Sashe 12
Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ni kike kira mugu Meramu? Ai kuwa yanzu zan yi maganin ki."
Hannu yasa ya tallabo mata ƙeya yana dariyan mugunta,
Bintu na ba shi haƙuri amma bai ƙyale ta ba yana cewa, "babu ruwanki, ki bar Ni da yarinyar nan mara kunya, har yanzu ashe bata yi hankali ba?"
Da gudu Maryamu ta ruga tabar gidan tana zagin shi,
Ai kuwa ya runtuma aguje ya bi bayanta,
Dayake akwai dogayen takalma a ƙafanta nan da nan ya kamo ta ya ci gaba da tallabe mata ƙeya yana tsokanarta,
Ita kuma tana zagin sa tana kuka wi-wi, domin duk yanda ta so ta kufce mishi ta kasa
Bashir da akwai mugunta, ba abun da yake so illa ya ga yana cin zalunta, ita kuma da bakin rashin kunya ta dinga zagin sa kenan kamar ba Yayanta ba, yace, "shegiya da bak'ar fuska, ashe har yanzu kina kukan babu hawaye?"
A haka ya iza ƙeyarta suka shiga gidan
Tun a sauro suka soma jin ihun ta
"Ah ah; Kai Kai! Bashir kanka ɗaya kuwa? Kai da aka ce ka kira ta shine ka taso ta gaba kana tallabe ta kamar yanda ka saba ko? Ashe halin ka na banza yana nan?"
Jin muryan Babansu yana wannan maganar, shiyasa Maryamu ta ƙara volume ɗin kukan ta kamar gaske, wurin Baban ta nufa tana cewa, "wlh bazan yarda ba sai an bi min hakkina, wlh Baba tun a can gidan Bintu yake naushina a ciki yana murɗe min kunne kamar zai kashe Ni, cewa ma yayi ai haushina yake ji dama ya rabu da duka na."
"Wlh Baba ƙarya..."
"Yi min shiru mutumin banza, kai baka san yanzu ta wuce duka ba Bashir? Ba na son wannan shirmen na wasan banza, kar in ƙara ji."
Umma Jummai tace, "ai tun farko ban so ya je kiran ta ba, tunda ya ji an ce ta zo a kira ta, yace shi zai je, na san dama da mugunta a ranka wlh, Bashir ba ka jin magana duk ka sa ta raina ka a banza a hofi."
Baba kuwa hannun Maryamu ya ja yace, "ta zauna gefensa."
Yana ci gaba da ma Bashir É—in faÉ—a tare da cewan, "zai haÉ—a shi da su Ashiru in suka shigo tunda bai jin magana."
Maryamu sai dad'i take ji tana masa dariya ƙasa-ƙasa.
***
_____A takaice a Zaria Maryamu ta ƙarisa hutun ta gaba ɗaya, wata ɗaya tayi da satikai a can, ba ƙaramin dad'i ta ji ba don ba kaɗan ba tayi yawo kamar yanda take so, tunda a can basu da lokaci koyaushe suna karatu, shiyasa hutun nan da tayi a garin su ga ta ga ƴan uwanta, ba ƙaramin farin ciki tayi ba,
daga ƙarshe ma daga gidan Iya Samira aka zo ɗaukar ta,
Ammee ta aiko driver tun daga Abujan ya zo ya tafi da ita,
Suma can sun yi murnan dawowanta since sun yi kewarta sosai
A satin suka ci gaba da zuwa makaranta, S.S 2 kenan, har yanzu kuma suna koyon computer duk da kaÉ—an ya rage a yaye su.
🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆
_____Sadiq shima a wannan time É—in ya gama graduation É—in sa, har an nema masa makaranta a can England kamar yanda su SHAREEF suka yi, zai tafi nan da kamar watanni uku masu zuwa zai wuce
Fannin SHAREEF dai babu abun da ya sauya yana can yana fama da dakon soyayyar Haseena, wanda ya rasa dalilin sauya masa da ba ta buƙatar farin cikin sa a yanzu, ga shi yanzu irin son da yake mata ko kaɗan ba ya iya mata faɗa, ba ya son ma abun da zai ɓata mata rai, duk abun da tace eh ko yana so ko ba ya so; eh ne a wurin sa, idan tace a'a ma haka, yana cikin wani hali da buƙatar Mace da ke damunsa, ba ta tsinana masa komai koda ya je wurin ta, sai dai ya ƙara wa kansa matsala tunda bazai samu yanda yake so ba, duk yanda zai nuna mata halin da yake ciki ta gaza fahimtar shi, sau tari yana ganinta da Nana idan ya je can, amma duk faɗan da zai mata da son daƙile alaƙar su,
Ta nuna masa, "sam babu ruwansa ya ƙyale su."
To dayake ba ya son ɓacin ranta sai dai ya haƙura yana ganin su tare ba shi da yanda zai yi, domin ya fahimci cewa alaƙar su da Nana shiyasa Haseena ta soma gurɓacewa ta canza mishi, tunda a zahiri yana kallon wasu ɗabi'u irin nata da take yi, abun ya soma damunsa, ga ba kwanciyar hankali kullum yana faman neman magani a kan matsalar sa muddin in sha'awa ta tashi mishi, shiyasa damuwar da ya sanya wa ransa a haka ya soma ramewa yana fita a hayyacin sa, duk ya sauya kamar ba shi ba
Iyayensa tun abun ba ya damunsu, har sun soma bincikar shi ko zai faÉ—a musu gaskiyar ainihin abun da ya sauya shi lokaci guda, domin ko magana wannan SHAREEF bai cika yi ba yanzu, dama can miskili ne a idon jama'a, to yanzu abun ya shafi har gida ba sa ganin walwalan sa, idan ya zauna ba abun da yake yi sai tunani, yawancin lokuta ma yana yawan rashin lafiya, su basu san ciwon mai yake yi ba amma idan sun bukaci su sani sai dai yace musu, "ciwon kai ne.".
To tun yana ɓoye wa yanzu sun soma fahimtar yanayin ciwon nashi kamar yanda Likita ya taɓa musu bayani, tunda ciwon ciki bai cika ɓoyuwa ba,
Abun yana damunsu matuƙa, amma kuma ai sun san har da taurin kai irin nasa, sun masa gata amma ya nuna ba ya son hakan, ita wacce yake ƙauna tana can wani wurin tana karatu baza ta amfane sa da komai ba, wacce suka ba shi ya nuna ba ya sonta,
Sun zauna sun masa nasiha mai ratsa zuciya a kan ya taimaki rayuwarsa tun wuri ya amince da auren Maryamu ta dawo nan da zama, wataƙil zai samu lafiya tun kafin hakan ya fi ƙarfin sa,
Amma har yanzu SHAREEF maganarsa ɗaya ce ya kafe ba ya son hakan, ya ƙi nuna musu amincewar sa,
Abun yana basu mamaki, shiyasa suka ƙyale shi, idan ya ji jiki don kansa zai dawo kan hanya, zai nemi taimako a wurin su
Inda gefe ɗaya ma Hanif yana ta nuna masa illan hakan, da ya zauna da cuta gwara ya nema wa kansa mafita, amma ya ƙi sauraren su
A ganin shi zai iya da matsalar shi, idan ya sha magani yana samun sauƙi sosai, sai dai idan ya tashi masa dole sai ya zauna jinya
Hanif ma ya fita harkansa don shima yana fama da tashi matsalar, saboda a yanzu Dady ya faÉ—a masa, "gwara shima ya nemo Matar yayi aure tunda lokaci ya soma ja."
To dayake a yanzu Hanif shima yana buƙatar auren, musamman yanzu da ya tabbatar wa kansa yana matukar ƙaunar Amra, duk da har yanzu bai faɗa mata ba, amma gaskiya yana bata kulawa ainun, don yanzu ya saba da ita sosai da sosai, har gidan su yana zuwa, duk ranan da SHAREEF bazai je aiki ba, to idan zai fita da kansa yake zuwa gida ya ɗauke ta, kuma shi zai mayar da ita,
A taƙaice dai har ƴan gidan su Amra sun san shi tunda suna shan labarin sa a wurin ta,
Shigowar sa cikin rayuwarsu ba ƙaramin taimakon su yayi ba, tun suna ɗari-ɗari suna mamakin irin taimakon da yake musu, daga baya da suka fahimci halin sa sai suka saki jikin su
Akwai wani ranan ma da ya zo É—aukar Amra, a nan ne ya tarar da Jabir ya zo gidan yana ci musu mutunci, sai zagin su yake yi yana kumfar baki,
Abun ya ɗaure mishi kai sabida yayi mamakin saurayin matuƙa, kuma tabbas ya gane sa tun ranan farko da ya taɓa ganin sa ya ga tsoro a idanun Amra,
Yanzun ma ga shi ya ga ya janyo ta yana ƙoƙarin barin gidan da ita,
Sun fito zaure yana kiciniyar barin gidan da ita da ƙarfi
Tana kuka tana ƙanƙame jikinta,
Yayinda su Afra suma sun ƙanƙamo ta sunan kukan suma
Mama na faÉ—in, "ina zaka kaimin Æ´a Jabir? Wai baka da tausayi ne baza ka sakar min É—iya ba?"
Karaf sai ganin Hanif suka yi ya shigo cikin zauren hankali a tashe yana cewa, "lafiya Mama? Me ke faruwa ne?"
"Yauwa Hanif, don Allah ka taimaka mana, wannan banzan Yaron ne ya zo zai tafi min da yarinya, ya je yayi shaye-shayen shi ya zo yana mana hauka a nan, ba irin yanda ban yi ba don in kuɓutar da ita amma mun gagara, dole sai ya tafi da ita."
Kallon Amra yayi wacce take ta faman kuka ita da ƴan uwanta, tana riƙe gam a hannun Jabir wanda ke layi idanunsa suna ƙin buɗe wa sabida shawuwan da yayi,
Sai sambatu yake yi yana ci gaba da zage-zagen sai ya tafi da ita,
Hanif cikin rashin fahimta yake ƙara kallon Mama da cewa, "to Mama, shi ɗin waye ne da zai tafi da ita? A kan me?"
Cikin kuka Afra tayi tsulum tace, "wlh Yaya babu abun da ya haÉ—a mu dashi, kullum sai ya zo ya ci zarafin Aunty Amra sabida mugu ne azzalumi, har dukan ta yake yi, ba abun da ya haÉ—a mu dashi wlh."
Hankalin Hanif yayi ƙololuwar tashi da jin abun da Afra take cewa, musamman da ya ji ta ambaci duka, shiyasa ya saka hannu lokaci guda ya finciko rigan Jabir; sai ga shi ya wantsalo gabansa,
Hannu ya sanya ya sharara mishi mari sabida yanda lokaci ɗaya ransa yayi ƙololuwar ɓaci,
"Kai dan Ubanka shaye-shayen naka ne yake faɗa maka ƙarya da zaka zo gidan mutane kana iskanci? Waye ya baka permission ɗin shigowa gidan mutane?"