← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 75

Sashe 53

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ban manta ba Haseena, ke ce Haseena wacce ta kasa faranta min a lokacin da nake buƙatarki, You chose my sadness over my happiness ko? To ai ban ga amfanin ci gaba da zama da ke a haka ba, karatu ne dai ki je ki ci gaba da yi, bazan hana ki ba, but ba da igiyar aure na ba, babu amfanin ci gaba da rayuwa da wacce a yanzu ba ta so na, I know Haseena you have changed me, I will give you this chance, because now I myself stop feeling your love in my heart, ina ga gwara mu rabu kowa ya je yayi rayuwarsa yacce yake so, abun da ba ki sani ba, a baya na ɓoye miki cewan ina da aure, before na aure ki iyayena sun yi min Aure, amma na watsa musu ƙasa a ido; na zaɓe ki fiye da farin cikin su, na kasa musu biyayya duk a sabida ina sonki, sai dai a yanzu babu amfanin ci gaba da nuna miki wannan soyayyar, zan zaɓi in zauna da zaɓin su sabida a yanzu itama zaɓina ne, a yanzu haka ta tare a ɗakin da kika ƙi ki tare. I have no more worries now Haseena, na sake ki..."
Daga haka ya gimtse wayan batare da ya jira jin mai zata ce mishi ba, don a yanzu mugun haushin ta da yake ji ko kusa bazai iya bata damar da zata ci gaba da masa magana ba, kuma ba ya sonta cikin rayuwarsa, gwara ya rabu da ita kawai ya huta tunda haka ta zaɓa, tabbas soyayyarta bata masa rana ba, Haseena ta cuce shi ta ci amanarsa, wanda bai taɓa tunanin hakan ba, sabida irin yardan da ya bata, duk wanda ya ci amanarsa ba ya iya yafe masa cikin sauƙi, a yanzu bata da sauran amfani a rayuwarsa,
Motansa ya ja da gudu yabar haraban asibitin, yayinda yana jin kiran wayan nata, hakan ya ƙara fusata shi, nan take ya tsayar da motan ya kashe wayan gaba ɗaya sannan ya ci gaba da tuƙin sa.

Juma'at Mubarakh fans.
[29/04, 7:44 AM] نفيسة OumƊahira: 🌱🌱🌱🌱🌱

       *SHAREEF*
           _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱

_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*Littafina na kuÉ—i ne, ki biya ki karanta, zaku iya samu na a kan wannan numban wayan. 07065334256.*

__________
*BOOK2*
_______________*PAGE27*
_____Dayake Hanif ya kira Maryamu ya sanar mata da zuwan nasu,
Lokacin ta farka kenan tana kwance tana duba wayanta sai ga kiran sa, ta ji daɗin jin cewan zasu zo, shiyasa da sauri ta miƙe ta soma aikace-aikace,
Gyara É—akin ta ta soma yi sannan ta gyara falo, ko kusa bata bi hanyar É—akin SHAREEF ba, bata damu da yana nan ko ba ya nan ba, aikinta kawai take yi,
Daga ita sai rigan barcin ta doguwar riga mai santsi kalan ruwan ƙasa, kanta kuma ta kwafa hula mai tambarin UB a gaban, red colour yana da tuntu,
Tsab ta gyara gidan ta saka turaren ƙamshi, sannan ta kwashe komai na saman dainng ta nufi dashi kitchen, sai da ta buɗe abincin ta ga alamun SHAREEF ya ci,
Bakinta ta taɓe ta zubar da sauran ta soma wanke-wanke, bayan ta gama sannan ta ɗaura girki,
Cikin sauri take yin komai kar su zo bata gama ba,
Jallop ɗin taliya ta ɗaura, shiyasa cikin sauƙi ya soma dafuwa, sai tayi using da sauran naman da aka ajiye mata, dama raguwa ne tun na washe garin ranan da aka kawo ta, Sadiq ya siyo ma su Ammee da suka zo gidan suka zauna, tare da kayan ciki, jiya ta ƙarisa amfani da hantan da ya rage, yau kuma ta zuba sauran raguwar Kazan, babu wasu kayan cefane a gidan duk da an tsibira kayan abinci kala-kala, shima kayan tea ɗin da suke amfani dashi duk su Ammee suka sanya Sadiq ya kawo su, dayake ba yawa a yanzu ma ya gama ƙare wa

Tana ganin ya soma sulale wa ta wuce É—aki ta shiga wanka,
Bayan ta fito ta nufi kitchen ɗin daga ita sai towel ta ƙarisa sauran aikin, sai da ta zuba a cooler sannan ta koma ɗaki tana ƙoƙarin shirya wa,
Riga da skirt na material lace ta ɗauka ta sanya, mai ruwan ƙwai da ratsin dige-ɗigen milk, tana cikin shafa lotion ta ji shigowar motan su, bata tabbatar da su bane shiyasa ta ɗauki ɗankwalinta ta ɗaura, ko powder bata saka ba ta fice a haka after ta zura flat shoes,
Tana fita kuwa sai ta ji nocking, hakan ne ya tabbatar mata da su ne, tunda in SHAREEF ne ya san ƙofan a buɗe take bazai tsaya nocking ba,
Wurin ta nufa ta buÉ—e musu tana washe baki

Hanif da Amra ne tsaye dukkan su sun sanya kaya iri É—aya shadda kalan purple, light purple,
Yayinda Amra tayi using da dogon hijab har ƙasa shima purple ɗin dack, ta sanya flat shoes da Jakar hannunta kuma farare,
Ba ƙaramin kyau tayi ba, dukkan su sai shining suke yi ƙyallin aure ya bayyana a fuskokin su,
Bata yi kwalliya ba amma ta saka jan Jambaki da yayi mata kyau sosai

Hanif yace, "Ƙanwata kin ganmu sai yanzu."

Dariya tayi tace, "ku shigo mana."
Ta matsa musu a hanya suka shiga

Tare suka nufi cikin falon,
While Hanif da Amra suka zauna a kan two sitter,
Ba ƙaramin kyau suka yi ba domin sun dace da juna

Maryamu kuma sai da ta nufi fridge ta É—auko musu ruwa da lemo, sannan ta zo ta zauna

Hanif yace, "Bro bai dawo bane har yanzu?"

Dayake bata san ya fita ba, sai kawai tace, "eh bai dawo ba."

"Ok, mun yi waya dashi ai, ya ce min ya fita,
To ga Amaryata na kawo miki, fatan za a kula min da ita don Ni ba zama zan yi ba?"

"Kai Yaya Hanif, tun yanzu zaka tafi? Ka bari mana ga abinci sai in É—ibo maka ka ci, kuma ai Yaya SHAREEF É—in ba ya nan tunda ka ce kun yi waya ka bari ya dawo."

"Aa dawowarsa ba yanzu ba, nima zan je in ga Likita ne a kan matsalar My Amrah, goben nan zata soma ganin Likita insha Allahu, muna bukatar addu'ar ki Allah yasa a dace."

Duban Amran tayi, tana murmusawa tace, "insha Allahu Yaya zan taya ku da addu'a, amma wlh tana da kyau Yaya, ka iya zaɓe, ta fi ka kyau fa, har dogon hanci ta fi ka."

A yadda tayi maganar ba ƙaramin dariya ta basu ba,
Daga shi har Amran suka dara

Itama tana dariyan tace, "wlh da gaske nake yi Yaya."

Ya dube ta yace, "wai haka My Amrah?"

Dariya tayi tana rufe fuskarta cike da kunya

"Kinga kin sa ta jin kunya, amma duk da haka fa kin faÉ—i gaskiya."

Murmushi Maryamun tayi, tana tsiyaya musu ruwan a cup ta basu, tare da cewan, "wlh ba wasa ba Yaya ta burge Ni sosai, ina sonta da ƙawa. Duk da dai kamar ta girme Ni, amma zan riƙa kiranta da Aunty."

Dariya Hanif yayi yace, "ban da abun ki, ai ko ta girme ki ke ce Matar Yaya, ita ce zata ce miki Aunty, ki ɗauke ta kawai tamkar ƙawar taki, don zan so ku haɗa kanku sosai, ita kanta tana da sister wacce na san zaku zo kai ɗaya da ita, sunanta Afra, jiya ta zo gidanmu ta wunin mana, kinga da yau ne ta zo da mun zo tare kin ganta."

"A'a, Ni dai na fi son Aunty Amra, ita ce ƙawata. Ko Aunty amra? Za ki amshe Ni a matsayin friend ko?"

Kanta ta gyaɗa mata da sauri tana murmusawa, domin hakan yayi mata dad'i, musamman yadda ta ga Maryamu ta saki jikinta da ita, bata nuna mata ƙyama ba, sabida Hanif ya bata labarin ta yace, "ita yar uwansu ce, auren zumunci aka yi da SHAREEF."
So a ganin ta baza ta amshe ta hannu bibbiyu ba, ko a yanayin da ta ganta akwai iyayi; sai kuma ta ga Maryamun ba haka ba, ta saki jikinta sosai da ita

Hanif bai jima ba yace, "zai wuce."
Ruwa kawai ya sha yayi musu sallama ya tafi, sai da ya sumbaci Amran sannan ya fice

Yana fita Maryamu tace, "gaskiya Yaya Hanif yana sonki, kun yi matuƙar burge Ni, wlh in faɗa miki gaskiya, Yaya Hanif yana da kirki sosai, ke kam kin dace, nayi farin cikin wannan auren naku ba kaɗan ba, Allah ya ba ki lafiya kema ki riƙa magana kamar kowa."

Murmushi Amra tayi cike da jin daÉ—in zantukan Maryamun, sai dai bata da bakin magana illa kallonta da take yi fuskarta a washe ta kasa dena murmushin

Yayinda Maryamu kuma dayake akwai shegen surutu ne, musamman da Amran take burge ta, sai tahau mata tambayoyi a kan yanda suka haÉ—u da Hanif din,
Ganin tayi shiru ta ƙi bata amsa sai dariya take,
Hakan yasa ta tuna bata magana, sai tace, "ki yi hakuri fa na manta da ba kya iya magana, kuma ga shi ban iya irin Yaren ku ba, ya zamu yi kenan? Don wlh ina son muyi hira sosai."

Amra dai bata ce mata komai ba illa sauraron ta da take yi,
Ita kuma ta samu bakin zuba sai rattafa zancen ita kaÉ—ai take yi, shiyasa idan tayi abun dariya sai dai Amra ta dara kawai cike da nishaÉ—i

A tare ma suka ci abincin, kamar sun jima da sanin juna, don sosai Maryamu ta ja ta a jiki kamar tun farko ta jima da sanin ta, yanda ta saki jiki da ita ita kanta tana mamakin hakan, bata san cewa Maryamu bata da nuna rashin sabo ba, musamman in ka shiga ranta,
Dole Amra ta biye mata wurin biye mata tana mayar mata da martanin maganar nata ta hanyar waya,
Ita kuma sai Maryamu ta amsa ta karanta,
Hakan ne yasa hiran nasu tayi daÉ—i sosai suna ta bada labarin junan su,
Ta hakan ne har Maryamu ta san labarin haÉ—uwar su a wurin aiki
Chapter 53 · 0% Book details