← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 75

Sashe 20

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

While shi kuma DPO ya sake jan kunnen su Jabir tare da Abokansa, kuma yace, "an yafe musu wannan laifin ne kawai don sun ci albarkacin mutanen nan, amma da basu isa ya sake su ba."
Rubutu yayi ya basu suka saka hannu, har Baba Jafaru da baƙin ciki da haushi ya cika sa kamar yayi hauka,
Itama Mama ta saka hannun sannan DPO ya sallame su,
Dukkan su suka fita a tare, Hanif ya ja su Mama suka wuce gida

A Mota sai sanya mishi albarka take yi har da kukan ta, farin cikin ta ya gaza ɓoyuwa, sai faɗa masa take yi, "ya ƙara ma mahaifinsa godiya don Allah."

Hanif kuwa murmushi yayi yace, "Mama babu komai, Dady yana yi wa da yawan mutane masu matsala irin wannan, don yayi muku kyautar gida ba komai bane, zuwa gobe sai ku shirya da wuri zan zo in tafi da ku tare da takardun gidan, ba sai Amrah ta je aiki ba nima bazan je da wuri ba, zuwa ƙarfe goma zan zo mu wuce."

Dad'i kamar ya kashe su, farin cikin su ya gaza ɓoyuwa,
Ita kanta Amra haƙoranta sun ƙi rufuwa don farin ciki, yau dai matsalar su ta kau duk a sanadin Hanif, shiyasa a ranta wani irin farin ciki da ƙaunarsa ne gauraye kamar ta samu bakin da zata iya furta masa ƙaunar da take masa; gami da godiyarta gare shi

Sai da ya kaisu lungun gidan su sannan ya sauke su,
Sallama kawai suka yi ya tafi, duk da yana son ganawa da Amra amma ya gaza tsayar da ita, kasancewar magriba tayi a time ɗin ma, ana ta ƙwalla kiran sallah

Ita kanta tayi tunanin zai tsayar da ita ne, amma kuma tunda ta kalle sa suka haÉ—a ido ta É—auke kanta sai zuba murmushi take yi, cike da kunya da tsananin soyayyarsa,
Tana jin godiyar da Mama take masa amma ita bata da bakin magana,
Sai da ya ja motan zai tafi before ta sake kallonsa duk da ba ta ganin sa,
Sai da motan tayi nisa before ta bi bayan Mama suka wuce gida,
Suna shiga bata tsaya mayar da hankali a kan su Afra da suka dame su da tambayoyi ba, kai tsaye dakin su ta wuce ta ɗauki wayanta ta soma rubuta text, domin abun da zuciyarta ta kitsima mata kenan, ba ta son ta ƙara jinkiri bata bayyana masa godiyarta a gare sa ba, don haka ta tsara mishi tausasan laffuza masu ɗaukan hankali da ita kanta bata san ta iya su ba, fuskarta ɗauke da murmushi haka take typing ɗin cikin yanayin shauƙi, daga karshen ta rubuta mishi tana matuƙar ƙaunar shi,
Sai da ta sake karantawa before tayi sending ta tura masa zuciyarta wasai, text É—in yana tafiya ta rungume wayan idanunta a rufe tana dariya mai sauti cikin farin ciki.
***

_____A hanya Hanif ya ji ƙaran shigowar text ɗin, bai ɗauka ba sabida tunanin da ke tare da shi, hankalin sa gaba ɗaya yana ga tunanin Amra shi kansa sai zuba murmushin yake yi cike da tsananin ƙaunarta, Allah ya ɗaura masa son wannan baiwa nasa, wanda bai taba tunanin hakan ba,
Sai da ya iso bakin gidan su before ya dawo hayyacinsa, horn yayi kusan sau uku before mai aikin gidan ya rugo aguje ya buɗe masa gate ɗin, don a lokacin Mai gadin ya kewaya, shi kuma mai aikin yana wurin yana alwala, sai yayi saurin ƙarisa alwalan ya je da gudu ya buɗe masa

Bayan yayi parking bai tsaya ɓata lokaci ba ya fito ya saka wayan a aljihun sa ya nufi cikin gidan da sauri,
A nan falo ya ci karo da su Dady suma sun fito zuwa masjid,
Da sauri ya ƙarisa toilet ɗin Falo ya ɗaura alwala ya bi bayansu,
Sai da aka yi sallan isha'i sannan suka dawo gida gaba É—aya

Sai lokacin Momy ta nemi ta ji abun da ya faru a station din,
Dady ya zayyane mata komai,
Ita kanta ta tausaya musu matuƙa tare da Allah wadai da masu hali irin na Baba Jafaru; don kowa ya san son zuciya irin na wasu mutane da ke faruwa a yanzu, mugunta da cin zalun marayu yanzu ya zama ruwan dare,
Kuma ikon Allah a cikin su babu wanda yayi zargin akwai wata alaƙa tsakanin Amra da Hanif, baya ga na wacce take aiki a ƙarƙashin sa basu kawo komai ba, musamman da suka ji cewa yarinyar Kurma ce, kawai sun yi tunanin maybe taimaka mata yake yi har ya je ɗauko ta, ko kuma sun saba tunda ma'aikaciyar sa ne, bare shi mai tausayi da sanin yakamata, ko kusa basu taɓa kawo Hanif zai so ta ba,
Shiyasa tuni sun sauya zancen sun koma hiran su daban

Har suka yi dinner Hanif bai duba wayansa ba tunda hankalin sa yana wurin hira,
Sai da Mahmud ya kira sa yana sake tuntuɓan shi a kan maganar da suka yi ɗazu, da kuma saƙon da ya tura masa a WhatsApp,
Shaf ya manta wlh, shiyasa da sauri ya kashe kiran ya soma duba wayan, a nan ya ci karo da saƙon Amra da ta tura mishi ta text messages, har zai wuce sai ya ga sunan ta ne that's why ya shiga yana karanta wa,
Abun farin ciki bakin sa ya ƙi rufuwa don dad'i

Dady da ke gefensa shi ya soma kula da shi, shiyasa yace, "my Son lafiya dai? Me kake kallo haka kake wannan fara'an?"

"Dad babu komai, wani saƙo ne mai muhimmanci da aka tura min, amma bari in je ɗaki Goodnight ina da aiki."
Yayi musu sallama ya wuce da saurin sa,
ÆŠaki ya koma zuciyarsa na masa wani irin dad'i, musamman da ya ji kalman son da ta furta masa, ji yake yi tamkar ya shiga wayan ya je ya haÉ—u da ita, wayyo! ina ma tana magana ya kira ta ya ji muryanta?
Amma duk da haka zama yayi ya tsara mata nashi text É—in tare da nuna mata farin cikin jin kalaman ta,
Yana nan zaune yana jiran amsarta don babu abun da yake bukata da ya fi wannan, don haka tuni ya sake manta wa da duba WhatsApp ɗin sa; ya mayar da hankali kan saƙon Amra da ta sake turo masa,
Daga haka fa sai suka ɓige da chart suna bayyanawa junan su irin ƙauna da begen da ke tare da su

Sai da SHAREEF ya shigo É—akin before Hanif ya tuna da zancen Mahmud,
Sai fa lokacin ya shiga WhatsApp din ya buɗe saƙon,
Video ne shiyasa ya kira SHAREEF yana faÉ—a masa, "Mahmud ya samo wani evidence tun É—azu ya tura masa, da alamun an dace yanzu."

Jin haka yasa SHAREEF ya dawo gefen sa ya zauna suka fara kallon videon

Kamar yanda Mahmud yayi ma Hanif bayani ne ɗazu, akwai wani hotel kusa da Companin da suke gina wa, to bayan zuwan su Mahmud jiya sun fita da wani Abokinsa ya je raka sa hotel din tunda a nan ya sauka, suna cikin zanta wa sun fito waje suna maganar building ɗin da suke aiki akai, since daga wurin suna hangen ginin kasancewar yana opposite da hotel ne, kawai sai wannan tunanin ya faɗo wa Mahmud, cikin ƙanƙanin lokaci ya tuna ai hotel din nan akwai Cameras, mai zai hana su bincika ƙila za a dace a samu wani evidence na gobaran da ya faru, don dama har lokacin suna nan suna fama da neman hujja amma sun kasa samu, abun na ransa kuma sai tunanin nan ya faɗo masa,
Dalilin da yasa yayi sallama da Abokin nasa kenan, bayan ya wuce shi kuma sai ya tafi wurin ma'aikatan hotel din ya nemi ganin Managern su,
Allah cikin ikon sa duk da ya ba shi bayanin abun da yake so, amma sun ƙi ba shi goyon baya sai da ya basu cin hanci, sannan aka duba Cemaran da ke side na building, Mahmud yana da tabbacin za a iya samun wani abu tunda gobaran da yammaci ta afku,
Kuma da aka duba na dai-dai ranan da gobaran ta faru, exactly sai ga shi an ga wasu mutane biyar da suke ta zirga-zirga a ranan, tun daga safe har yamma, sai kuma aka ga sun zagaya ta wani ɓangare sun haura ba tare da sanin masu gadin wadanda suka tafi yin sallan la'asar ba,
Videon ya nuna sun jima a ciki sannan aka fara ganin hayaƙi ya soma ci,
Abun da ya É—auki hankalin mutane da masu gadin da suka rufta ciki don ganin mai ke faruwa,
Nan fa suma jama'a suka hau hatsaniya suka mara musu baya,
Babu jimawa sai ga su sun fito mutanen da Mahmud yake kyautata zaton su suka haddasa gobaran, domin sai a lokacin ya ga fuskar sani a cikin su, ya taɓa ganin ɗayan su da ya taɓa zuwa Companin su Hanif ya zo wurin Shuraihu, tabbas tare ya taɓa ganin su

Wannan bidiyon shi Mahmud ya ɗauka ya tura ma Hanif bayan ya soma mishi bayani, tare da ce mishi, "ya shiga kawai ya kalla sai ya kira shi ya ƙara mishi bayani."

To kuma hankalin Hanif ya É—auke sanadin bayyana soyayyarsa wurin Amra bai duba ba,
Shima kuma Mahmud bai kira sa ba don shima bai samu lokaci ba, sai yanzu da ya kira sa ya ƙara tuntuɓan sa since ya ji shiru bai kira ba, yace masa, "anya kuwa ya duba videon da ya tura masa?."

_Ramadhan Mubarakh Masoyana, fatan kuna lafiya? Allah ya amsa ibadanmu ya hana mu ƙishin banza._

[31/03, 9:20 AM] نفيسة OumƊahira: 🌱🌱🌱🌱🌱

       *SHAREEF*
           _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱

_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*Littafina na kuÉ—i ne, ki biya ki karanta, zaku iya samu na a kan wannan numban wayan. 07065334256.*
Chapter 20 · 0% Book details