← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 75

Sashe 3

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

__________
*BOOK2*
_______________*PAGE2*
_____Kafin ta dawo cikin hayyacinta; tuni ya koma ya ɗauki Jakar kayansa da yake yashe a cikin Falon, ya buɗe ƙofan ya fice a mugun fusace; ko damuwa da duhun da ke gari bai yi ba, haka ya fice a gidan ya bar ƙofofin a buɗe

Inda Haseena na yashe a ƙasa babu kaya a jikinta, sautin marukan da yayi mata sai amsa kuwa suke mata a cikin kunne, tunda uwarta ta haife ta bata taɓa jin azaba makamanciyar irin wannan ba, sosai marukan da yayi mata suka ɗimauta ta suka fitar da ita gaba ɗaya a cikin hayyacinta, wani irin kuka ta saka har yanzu tana kwance ta gaza buɗe idanunta sabida azaban da ke ratsa ta,
Kukan kawai take yi kamar zata shiÉ—e don azaba, tana jin tamkar yanzu ne ake marin ta domin yanda wurin yake mata zafi ko hannayenta ta kasa cire wa a wurin,
Tsawon lokaci tana a haka before ta buɗe jajayen idanuwanta cikin kuka ta soma yunƙurin tashi zaune, babu inda jikinta ba ya rawa, take ta sake mayar da hannayenta a wurin domin ji take yi kamar an sauya mata halittar kumatun ta, wurin ne ya kumbura suntum har da shatin yatsunsa, domin ba ƙaramin mari ta sha ba a wurin SHAREEF, abun da bata taɓa tunani ba, wai yau ita SHAREEF ya mara,
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Ba marin ya fi É—aga mata hankali ba illa tafiyar da yayi ya barta,
Daƙyar ta iya mike wa ta isa cikin bedroom tana neman kayan da zata saka, kuka sosai take yi ko saurara wa kanta ba ta yi, domin hankalin ta idan yayi dubu to ya tashi, ba ta jin zata iya rayuwa babu SHAREEF a tare da ita, ƙaunar da take masa hakan bazai taɓa sa ta rabu da shi ba,
Tabbas a yau tana tsananin cikin dana-sanin aikata zunubin da tayi, bata taɓa tunanin kasancewar ta da Nana zai sa har SHAREEF ya gane ba, kenan ta rasa budurcin ta batare da ta mu'amalanci namiji ba? Dama hakan tana iya kasancewa ne?
Wani sabon kuka ta fashe dashi tana ɗaura kanta a saman gadon, while jikinta na a ƙasa tana ta sharɓan kuka, ta rasa ma me ke mata dad'i babu inda jikinta ba ya rawa, cikin kukan take cewa, "don Allah SHAREEF ka dawo gare Ni, bazan iya rayuwa babu kai ba, kai kaɗai nake so, kayi min alƙawari ko mene ne baza ka taɓa iya rabuwa dani ba, ba laifi na bane, Ni kaina ba a san raina na aikata wannan zunubin a gare ka ba, babu yanda zan yi ne, wlh bazan taɓa iya rabuwa da kai ba."
Sambatu ta dinga yi kamar wata mahaukaciya, gaba ɗaya ta kasa sararawa kanta jin ta take yi tamkar ta kashe kanta don baƙin ciki,
"Ka yi hakuri don Allah SHAREEF, ban taɓa aikata zina ba, ban san hakan zai kawar min da budurcina ba, Nana ce ta cuce Ni, Ni ban san meyasa na biye mata ba."
Idanunta jazur sun gama kumbura sun yi suntum, ta gaza yin shiru haka take ta sambatu kamar akwai SHAREEF ɗin a gabanta, miƙe wa tayi ta nufi ƙofa zata fice, sai dai yanda ta ga gari yayi duhu alamun dare ya tsala, baza ta iya fita a haka ba, tsoro bazai bar ta ba, don haka ta rufe ƙofan tana koma wa daki ta ɗauki wayanta, kiran layin SHAREEF ta soma yi, tun farko da ya shiga yayi rejected tare da kashe wayan gaba ɗaya, koda ta sake kira sai ta ji a kashe, kuka ta dinga yi ta kasa runtsa wa a daren nan, wayanta na a hannunta lokaci kaɗan ta dauka ta kira sa, but abu ɗaya ake faɗa mata wayan a kashe; amma ta kasa hakura, babu irin text na bada haƙurin da bata tura masa ba, amma babu reply, ƙarshe a haka ta kwana a ƙasa batare da ta san lokacin da barci ɓarawo ya sure ta ba.
***

_____Kai tsaye SHAREEF hotel ya wuce ya kama É—aki, tunda ya shiga ya rufe kansa ya kwanta bai sake motsa wa ba, kamar matacce haka ya koma, hawayen da ke fita a kwarmin idanunsa su kaÉ—ai zasu tabbatar da cewan yana raye, abun yayi masa ciwon da har ya kasa bama kansa damar yin wani tunani, tamkar ya haÉ—iya zuciya ya mutu haka yake ji, musamman in wasu tunanuka suka bijiro masa a kan Haseena ta ci amanar sa, kuma bai san tun tsawon lokacin da ta É—auka tana mu'amala da Maza ba bayan shi, duk irin son da yake mata da tattalin zuwan wannan ranan, ashe wani ya riga sa? Maiyasa Haseena zata ci amanarsa irin haka? a karon farko; a karon farko ya soma jin nadamar sanin ta a rayuwa,
Shi mutum ne mai tsananin zafin kishi, zai iya yin komai a kan abun da yake so, idan yace komai; to yana nufin komai, shiyasa dole ya hassala ransa yayi mugun ɓaci, wani irin kishi mai zafi ya turniƙe shi wanda yasa ya kasa control kansa,
Da zafin zuciyar ya kwana a wannan halin tamkar matacce har garin Allah ya waye, kuma bai runtsa ba ko kaÉ—an, bare shi ba mai ibada bane balle ya nemi sassauci wurin Allah; yanda ka san kamar zai cire zuciyar ya yasar tsaban tafarfasan da take mishi,
Har safe yayi ya kasa tashi sabida yanda ya ji jikinsa ya saki ga wani irin ciwon kai da ya kawo mishi mamaya, zazzaɓi ne mai zafi ya soma kama shi sabida yanda abun ya tsaya mishi a rai zuciyarsa ta jagule tamkar zata fito ƙirjinsa don zafi da raɗaɗi,
Ko sallah ya kasa yi a haka ya zauna har rana,
Daƙyar ya iya samu ya tashi jiri na son kayar dashi, a haka ya shiga toilet ya daura alwala idanunsa sun canza kala face ɗin nan ta ƙara jazur da ita duk ta kumbura, sallan asuba ya gabatar ya haɗa dana azahar sannan ya koma ya sake rafke wa zuciyarsa na tafarfasa; a duk second ɗaya idan ya tuna abun da Haseena tayi masa ji yake yi tamkar ya mutu,
Dole ya koma ya tuhume ta a kan wanda ta ba shi kanta, domin bazai taɓa samun sukuni ba muddin bai aikata abun da ke zuciyarsa ba.
***

_____Haseena tana kwance itama har garin Allah ya waye ba tare da ta farka ba, wani wahalallen barci take yi mai cike da mafarkai kala-kala a kan SHAREEF; tunda shi ne ya tsaya mata a rai,
Wayanta ne ta soma Ring; wadda ta sa lokaci guda ta farka a gigice,
A tunanin ta ko SHAREEF ne shiyasa nan da nan ta wawura wayan tana duba screen É—in, sunan Nana da ta gani shiyasa ta ajiye wayan jiki a sanyaye,
Ƙin ɗaukar wayan tayi duk da tana jin kiran da take mata, almost three missed calls before ta dakata

Sabon kuka ta saka a lokacin tuna abun da ya faru jiya, wi-wi haka take kukan domin tana jin baza ta iya yafe wa kanta ba in har SHAREEF bai yafe mata ba, taya ya zata iya rayuwa mai daɗi babu shi a kusa da ita? Fushi fa yake yi da ita; wanda hakan bai taɓa faruwa ba,
A nan ta wuni tana kuka ta kasa yin komai sai duba wayanta da take yi tana sake neman layin sa, but har yanzu switch off ake ce mata,
Tabbas in har bai yafe mata ba baza ta taɓa iya zama a ƙasar nan ba, dole ne ta koma gida, ta je ta ba shi haƙuri ta faɗa masa gaskiyar abin da ke faruwa, ita bata taɓa sanin wani namiji ba, wlh bata taɓa sanin son da take mishi ya zarce haka ba sai a yanzu da ta san cewa ta rasa shi, ji take yi kamar tayi hauka, tabbas baza ta iya rayuwa babu SHAREEF ba, soyayyarsa ya bi jinin jikinta ya zama tsoka a jikinta, fushin sa babban illa ne a gare ta,
Tashi tayi ta shiga toilet tayi wanka shaf-shaf ta fito, ko tsaya shafa komai bata yi ba ta soma haɗa kayanta a trolly; after ta zura doguwar riga mai sulɓi da mayafinta. dama rabon da tayi sallah ta manta, sai idan ta ga dama ne zata haɗa su dukka a lokaci guda ta rama, yanzu kuwa hankalin ta a tashe yake bata da time,
Tana jin wayanta tana ƙara but ta ƙi ɗauka tunda ta tabbatar da Nana ce, ga yunwa da ke addabar ta amma bata bi ta kai ba; ta ja trolley ɗin ta zuwa Falo, komai na na'ura ta kashe sannan ta fice zuwa waje,
Wurin Motanta ta nufa, but bata kai ga shiga ba sai ga Nana ta shigo gidan,
Hango ta da tayi shiyasa tayi saurin ƙarisa wa wurin motan tana buɗe wa da sauri ta jefa Jakar ciki, sannan ta zagaya zata shige motan

Sai dai tuni Nana ta iso wurin ta tana kiran sunan ta cikin mamaki,
"Haseena, where are you going now?"

Daurewa Haseena tayi ta juya tana kallon ta fuskarta babu walwala

Sosai Nana ta tsorata da ganin yanda fuskar Haseena ta koma, ta kumbura suntum ga shatin yatsu alamun an mare ta, idanuwanta sun canza kala sun yi jazur,
That's why one time Nana got confused and asked what was bothering her?
Tuni ta kamo hannunta a rikice cikin tashin hankali

Amma sai Haseena ta kaɓe hannunta, lokaci guda hawayen da take riƙewa suka soma zuba a kan face ɗin ta, cikin rawan murya take cewa, "Leave me for God's sake, I will go, daga yau babu Ni babu ke, from today I am gone, don't come to my place again, domin tarayyana da ke babu alkhairi, a kanki zan rasa wanda na fi so da ƙauna, sake Ni."
Ta sake janye hannun tana share hawayenta tare da ƙoƙarin juyawa ta shiga Motan

Amma sai Nana ta sake riƙo ta da ƙarfi sabida ranta ya ɓaci da jin kalmomin Haseenan, take tayi amfani da tsafin ta wurin control ɗin ta, suna haɗa ido lokaci guda idanun Nana suka juye zuwa ja wani walƙiya suka soma fitowa suna shiga idanunta
Chapter 3 · 0% Book details