Sashe 26
Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk da haka sai da Umma tace, "bazai yiwu ta tafi ba sabida mutuwa ce aka yi, kuma ai bata yi yawan hutun ta ba, dukka-dukka kwanaki takwas da zuwan ta, ta bari ko arba'in in an yi sai ta wuce. "
Haseena tace, "No Umma bazai yiwu in ƙara kwanaki a nan ba gaskiya, sabida zan iya samun matsala gwara kawai in wuce."
Umma zata sake magana; amma Abba ya hana ta, yace, "kawai ta barta tunda harkan karatu ne, tafiyarta bazai sa Haajara ta dawo ba, gwara ta tafi kar ta samu matsala kamar yadda ta faÉ—a."
Daga nan suka yi mata fatan alkhairi har bakin mota suka raka ta, driver ya wuce da ita zuwa airport
After Haseena tayi landing a Sydney,
Sai daga baya ta sanar da SHAREEF domin bai san da tafiyarta ba, sai da ya kira ta sannan take sanar mishi, "ita yanzu haka ta wuce."
Tsaban takaici da mamaki ma ya rasa mai zai ce mata, yanzu ya soma fahimtar Haseena ta rage sonshi, ko ya yarda ko kar ya yarda tabbas Haseena ta canza mishi, matsayin da ta ba shi a baya; yanzu ba haka ba, tunda har zata tafi bata sanar mishi ba sai yanzu da ta isa can, ya ma rasa mai zai ce mata tunda bai da bakin magana, amma yayi mamaki gaskiya tunda mutuwar ƙanwarta aka yi; bai yi tunanin zata tafi nan kusa ba, kuma a yanzu din ma bai tambayi ba'asi ba haka ya kashe wayan yana takaicin ta, ga shi babu halin ya nuna mata ɓacin ransa sabida yanda yake jin tsananin soyayyarta a zuciya, a yanzu ji yake yi tamkar ya rabu da ita, yana son Allah ya cire masa wannan soyayyar da bata da amfani a wurin sa, da zai sami hakan tabbas da yayi farin ciki a ransa
A ranan haka ya wuni sukuku ko abinci ya kasa saka wa a cikinsa, damuwa ce fal cikinsa ya rasa inda zai tsoma kansa ya ji daɗi, meyasa komai ya canza; yanda yake zato ba haka ba? Why Haseena zata sauya mishi maimakon ta ba shi farin ciki take wahalar dashi? A kullum soyayyarta ƙara ninkuwa yake yi a ransa, koda da ƙwaran zarra na wucewar daƙiƙu ba ya wucewa batare da tunanin ta ba
Dalilin da yasa lokaci ƙanƙani rayuwarsa ta sake canza wa, domin a yanzu ba shi da wadataccen farin ciki tunda Haseena ba ta ba shi kulawa yanda yake buƙata, abun da yake so a wurin ta ta hana sa, wayan ma da yake samu suna yi sai idan ita ta ga damar a yi sannan za a yi,
Idan ya ɗauki ƙafa ya je can bazai samu farin ciki ba, sai dai kawai yana zuwa ne domin ya samu salama daga cikin zuciyarsa, tunda ganin ta ma wani samun natsuwa ne a tattare da shi, walwalan sa yanzu ta ragu fiye da baya, duk da daman shi ba mutum bane mai sakin fuska, amma yanzu damuwa ta ƙara mishi yawa,
Idan ya zauna bai da aiki sai tunani a ransa, ko É—an wayan da zaka gansa ya zauna yana latsawa ba ya yi yanzu, tunda wacce suke charting É—in yanzu ta janye mishi,
Lokaci guda ya zabge duk ya wani sukurkuce tamkar ba É—an gayen nan ba mai ban sha'awa da kyan kallo, yanzu babu wannnan gayun tunda babu natsuwar yin sa, kallo É—aya ma idan ka yi masa zaka san cewa ya sauya duk ya fita a hayyacinsa, ya rame ga ciwo da koyaushe fama yake yi da kansa
Hanif ne mai rarrashinsa tunda shi ne ya fi sanin halin da yake ciki,
Yakan ba shi shawarwari da dama musamman a kan Maryamu, amma sam ba ya kula sa bare ya nuna alamun yana jin sa,
A koyaushe yana nuna masa kan cewa, "shi ya É—aura ma kansa wannan laluran tunda yana da damar da zai iya magance matsalar sa, Haseena a yanzu bata da lokacin sa sabida ko yanayin da take nuna masa dole zai fuskanci hakan, yakamata ya san me yake yi kafin ya halakar da kansa."
Cike da sanyin murya SHAREEF yace, "na sani Bro, na san Haseena ta sauya daga ra'ayina yanzu, amma abun takaicin yanda zuciyata ta makance da tsananin ƙaunarta, a duk sakon ɗaya ina jin soyayyarta tana ƙara ninkuwa fiye da koyaushe, da zan samu na fitar da sonta a zuciya tabbas zan so hakan, Hanif ina cikin tashin hankali, ita kaɗai nake so, ba na jin zan iya kallon wata Mace a fuskata ta bani sha'awa bayan ita, bazan iya kallon wata bayan ita ba, amma ina mata uzuri na san komai zai wuce da zaran ta kammala karatunta ta tare a gidana, haka nan zan jure tunda bazan iya aikata zina ba."
Cike da tsananin tausayinsa Hanif ya dafa sa yana kallonsa, yayinda yake furta, "ina ji a jikina Haseena baza ta sauya ba, sabida a yanzu rayuwarta ta sauya ba kamar baya ba, kuma na tabbata a can inda take ta koyo wasu dabi'u wanda duk mai hankali zai iya fahimtar hakan, wlh sam yarinyar bata dace da kai ba Bro, ni na tabbata alhakin yarinyar nan zai iya kama ka, kamar yanda kake jin zafi da ƙunci a ranka, haka itama Maryam tayi fama da dakon soyayyarka tana azabtuwa, amma sam ka ƙi tausaya mata, meye laifin yarinyar; meye aibun ta? Don kawai Allah ya yi ta a cikin ƙauye ba irin rayuwar wayewan da kake so ba? Ka sani yanda ka wahalar da ita; kaima haka zaka ɗanɗani irin wannan azabar, ko ba don ka so ta ba; ka sassauta mata daga irin tsanar da kake mata, watakil Allah zai sassauta maka kaima a naka soyayyar, imagine! Ka taɓa tunanin Haseena zata juya maka baya bare har ta baka wannan wahalar?"
Sai ya girgiza kansa tare da ci gaba da faɗin, "shawaran da zan baka kawai yanzu ka dage da addu'a domin samun sauƙin wannan makauniyar soyayyar naka da baza ta kaika ko'ina ba, already yanzu Haseena idanunta sun buɗe fiye da na da, illan wayayyun Matan kenan; don su basu da alƙibla a koyaushe zasu iya juya maka baya su nuna sun fi ƙarfin ka, ɗan samun lokacin ta da kake yi ma yanzu zaka iya rasawa a nan gaba, sabida ta canza daga wacce ka santa."
Shiru yayi bayan yakai zancen sa nan
Yayinda ɗakin ya ɗauki shiru babu wanda ya sake yin magana tsawon lokaci, sai ma SHAREEF ɗin da ya miƙe ya nufi cikin bedroom ɗin su daga shi sai short wando, yana tafiya tamkar zai faɗi ƙasa tsaban yanda yake jin yanayin sa babu daɗi
While Hanif ya bi sa da kallo har ya shige, sannan ya girgiza kansa yana mamakin halin ɗan uwan nasa, ya san bazai taɓa ɗaukar maganarsa ba kasancewar sa mai tsaurin ra'ayi,
Murmushi kawai yayi ya tashi ya fita a cikin Falon
Yayinda SHAREEF kuma yana shiga; toilet ya wuce kansa tsaye, domin rabon sa da yayi wanka tun jiya, ko fita yau bai yi ba sabida ciwon kan da ya dame sa, a nan ɗaki ya wuni sai dai Sadiq ne ya kawo masa abincin sa har nan, kuma ko taɓa wa bai yi ba sai yanzu da Hanif ya dawo, shi ya tilasta masa har ya ɗan ci kaɗan suka zauna suna tattaunawa a kan matsalar nasa,
Wankan yayi ya fito ya zura riga da wando masu sauƙin nauyi na shan iska, ko lotion bai tsaya ya shafa ba don yanzu bai ɓata lokacin sa a kan ƙalƙale kansa; sabida halin damuwa da yake ciki, duk ya bar gashi a face ɗin sa yayi buzu-buzu ya sauya mishi kamanni, tamkar ba shi ba, madaidaitan idanun nan sun sake shige wa sun yi ciki sun faɗa, duk wanda ya kalle sa sai ya ga ramar da ke face ɗin sa,
Room slippers ya zura a kyawawan fararen ƙafafunsa before ya fita zuwa downstairs
Su Hanif suna zaune a falon suna taɓa hira, ban da Dady ba ya cikin gidan a lokacin
Zuwa yayi ya zauna a gefen Hanif yana É—an kwantar da kansa a jikin kujerar
Yayinda Momy ta bi sa da kallo tana faɗin, "ka ji sauƙin kan yanzu?"
Kai ya gyaÉ—a mata bayan da ya É—ago yana kallonta
Sai tayi shiru tana kallonsa before ta kiran sunan sa da faɗin, "har yanzu SHAREEF baza ka yi wa kanka faɗa ka san abun da ya dace da kai ba ko? Meyasa ba ka jin magana ne? Ka fi son ciwo ya kashe ka a banza wato? Kana ganin ba na shiga lamuranka a tunanin ka abun ba ya damuna ne? Kana fama da ciwo tsawon lokaci, mun yi maka gata amma ka kasa bin ra'ayin mu, ita wacce kake so bata yi maka maganin komai ba, Don Allah ji be yanda ka rame ka fita a hayyacinka sabida taurin kai irin naka, ka saka mu cikin damuwa kai kanka baka da natsuwa ko kaɗan, idan har zaɓin mu bai yi maka ba mun yi kuskure, zai kyautu a ce ka nemo wata Macen ka aura tunda Allah ya halarta muku zama da Mace fiye da ɗaya, ba wai ka zauna kana cutar da kanka kullum kana ɗaga mana hankali ba, wlh ka ji na rantse maka idan har baka samu mafita tsakanin ita wacce kake so da Maryam ba; idan har babu wacce zata zauna da kai to dole ka ƙara aure, don bazai yiwu muna ji muna gani ka faɗa halaka ba, daga ƙarshe ka zo kana aikata zina; na faɗa maka ka ɗauki mataki tun kafin mu mu ɗauka."