Sashe 44
Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Momy a lokacin ta baro Maryamu a ɗakinta ta zo tana basu haƙuri, amma inaa; maganar dai ta ƙi mutuwa, duk yanda ta so ta basu hujjar da zata kare kansu amma sun ƙi fahimta sai yaɓa maganganu suke yi,
Shiyasa ta tafi tabar su nan, tabar su da su Aunty Zainab su faÉ—a; su faÉ—a, tunda ba baki suka fi su ba
Magana dai sai da Dady ya zo ya tsawatar musu sannan ya faɗa musu dalilin ƙin bayyana musu maganar, yace, "shi da kansa yace kar a faɗa tunda ba tarewa zata yi ba, amma yanzu tunda dalilin tarewan ya zo dole zasu bayyana musu, don haka biki dai dana SHAREEF za a yi."
Daga baya dai haka suka koma suna ƙus-ƙus babu kalan zage-zagen da basu yi ba,
Abun da biyu ne dama tunda sun so su Hanif su auri ƴaƴansu, amma babu wanda ya neme su, sai wacce suke ganin ba kowa ba ita ce aka haɗa auren ta da SHAREEF, ai ga Mubeena ga sauran ƴan Matan da suke da burin haɗa auren zumunci, duk Momy ta ƙi basu fuska,
Abun yayi musu ciwo sai dai haka nan suka liƙe maganar a ransu suka bar abun na ciki na ciki
Yayinda Maryamu tana can É—akin Momy, ta zaunar da ita tace, "kar ta fara ta fito."
A tunanin ta ma ciwon ta ne ya tashi ko aljanun ta sun hayo, amma ganin yanda Maryamun ta ci gaba da harkokin gabanta da hankalin ta a jikinta, shiyasa hankalin Momy ya kwanta ta sake fita tabar ta a É—akin,
Sai da Dady ya dawo sannan ta jawo hannunta suka je É—akin sa tunda yace ta kira ta
Sai a lokacin Maryamu tasan mai ke faruwa tunda Dady yayi mata bayanin komai a yanzu, hankalin ta ya tashi tunda a yanzu gaskiya ba ta son SHAREEF sabida halayyarsa da yake gwada mata mugunta babu tausayi a ransa, a ganinta yanzu shi ba Mijin aure bane, ya fice mata a rai,
Don haka ta buɗe baki tace, "Dady wlh ba ya sona, nima yanzu na haƙura dashi wlh, gwara a raba auren kawai."
"A raba auren kuma Daughter?" Dady ya tambaya cike da mamakin furucin ta
Yayinda Momy da ke tsaye tana sauraron su, sai ta koma ta zauna tana cewa, "zancen a raba ai bata taso ba Maryam, ko kin manta halin da kika shiga ne a kan soyayyarsa? Yanzu kuma shi da kanshi yace zai zauna da ke sannan kuma ki ce a raba? Bayan kina ganin yanda mutane suka soma gutsiri-tsoma a kan maganar har hakan ya ja ku da faɗa, ai wannan hanyar ne kaɗai za ki bi domin tusa musu haushi, zuwan iyayenki ma sun zo ne har da tariyan ki, suna farin ciki kuma ki watsa musu ƙasa a ido?"
"Momy..."
"A'a ya isa, na san abun da za ki ce, a kan dai maganar ba ya sonki ne, to yanzu ke kike da damar da za ki ƙwace SHAREEF tunda har ya nuna zai zauna da ke, ita wancan da kike tunani a kanta tana can inda ta fi wayau ta ƙi amincewa ta zauna da shi, don haka wannan damar ki ce Maryam, ba na son wata zance da zai fito a bakin ki; ki shirya gobe ke ma za a kaiki dakin ki, maganar makarantar ki kuma; mun rigada mun yanke hukuncin daga baya za ki zana jarabawar Weac da Neco sai ki fara babban makaranta, kin san dai da muna so mu raba auren nan da tuni mun raba shi, sabida halin da kika shiga a baya da kuma abubuwan da SHAREEF yayi miki, to ki yi hakuri kawai baza a raba auren nan ba, dama burinmu kenan ki samu wani matsayi a wurin sa, kuma yanzu kin samu tunda ya amince da ke."
Kallon Momyn kawai Maryamu take yi idanunta sun cika da hawaye, gani take yi kamar har da son kai a maganar Momyn, tunda ita yanzu ta nuna ba ta so why not baza a raba auren ba, mutumin da ya nuna ba ya sonta don yanzu yace zai zauna da ita; hakan kuma sai su goyi bayan shi,
Kallon Momyn kawai take yi tana sauraron ta zuciyarta na mata zafi
Dady yace, "haƙuri za ki yi Maryam babu zancen raba auren nan, mun san kina sonshi kuma babu yanda za a yi ki dena sonshi tunda tun farko kin furta, na san ɓacin rai ne da kuma abubuwan da yayi miki a baya, amma mu muna alfahari da wannan auren daughter, za ki ji daɗin sa Insha Allahu Allah zai sanya muku albarka a auren nan, don haka ki yi biyayya kinji ko kamar yanda tun farko kika yi mana, SHAREEF bazai taɓa cutar da ke ba a wannan karon, idan ma ya cutar da ke ga ki gani ki zo ki sanar min zan ɗauki mataki."
Ya ƙare maganar cikin lallaɓa ta ganin hawaye sun cika idanunta
Maryamu ta kasa yin wata magana sabida sun ɗaure ta da jijiyoyin wuyanta, bata da yanda zata yi, idan ma ta bijire ga Iyayenta a gidan su zasu ji kunya, har ga Allah yanzu babu SHAREEF a ranta, amma ta san yanda zata dauki mataki a kansa, wlh wlh in har ta amsa sunan ta Maryamu sai ta ɗauki fansar wulaƙancin da SHAREEF yayi mata, don haka ta komar da hawayenta ta hana su fito wa, ta nuna musu ta amince da abun da suka ce
Sun ji dad'in amsar ta, daga nan Dady ya sallame ta yace, "ta tafi zasu yi magana da Momyn nata."
Tashi Maryamu tayi ta fita zuciyarta har lokacin tafarfasa take yi, ranta a ɓace yake, a fusace ta bi ta benen baya zata sauka,
amma sai ta jiyo sautikan dararrakun su Halliru da Bashir, har da Sadiq don shima ya dawo bikin ne a yau,
Suna zaune a kan benen suna ta hira har da wasu daga cikin Abokan Sadiq É—in,
Koma wa tayi da baya ta zo wuce wa ta bakin ƙofan su SHAREEF da ta wuce, yanzun ma har ta gibta sai kuma ta ga baza ta iya barin baƙin cikin da ke ranta ba, sai ta je ta gaya masa magana ko zata samu zuciyarta ta samu sauƙi,
Tura ƙofan tayi da ƙarfi ta shige tana bin ko'ina da kallo; kasancewar akwai duhu babu hasken glop, hannu ta saka ta laluba ta kunna glop ɗin sannan ta soma duban Falon, ganin babu kowa sai ta nufi kanta tsaye cikin bedroom ɗin; nan kuma ta kwankwasa tana son ta ji ko akwai motsin mutum
Daga ciki SHAREEF ne kwance a saman gado ya gama sharan barci, tashin sa daga barcin kenan sai dai yana a kan gadon bai miƙe ba idanunsa a rufe, ya soma jin sautin nocking, a hankali ya buɗe madaidaitan idanuwansa masu cike da barci yana sakin hamma,
Jin ana sake buga wa ne, sai yace, "Yes." Yana ƙoƙarin tashi zaune,
Ɗakyar ya miƙe ya zauna a bakin gadon amma ya kasa tashi
Itama kuma Maryamu tana jin muryansa sai ta ƙara buga ƙofan da ƙarfi; sabida bata gane muryan waye ba, ba ta son ta shiga ciki kuma ba SHAREEF bane
"Wai waye ne?" Yayi maganar da ɗan ƙarfi yana miƙe wa da nufan wurin ƙofan
Yanzu ta gane muryansa shiyasa ta tura ƙofan ta shiga suka kusa cin karo a bakin ƙofan,
Saurin ja da baya tayi gabanta na faÉ—uwa sabida ganinsa babu kaya daga shi sai short wando
Da tsananin mamaki shi kuma yake kallonta bai iya cewa komai ba illa bin ta da ido da yayi kamar zai cinye ta, yana ƙare wa jikinta kallo
Tana sanye cikin doguwar rigan material blue colour mai design na flowers an ƙawata shi da kalan ja da fatsi-fatsin brown, yayi mata cif ƙirjin nan nata kamar zasu faso a cikin rigan, farin hula ne a kanta na sanyi amma yayi baya kamar zai cire, wanda hakan ne yasa gashin gaban kanta ya bayyana Almajiran gashin kanta sun fito waje, manyan idanuwanta sun ɗan yi ja sakamakon ɓacin ran da take ciki da kuma hawayen da ke tattare a cikin su sun kwanta suna shirin fitowa
Maryamu duk tadabarbarce sabida ganinsa ƙiƙam babu kaya a jikinsa, tana kallon tsarin jikinsa da ke cike da gashi gazar-gazar musamman ƙirjinsa yayi luf sai sheƙi yake yi, shiyasa lokaci ɗaya ta janye idanuwanta tunda tayi masa duba ɗaya, ta ja da baya tana kama ƙofan tare da ƙoƙarin daidaita kanta
Shi kuma yana tsaye ya zuba mata ido kamar zai cinye ta, idanunsa ƙyam a kan ƙirjinta ko ƙoƙarin ɗauke su ba ya yi
Ɗagowan da zata yi ta ga kallon da yake mata, hakan ne ya ƙara fusata ta bata san sanda wani jarumta ya zo mata ba; ta kalle sa rai a ɓace tace, "mene ne dalilin ka na son zama dani har ka iya canza ra'ayi a kaina? Ko har ka manta abubuwan da ka faɗa a kaina ne maganganun ka da baza su taɓa gushe wa a ƙwaƙwalwa ta ba?"
Ɗan waro idanu yayi waje yana mayar da su cikin nata, kamar zai yi magana kuma sai ya kama haɓa yana ci gaba da zare mata idanunsa; alamun har yanzu mamakin ta yake yi
Ita kuma Maryamu ranta ya ƙara ɓaci, cikin fushi da wani irin haushin sa tace, "ko don kana ganin na zama Mutum shine don baka da kunya har kake iya tunanin zaka same Ni a banza a hofi? Wlh bari ka ji Ni Maryamu ba na tsoron ka kuma duk abun da ke raina sai na faɗa maka shi, tun wuri ka je ka janye maganarka kar kayi gigin da zaka ce zaka ɗauke Ni ka kaini gidan ka, kai ka gaya min wannan maganar a baya, amma yanzu Ni ce zan faɗa maka, idan ka sake kayi kuskuren da na sanya ƙafata a cikin gidan ka."
Sai ta kaÉ—a baki tana sake ware manyan idanuwanta da suka sake yin ja,
"Zan nuna maka ainihin wace ce Ni, kuma ƴar ƙauyen nan dai da ka raina."
Ta ja dogon tsaki ta juya zata bar Falon babu ko tsoron sa a cikin ranta