← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 75

Sashe 14

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai ya sakar mata tattausan murmushi yana cewa, "Zan fi jin dad'i idan muna tare na riƙa ganin wannan murmushin naki mai ƙara miki kyau da haiba, ki manta da wannan Yaron babu wanda ya isa ya sake ɗaga hannu ya taɓa ki in har ina tare da ke, nayi miki wannan alkwarin, amma sai dai..."
Sai yayi shiru yana cije laɓɓa, yayinda yake kallonta cike da so da ƙauna

Ita kuma ta kasa É—ago kai ta sake kallonsa duk da kalaman nasa suna mata dad'i, wanda nan take suka soma sanyaya mata zuciya tare da yaye mata damuwarta,
Shiru tayi tana sake kasa kunne da jin zantukan shi

A cikin cool voice mai ratsa zuciya still ya kira sunan ta

Wanda hakan ba ƙaramin faɗar mata da gaba yayi ba, ɗakyar ta ɗago kai tayi mishi duba ɗaya tayi saurin janye idanun sabida kallon da yake mata, wanda take kumburarrun idanuwanta suka nitse cikin nasa, baza ta iya juran kallonsa bane sabida yanayin kallon da yake sauke mata, dalilin da yasa ta duƙar da kanta kenan tana murmusawa a hankali

Karon farko da ya ga face É—in ta da murmushi shiyasa shima ya sake sakin murmushin yana jin a ransa zai yi nasara Insha Allahu, "ina son in tambaye ki a kan wani abu, but kar ki yi min wata fahimta daban sabida akwai maganar da zamu yi daga baya.
Zan iya sanin aƙidan ki?"

Shiru tayi tana maimaita tambayan a ranta duk da bata fahimci mai yake nufi ba

Shi kuma ganin tayi shiru kuma ta ƙi kallonsa, sai ya sake cewa, "i know za ki ji tambayar tawa wata iri, but kawai don na ga kina yawan saka baƙin Hijab ne shiyasa nake tambayar ki, sabida na ga ƴan Shi'a suka fi saka wa."

ÆŠago kai tayi ta kalle sa, sai tayi murmushi mai sauti wadda fuskarta tuni ta washe alamun maganar nasa ne ya bata nishaÉ—i,
Hannunta ta É—aga tana masa bayani bakin ta a washe

Dariya yayi yace, "kin san ba na gane Yaren nan naki, amma very soon zan koya ko don sabida ke, sabida ke; ke kaÉ—ai."
Ya ƙare maganar cikin wani salo yana zuba mata ido kamar zai cinye ta

Da sauri ta É—auke nata idanun cikin jin kunyarsa, sai dai ta kasa wani motsi sai murza hannayenta da take yi idanunta a kan titi

"Oya, faÉ—a min mana, ki rubuta min text ina son sanin amsar ki."

Wayanta ta ɗauka cikin jaka, ta soma mishi typing, after ta gama bata tura ba sai ta miƙa masa wayan ya amsa

"Ni ba ƴar Shi'a bace, It's just that it's my favorite color, I really love the black color very much, that's why kodayaushe nake sanya baƙin Hijab."

Yayi mamakin amsar nata, kuma ta burge sa, shiyasa ya dube ta yace, "but any time kalan kike saka wa, why don't you change?"

Shiru kawai tayi tana ci gaba da mirza yatsunta

While shi kuma sai ya ajiye mata wayan nata yana faÉ—in, "yau ina son in faÉ—a miki wata magana mai muhimmanci, but sai dai zuwa anjima idan mun fito daga meeting zan neme ki."

Kanta ta É—aga masa har yanzu bata kalle sa ba, idanunta na a kan cikin companin da suka shigo

Shima bai yi magana ba har ya dakatar da motan,
Sannan ya leƙa back sit ya dauko Jakarsa

Itama wayanta ta É—auka tunda tana jin sanda ya ajiye,
Kallonsa tayi but ganin yana shirin juyo wa gare ta, sai tayi saurin É—auke idanunta a kansa ta buÉ—e motan da sauri ta fice

Murmushi kawai yayi yana dubanta, har cikin zuciyarsa yake jin farin ciki a tare ita, yau dai dole zai bayyana mata irin tarin ƙaunar da yake mata, ya shirya tsab domin fuskantar ƙalubalen sa,
Da zaran ta amince dashi zai gabatar da ita a wurin Iyayensa; domin sanin wace ce ita,
Kuma yana da yaƙinin Insha Allahu zasu fahimce sa, shi yake da burin zama da ita a haka, kuma Insha Allahu bazai taɓa samun matsala ba daga wurin Iyayensa

Har ya fito tana tsaye tana jiran sa domin ta kasa tafiya,
Sai da ya fito sannan ta zagaya side din sa tana mishi nuni da ya bata Jakar sa ta riƙe

Fahimtar hakan shiyasa ya girgiza mata kai yana Æ´ar dariya kaÉ—an, tare da furta, "no ki bari kawai, ba na fatan in sanya Gimbiyyata irin wannan aikin mai wahala. Mu je kawai."
Ya nuna mata hanya yana zuba mata murmushin sa mai kyau

Zuciyar Amra gaba É—aya ta soma mata wani iri sabida yanda take jin gabanta yana faÉ—uwa a game da kallon da Hanif yake mata da kuma kalaman sa, amma sai ta daure ta janye idanuwanta before tayi gaba yana bin ta a baya, gaba É—aya tana jin ta a takure musamman yanda ya tasa ta a gaba, tana ji a jikinta ita yake kallo shiyasa ta sake natsuwa sosai tana tafiyarta a hankali gudun kar ta harÉ—e; cus yanda take ji a jikinta da jin idanuwansa a kanta

Bayan sun isa office É—in, sun tarar da Secretary É—in sa har ya zo ma,
Yana ganin Hanif É—in yayi saurin amsar mishi Jakansa yana masa welcoming

Itama Amra sai tayi masa sannu ta wurin É—aga masa hannu tana washe masa baki

Murmushi yayi ya É—aga mata hannu before ya bi bayan Hanif da sauri suka shiga office É—in

Amra zama tayi a kan kujerar ta tana sauke numfashi a hankali, shiru tayi tana tuna fuskar Hanif, a ranta tana mamakin kirkin sa, babban Mutum dashi amma ya kasance mai taimaka mata, bai É—auki kansa a bakin komai ba yana hurÉ—an shi babu girman kai ko wani isa na masu shi,
Gaskiya shi alheri ne a rayuwarta, tabbas ya taimaka mata sosai a rayuwa, tana son tayi mishi godiya a kan abun da yayi mata yau,
Amma ta yanke shawarar zuwa anjima in zasu yi maganar da yace, zata nuna masa godiyar ta,
Tana nan zaune har Secretary ya fito ya taho wurin ta yana mata dariya,
Cikin faram-faram suka gaisa duk da shima ba wai ya iya Yaren su bane, amma suna yawan chart a waya since yawanci shine mai kula da ita, kuma mataimakiyar sa ce tare suke aiki

Yanzun ma aikin suka ɗaura suna yi suna ɗan taɓa hira, duk da shine yake bata bayanan a kan aikin nasu, ko ya sako wasa a ciki,
Ita dai sai dai tayi murmushi ko dariya, in da yiwuwar ta maida masa da martani sai tayi masa typing a kan waya ya karanta

Ƙarfe biyu suke da meeting,
Zuwa ƙarfe daya suka tashi a aiki,
Daga nan masallaci suka wuce kowanne ya gabatar da Sallah before suka yi lunch,
After an dawo daga break sai suka wuce meeting

Yau SHAREEF bai zo ba dole Hanif ne yake jagorantar komai tunda hakan suke yi,
Masu offices- offices da su aka yi meeting É—in,
Sauran ma'aikatan kuma suna bakin aiki

Amra ita kaÉ—ai ce a office tana faman aiki, since Secretary tare da Hanif suna can tare a wurin meeting É—in,
Bata san da shigowar ta ba sabida hankalin ta na a kan computer tana faman daddanna wa,
Sai sallamanta ta ji a dab da ita,
Da sauri ta É—ago kai tana kallon Matashiyar budurwan da ke dab da ita, wanda a haife baza ta fi 19years ba

Tana sanye cikin riga da wando wanda ta É—aura Red colour na Abaya, sai tayi rolling da mayafin shi, face É—in ta babu MakeUp amma ta saka red colour na janbaki ya ji raÉ—au,
Ƙafafunta sanye cikin Black cover shoes masu ɗaukar hankali,
Ta rataye hangbag ɗin ta tana riƙe da wayanta a hannu

Ido Amra ta zuba mata tana kallonta

Hakan ne yasa Haajara ta yatsina face tana faÉ—in, "kina jin ina sallama, ko ba kya amsa wa ne?"

Kanta ta girgiza mata tana sakin murmushi tare da É—aga mata hannu

Haajara tace, "tofa, alamu da Kurma nake magana kenan?"

Kai ta É—aga mata still face É—in ta da É—an yalwan fara'a

Ita kuma sai ta ja tsaki tana nufan office din Hanif ba tare da ta sake magana ba,
Koda ta shiga ta ga babu kowa sai ta dawo tana kallon Amran tare da cewa, "wai ke da gaske Kurma ce kenan? To ya aka yi aka É—auke ki aiki tunda ba ki da wani amfani a nan?
Taya ya za ki yi min bayanin inda ya tafi?"

Shiru Amra tayi sabida sam kalaman Haajaran basu yi mata dad'i ba, shiyasa ta kasa mata bayanin komai sai kallonta da take yi

While Haajara ta bi ta da kallon ƙasƙanci tana jan guntun tsaki, tare da ja da baya ta nemi wuri ta zauna tana harɗe ƙafafu, ta soma latsa wayanta batare da ta sake kallon inda Amra take ba

Itama dai bata sake bi ta kanta ba tunda ta ga ta zauna, sai ma ci gaba da aikin gabanta da tayi har sanda su Hanif suka dawo

Yayi mamakin ganin Haajara a office din nasa, cike da mamaki fuskarsa da É—an fara'a yake cewa, "Haajara, ke ce?"

Tashi tayi tana masa murmushi da faÉ—in, "wlh kuwa, na zo nan kusa da ku ne shine nace bari in zo mu gaisa, and kuma na je office É—in Yaya SHAREEF aka ce min bai zo ba shine na zo nan."

"Ok mu shiga ciki."
Yayi maganar yana yin gaba zuwa office É—in sa

Bayansa ta bi suka shiga ciki, after sun zauna ta gaishe shi fuskarta da murmushi har yanzu

Ya amsa ta yana faÉ—in, "ya mutanen gidan? Kowa lafiya ko?"

"Alhamdulillah, ya aikin naku?"

KafaÉ—a ya É—age yana ware hannunsa da É—an dariyansa yace, "aiki da dad'i zamu ce, amma ba dad'i."

Dariya tayi tace, "kai Yaya Hanif, da daɗin dai tunda ga shi nan har ya sauya ka har wani ƙiba kayi, mun daɗe bamu haɗu ba sai yau, Kodayake dama Yaya SHAREEF ne yake zuwa but kamar baka sanmu ba; har yanzu baka sake takowa inda muke ba."

"To ban da abunki, mai zan zo in yi? Since itama Matar Bro É—in ba ta nan kinga babu abun da zai kawo Ni."
Chapter 14 · 0% Book details