← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 75

Sashe 49

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

__________
*BOOK2*
_______________*PAGE25*
_____SHAREEF kai tsaye ɗakin sa ya koma, gaba ɗaya a sukurkuce yake don har yanzu jin sa yake yi cikin buƙata, ya ga samu ya ga rashi, dole ya shiga yayi wanka ya kimtsa kansa cikin riga da wando na shadda, mai ruwan omo, ba ƙaramin fitar masa da kyawun sa suka yi ba, kayan sun zauna mishi sosai sun ƙara bayyana hasken sa, sak Angon sa ya fito duk da babu hula a kansa, kuma fuskarsa babu walwala sosai a dame take,
Falo ya fita, yana fita ya hangi kayan Maryamu a yashe, zuwa yayi wurin ya É—auka yana shinshina wa yana jin wani irin yanayi a tattare dashi, har wani lumshe idanu yake yi,
Ya jima a haka before ya zuba kayan a saman kujeran yana nufan wurin Dinnig ganin akwai kaya a saman,
Zama yayi shima ya haÉ—a tea É—in ya shanye, sannan ya kora da gasashshen Kazan da ta rage,
Bayan ya gama ya koma kujera ya zauna idanuwansa a kan ƙofan ɗakin Maryamu, ya jima a zaune yana ta faman tunani abubuwan da suka faru duk suka dinga dawo masa, ji yake yi tamkar ya buɗe ido ya sake tozali da ita a gabansa, ba ƙaramin nishaɗi abun da ya faru ya saka shi ba, har zuciyarsa yana jin wani sanyi yana ratsa shi sai dai baza ka taɓa fahimtar hakan a face ɗin sa ba.
Lallai yanzu ya tabbatar da cewan ƊAN HAKIN DA KA RAINA... ga shi duk abin da yake buƙata a jikin Mace Maryamu tana dashi, idan da tun farko yayi haƙuri ya yi wa iyayensa biyayya da tuni an wuce wurin nan, ba wannan zancen ake yi ba, amma idanunsa sun rufe da soyayyar Haseena, bak'ar fatan Maryamu da kuma kasancewar ta ƴar ƙauye su kaɗai yake iya gani a baya, ashe bai san cewa tana da kyakkyawar surar jiki mai ni'ima da kyan kallo ba, ji be a ɗan ƙanƙanin lokaci yanda ta haɓake ta zama cikakkiyar Macen da ko yar shekaru 30yrs baza ta nuna mata komai ba, uwa uba yanda ta ɗauki wanka a yau face ɗin ta ya tsaya mishi a rai, dama shi mutum ne mai son kwalliya, abun da yake ƙara ƙauna kenan a wurin Haseena, idan ta caɓa ado ba ƙaramin tafiya da imanin sa take yi ba, yau sai ga shi ya ga inda makeup ya fi ɗaukar hankali, a fuskar Maryamu, a yau yake sake tabbatarwa tabbas kyakkyawar Mace kyakkyawa ce kawai, koda baƙa ce ko fara, tunda ga shi ya ga inda makeup yayi mugun yin ma bak'ar Mace kyau, skin ɗin ta very smooth and fresh, Mai ɗaukar hankali da kyan kallo, lallai babu abun da gyara bai saka wa, domin yana ji a ransa kawai don Maryamu ta samu inda ta huta ne har wannan kyawun ya bayyana a jikinta, ya san da tana ƙauyen can ne ai ko kashi sai ya fi ta kyau, ashe rashin gyara ne yake ɓoye kyawawa?
Hmm numfashi ya ja mai ƙarfi yana miƙe wa tsaye, ya gaji da zaman shiru yana faman tunani; shiyasa ya nufi ɗaki ya ɗauki mukullin mota ya fita gidan,
Bai da inda zai je dalilin da yasa ya wuce gidan su kenan

Duk an watse Æ´an biki, su Ammee kawai ya tarar a gidan ita da yaranta, itama a gobe zata wuce Abuja

Bayan sun gaisa take tambayar shi Maryamu?

Alhamdulillah kawai yace mata, Na'ilah na jikinsa ta maƙale mishi

Dayake babu Momy a wurin sai ga ta ta fito daga É—akin ta, ta sauko saman benen tana kallon shi

Sai da ya bari ta zauna sannan ya gaishe ta yana wani sussunne kai ganin yanda ta kifa mishi manyan idanuwan nan nata

Amsa shi tayi har lokacin bata janye ido a kansa ba, yayinda take mamakin yanda ta ganshi a wani sukuku kamar akwai abun da ke damun sa, domin Momy a cikin ƴaƴanta babu wanda ta fi karantar yanayin sa sama da SHAREEF, ko awanne yanayi yake tana saurin gane shi sai dai tayi shiru ta ƙyale sa, yanzu kuwa sai dai tace mishi, "ya Maryam ɗin? Ina fata tana nan lafiya babu wani abun da ya faru?"

Kai a ƙasa ya amsa mata don ba ya son sake tozali da manyan idanunta sabida ya gane tuhumar sa take son tayi, shiyasa ya ƙi kallonta

"Hmm Allah yasa dai da gasken ne tana lafiya, zan ma kira ta in ji dai."

Dariya Ammee take yi, tace, "Oh! Aunty, na ga alamun kamar ba ki yarda dashi bane, ai tunda yace tana lafiya tana lafiyar ne."

SHAREEF dai yana jin su bai ce komai ba,
Har lokacin da su Aakifah suka fito suna gaishe shi, sannan ya É—ago kai ya amsa su yana bin su da kallo

Suka zauna a kan kujera É—aya, Aakifan take cewa, "Ammee don Allah zamu je mu sake ganin Maryam kafin mu wuce."

Harara ta dalla musu, "ba na son yawon nan fa, baza ku je ba, tunda jiya kun je meye kuma zaku koma gidan?"

Marairaice fuska suka yi, wannan karon Yusaira ce tayi magana tana cewa, "don Allah Momy ki sanya baki tabar mu, wlh baza mu daÉ—e ba."

Momy tace, "ki bar su kawai su je, tunda ga Mijin nata ma ya baro ta ita kaÉ—ai kar ta zauna cikin kaÉ—aici, ku kira Sadiq yakai ku tunda yana gida."

Farin ciki ne ya cika su suka tashi suna ɓashe baki, da sauri suka wuce,
Na'ilah ma ta bi su tana musu rigimar, "itama zata je."

Yusaira ta aiki Na'ilan wurin Sadiq ta faÉ—a masa abun da Momy tace,
Su kuma suka tafi ɗaki suka hau shirya wa, tunda dama sun yi wankan su kawai sauya kaya suka yi suka shirya cikin riga da skirt na atamfa iri ɗaya, don ba a bambanta musu kaya tamkar ƴan biyu aka mayar da su, su kansu suna jin daɗin hakan domin mutane da dama suna musu kallon Twins ne, since suna kama sosai, kuma ba kowa ya san Yaya da Ƙanwa bane tunda ba sa faɗa komin nacin mutum da son jin ƙwaƙwaf, kansu a haɗe yake sosai baza ka taɓa bambance su ba bare ka ce yaya da Ƙanwa ne tunda babu bambancin jikin su,
Koda Maryamu ta koma can; sai yazamana itama iri ɗaya da kayansu ake mata, komai su uku ake musu, hatta Abee in zai siya musu wani abun tare yake siya musu, su Ammee basu taɓa bambanta Maryamu da ƴaƴansu ba, tabbas ba ƙaramin daɗin zama ta samu a can ba, don ita kanta a yanzu tayi baƙin cikin rashin komawar ta tunda sun saba

Bayan sun shirya suka bar gidan har Na'ilah, Sadiq ya É—auke su a Mota

Aka bar Momy da Ammee suna ta zuba hiran su

SHAREEF kuma na zaune a falon ya ƙi tashi, hankalin sa yana a kan wayansa amma jefi-jefi yana kallon t.v, tunda tashan MBC 2 ne sun saka Film mai kyau, dalilin da yasa ya ƙi tashi kenan yana kallon,
Sai da aka kira sallah sannan ya je yayi ya koma É—akin su ya kwanta abun sa sai barci,
Bai farka ba sai kiran sallan la'asar ya tayar dashi, alwala yayi ya tafi masallaci

Shima Dady ya dawo gidan lokacin, a tare suka dawo daga Masallaci, sai da ya tsare sa da tambayoyi a kan Maryamun yana tambayar sa, "Allah yasa bai muzguna mata ba?"

Kansa ya shafa before ya amsa mishi

Sosai Dady ya sake jan kunnensa a kan Maryamun a kan, "ya riƙe ta da amana, kar ya ci zalunta, ya kyautata zamantakewar su, idan ya ci amanar riƙon da aka ba shi tamkar ya ci amanar su ne, bazai taɓa yafe mishi ba."

Tabbas jikin SHAREEF ba ƙaramin sanyi yayi ba, sabida jin furucin Dadyn, ya san da gaske yake yi tunda ya furta hakan,
Bai dai ce komai ba har yayi musu sallama yabar gidan,
Kai tsaye gida ya koma ya tarar da su Aakifah har yanzu suna nan

Sadiq ma yana tare dasu bai tafi ba, yace, "ƙafanshi ƙafar su bazai je ya dawo ba, gwara a yi hiran dashi."

Lokacin da ya shigo gidan ya tarar dasu suna baje suna hira sai dararraku suke yi,
Har Maryamun wacce tuni ta sauya kaya ta saka kalan atamfar su, don zuwan nasu ne suka tashe ta barcin da take yi,
Sai tsokanarta suke yi a lokacin da suka zo suka tarar da ita babu kaya, tunda kofofin rufe wa kawai SHAREEF yayi bai saka key ba, sai da suka shiga cikin falon suka ji shiru sannan suka wuce É—akin Maryamu,
Bayan sun kwanƙwasa ta farka, tana jin su ne ta buɗe musu ƙofan ko kaya bata sanya ba; illa blanket ɗin da ta rufe jikinta ta zo dashi har ƙofan ta buɗe musu

Dalilin da yasa suke ta tsokanarta kenan suna dariya, musamman da suka ga kayanta a falo,
Sai da suka gama shaƙiyancin su suka fada mata, "da Yaya Sadiq suka zo yana falo."

Sai tayi maza ta ciro kayanta tana cewa, "irin naku ma zan sa, anko zamu yi wlh."

Tana gama wa suka fita falon,
A nan suka shantake suka yi ta hira har suka yi girki tare suka ci suka ƙoshi suka wanke komai,
Sallah kaÉ—ai ke tayar dasu

Sadiq ma a falon yayi Sallah ya ƙi fita ya biye musu suna ta surutai

Shigowar SHAREEF ne yasa suka dakata da hiran nasu,
Yayinda idanunsa na a kan Maryamu yake amsa gaisuwar da suke mishi

Ita kuwa ko ɗago kai ta kalle shi ta ƙi yi, sai yanzu ta soma jin kunyar abun da ya faru tsakanin su, takaicin da ya rufe ta kuma yanda ya gama ƙare mata kallo babu riga,
Bata san sanda ta É—aga kai ta watsa mishi wani kallo har da harara ba

Waro ido SHAREEF yayi yana mamakin abun da tayi masa,
Amma bai ce komai ba ya wuce É—aki,
Na'ilah na biye dashi kamar jela tana kiran sunan shi

Aakifah ce ta raÉ—a wa Maryamu a kunne, "Mijinki fa ya dawo ki je ki tarbe shi, ba ki ga sai kallon ki yake yi ba."

Dukan ta Maryamu tayi tace, "ban san iskanci fa."
Chapter 49 · 0% Book details