙarƙashin ka take aiki, zaka iya sanya ta ta ɗauko min da kanka."

Jin abun da tace ransa ya soma ɓaci duk da shi ba wai ya cika saurin fushi bane, amma ya kula don ƙasƙanci Haajara take son aikan Amra, musamman yanda take magana a gadarance ya soma fahimtar take-taken ta,
Don ya baƙanta mata yace, "wannan ta wuce yadda kike zato, aiki take yi a karkashina amma tana da matsayi sosai a wuri na, ba bukatar ki aike ta don nima ba ki ga ina aiken ta ba."
Sai ya dubi Amra da ke tsaye har yanzu, fuskarsa a É—an sake yace, "za ki iya tafiya Amrah."

Murmushi tayi masa; tare da juyawa ta fice a cikin office É—in tana jin daÉ—in abun da yayi domin ta

Wanda hakan ba ƙaramin fusata Haajara yayi ba, ranta ya sosu sai dai ta kasa ƙwaƙƙwaran motsi bare tayi magana,
Yanzu ta tabbatar da cewan bata da wani matsayi a wurin Hanif, kuma tabbas wannan doguwar yarinyar duk yanda aka yi Hanif sonta yake yi,
Kamar tayi kuka haka take ji, amma sai ta daure ta hana bayyanuwar hawayenta a waje, tare da ƙoƙarin kame kanta tana miƙe wa da faɗin, "to zan tafi, sai mun yi waya kenan?"

ÆŠago kai yayi ya dube ta, sai yayi kamar bai fahimci halin da take ciki ba, kuma bai saki fuskarsa ba yace, "ok."
Yana É—auke kansa ya mayar saman computern sa

Abun yayi mata ciwo, amma bata da yadda zata yi, dole ta juya ta fice jiki a sanyaye,
Tana fita suka haÉ—a ido da Amra da ke zaune wurin zamanta,
Amma tuni ta É—auke kai sabida kallon da Haajara ta sauke mata

Secretary ma tuni ya É—ago yana duban ta, bai ce mata komai ba shima ya É—auke kansa sabida aikin da ke gabansa
Chapter 15 · 0% Book details