Sashe 56
Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_____Har kusan ƙarfe shida na safe babu wanda ya farka a cikin su, domin wani irin barci suke yi mai cike da kwanciyar hankali, musamman ma SHAREEF wanda ya fi samun natsuwa barcin sa yake yi cikin farin ciki sakamakon abun da ya wakana a tsakanin su,
Shi ya fara farka wa a wannan lokacin, yayinda ya bi fuskar Maryamu da kallo, wacce take ƙudundune a jikinsa tana sharan barci sai numfarfashi take yi, duk da barcin nata yayi nisa amma koda gani akwai ɗan rashin natsuwa a tattare da ita,
Musamman da ya ji jikinta da ɗan zafi, sai ya daura hannunsa a saman goshin ta ya ƙura mata ido yana ƙare mata kallo, ba ƙaramin farin ciki ne a kan fuskarsa ba, wani irin nishaɗi ne yake tattare dashi sabida samun abun da yake so,
Duk da har a zuciyarsa bai so hakan ta kasance a lokacin da take cikin wannan halin ba, ya so ya tausaya mata amma ya gaza, ya gaza riƙe kansa balle ya haƙura, dole ne yasa ya aiwatar da hakan, amma shi kansa ya jinjina mata kuma ta ba shi tausayi matuƙa,
A hankali ya zare jikinsa ya sauka daga kan gadon,
Sai dai ya kasa tafiya sai da ya jima yana kallonta ganin yanda take ta numfarfashi tana jujjuya kwanciyar ta,
Sai da ya ga kuma kamar ta koma barcin ta dena motsi before ya fita a dakin ya koma nasa É—akin,
Wanka yayi ya nemi riga da wando masu taushi ya saka a jikinsa,
Sannan ya gabatar da sallan asuba da basu samu sun yi ba,
Dawowa dakin yayi, ya tarar da Maryamu har yanzu tana barcin bata farka ba,
Zuwa yayi bakin gadon ya tsira mata ido yana faman murmushi, sai yanzu hankalin sa ya kwanta ya samu abun da ya jima yana bukata, yau yarinyar da ya raina ta ba shi farin cikin da bai taɓa samun sa ba a tsawon rayuwarsa, yanzu ya kara gasgata cewan akwai bambanci tsakanin su da Haseena, domin a yanda ya samu Maryamu a cikakkiyar budurwan ta hakan ya fi komai faranta mishi, hakan na nufin shi ya soma sanin ta, nashi ce ita, shi kaɗai,
Zama yayi a gefen gadon while yana bin gashin ta da kallo ganin yanda ya cure wuri ɗaya a cinkushe, hannu ya sanya zai taɓa gashin, sai kuma ya ɗaura a kan goshinta, amma kuma zafin da ya ji sosai hakan ne yasa ya cire hannunsa da sauri, nan da nan murmushin kan fuskarsa ya gushe ya sake mayar da hannun yana sake taɓa wuyanta zuwa kanta, alamun zafin zazzaɓi ne don yanda ya ji jikin zauu hakan ya tsorata shi,
Bazai yiwu ya barta a haka bai kaita asibiti ba, ko don raunin da ke kanta da kuma ƙananun ciwukan da Magen ta karce ta, sai yanzu ne ma yake ganin yakushin da kyau daga saman wuyanta zuwa ƙirjinta, sosai ta karce wurin har ya ƙafe ya bushe da jini, don ma kwanciyar da suka yi duk sun kwashe,
Ƙoƙarin tayar da ita yake yi wurin hura mata iska daga bakin sa
A hankali ta soma motsa wa tana mimmiƙe ƙafafunta, kamar wucewar seconni ta soma motsa idanunta zata bude su, a hankali ta buɗe manyan idanuwanta da suka yi luhu-luhu suka canza launi, daƙyar ta iya buɗe su tana kallonsa, sai dai tuni tayi ƙoƙarin mayar da su sabida zafin da ya soma ratsa ta daga kanta, wani irin ciwon kai ne ke addabar ta ban da azaban da ke ratsa ta na saman goshin ta, hannu ta soma ƙoƙarin kaiwa wurin
Amma sai yayi saurin riƙe wa yana cewa, "sorry, kar ki taɓa, forgive me please, na kasa control na kaina ban tausaya miki a halin da kike ciki ba, but sorry zan yi ƙoƙarin taimaka miki yanzu sai mu je asibiti, i know kina jin ciwo sosai ko?"
Cikin lallami yake maganar a kuma sanyin muryan nan nasa
Wanda hakan ne yasa Maryamu ta ƙoƙarta ta buɗe idanuwanta ta zuba mishi, sai dai babu wani walwala a kan face ɗin ta, kallon sa kawai take yi tana ɗan runtse idanunta
Hakan ne yasa ya gane tana jin jiki, don haka ya dinga bata haƙuri kamar zai ari baki, shi da kansa yayi ƙoƙarin ɗago ta
Bata yi musu ba duk yanda yayi da ita haka take bin shi, sai dai ta mayar da idanunta ta rufe saboda ciwon kan da ke addabar ta, ko kusa ba ta son ta motsa kan, sosai ta soma jin yana ƙaruwa sabida moving da yake yi da ita, sai cije laɓɓa take yi tana sakin huci da ƙara
Nan da nan SHAREEF ya ruÉ—e ya rasa yanda zai yi, musamman yanda ya ga hawaye suna zuba a idanunta kuma ga shi ta kasa buÉ—e idanun, sai faman kiran kanta take yi ta manne masa tana kuka,
Sosai ya tausaya mata; kuma bai gushe wajen bata hakuri ba har suka shiga toilet, shi da kansa ya haÉ—a ruwan É—umi tunda an dawo da wutan tun asuba,
Sai ya kunna shower ya soma mata wankan, a lokacin ba ƙaramin kai zuciya nesa yayi ba; domin wani irin mugun sha'awarta ne ya sake taso mishi musamman yanda ya ga surar jikinta a waje, sai dai ya kasa taɓuka komai sabida a halin da take ciki tana kuka daƙyar ta tsaya yayi mata wankan,
Wankan tsarki yayi mata before ya saka sabulu sama-sama ya wanke ta, da sauri yake yin komai har ya gama ya fito da ita sai sannu yake mata,
Doguwar riga ya ɗauko mata na atamfa, sai da ya tsaya ya dubo hijab dogo har ƙasa fari ƙal, sannan ya saka mata ya sure ta zuwa waje,
Har sun kai wurin motan ya tuna bai dauko car key ba, dole ya koma da ita tana manne a jikinsa sai ƙanƙame shi take yi, jikinta har ya soma rawan sanyi sakamakon ruwan da ta shiga, hankalin sa ya ƙara tashi sosai haka ya dauki key ya zo ya saka ta a front seat, sannan ya zagaya ya shiga ciki ya ja zuwa bakin gate, fita yayi ya buɗe cikin sauri ya fitar da motan, sai ya dawo ya rufe ya ja ya tafi,
Hannunta ya kamo yana kallonta fuskarsa da tsananin damuwa, a hankali ya furta, "is ok Baby, don Allah ki yi hakuri yanzu zamu je asibiti a duba ki."
Shiru yayi kuma ya ci gaba da tuƙin, yayinda ya soma laluba aljihun sa don ya kira Doctor Abbas, but babu wayan ya barta a gida, haka nan ya haƙura ya ci gaba da tuƙin a cikin ƙanƙanin lokaci suka iso asibitin,
Shi kansa ya soma tsorata da yanda ya ga Maryamu take yi a yanzu, sai mimmiƙa take yi tana kuka sosai, jikinta yayi zafi zauu kamar garwashi,
ÆŠaukan ta yayi da gudu ya nufi cikin asibitin da ita, babu wasu mutane sosai tunda safe ne,
Amma duk inda ya gibta sai an kalle shi ganin sa rungume da ita yana tiƙan gudu,
Kai tsaye office din doctor Abbas ya nufa
Ya ci Sa'a yana nan tunda shi ne a kan duty, yana zaune yana duba wasu files sai jin bugun ƙofa yayi, ko kafin yayi motsi sai ganin SHAREEF yayi a ciki ya nufo inda yake,
Hakan yasa shima ya mike da sauri yana tambayar sa lafiya?
"Please Doctor, give her emergency help, I think it's a fever in her body, please do something."
"Is ok, É—aura ta a gadon mu gani." Doctorn yayi maganar yana nufan wurin gadon shima,
Bayan ya daura ta sai ya soma duba ta, daga bisani ya É—ago kai yana kallon SHAREEF da ke tsaye a wurin hankalin sa a mugun tashe, don gani yake yi har da laifin sa maybe kusantan ta da yayi ne a halin rashin lafiya,
"S. Ahmad ka kwantar da hankalin ka Please, ka samu wuri ka zauna, insha Allahu ba wata matsala alamun zazzaɓi ne mai zafi ya rufe ta, but yanzu zamu bata taimakon gaggawa."
"No Doctor, ka duba ta ina gani, hankalina zai fi kwanciya."
Murmushi doctor Abbas yayi, sai dai bai ce komai ba ya ci gaba da duba ta, amma ya tambayi SHAREEF É—in abun da yasa ta ji ciwo haka?
Bai ɓoye masa komai ba ya sanar masa, sannan ya kara da ba shi labarin neman ta da yayi yace, "ya nemo doctor Mace ta duba ta, maybe ya ji mata ciwo ne."
Smile doctor yayi sabida jin abun da yace, sosai yake ganin kishi a tattare da SHAREEF É—in ganin yanda ya kasa ya tsare a wurin, ya kasa ma bari a cire mata hijab sai dai É—aga wa aka yi,
Don haka a haka yayi mata treatment bayan ya gama duba ta ya gane matsalar ta
Ba wani abu bane illa zazzafan zazzaɓi da ya rufe ta, dama akwai wasu mutane haka suke idan ciwo ya kama su nan da nan yake rikitar da su ya fitar da su a hayyacin su, wasu ma har sambatu suke yi kamar sun zauce, jikinsu bai da jimirin ɗaukan ciwo nan da nan yake rikitar da su,
To itama haka jikin Maryamu yake, bare da tsoron da ya ƙara taimaka wa nan da nan zazzabin ya samu gurbin zama a jikinta, ga kuma ciwukan da ta samu, at the short time suka fitar da ita a hayyacinta
Sai da ya gama yayi masa bayanin komai, sannan ya kira wata Likita Abokiyar aikinsa, ya faÉ—a mata matsalar da kuma binciken da zata yi a kanta,
Dole aka É—auki Maryamu a keke zuwa wani É—akin,
A can Likitan ta duba ta, so babu wata matsala ba wani ciwon da ya ji mata, amma duk da haka ta É—an taimaka mata,
Kuma ta yi wa SHAREEF bayanin, "kawai ruwan É—umi za a taimaka mata tana shiga shikenan, amma ba wata matsala."
Sai kuma wasu magunguna da ta rubuta wadda zata sha
Shima Doctor Abbas ya rubuta mata na zazzaɓin, sannan ya ɗan basa wasu shawarwarin
Har hankalin SHAREEF ya kwanta musamman da ya samu Maryamun jikin da ɗan sauƙi tana barci, dole ya jira don ta tashi, but bai sanar da kowa ba haka ya zauna shi kaɗai a asibitin yana jiran farkawar ta.