← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 75

Sashe 67

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

       *SHAREEF*
           _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱

_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*Littafina na kuÉ—i ne, ki biya ki karanta, zaku iya samu na a kan wannan numban wayan. 07065334256.*

__________
*BOOK2*
_______________*PAGE35*
_____Da sassafe sai ga Hanif ya zo gidan shima, lokacin su Momy ya samu a kan dainng suna karyawa,
Ya wuce wurin su ya gaishe su; bayan ya zauna a kan É—aya daga cikin kujerun Dinnig É—in

Suka amsa a tare dukkansu, tare da tambayarsa Iyalinsa?

Yace, "Alhamdulillah tana gaishe ku."

"Muna amsa wa, ya batun maganar neman lafiyarta? Ana samun ci gaba ko har yanzu shiru ne?" A cewar Dady da ya ajiye Cup din hannunsa yana mai kallonsa

Hanif yace, "Dad, to Alhamdulillah zamu ce, but har yanzu dai shiru ne amma tana kan shan magani ne, kuma muna koma wa asibitin kamar yanda suka ce mu riƙa yi, ana dai ta treating ne sai dai mu ga abun da hali zai yi a nan gaba."

Daga shi har Momy suka haÉ—a baki wajen faÉ—in, "Allah ya bata lafiya, yasa a dace."

Ya amsa sannan ya tambayi jikin Maryamun yana faÉ—a musu, "Bro ya kira sa ya faÉ—a mishi komai."

Momy tace, "jiki da sauki, but har yanzu bata farka ba dai, SHAREEF É—in ma yana É—akin ka shiga ka duba ta, tana nan a É—akin ta."

"Ok bari in je."
Ya miƙe yabar wurin zuwa ɗakin kwanan Maryamu a da,
Da ya shiga ya samu SHAREEF zaune a bakin gadon

Shima jin sallaman sa ne sai ya motsa daga kallon Maryamun da yake yi, sannan ya gyara mata blanket ɗin da aka rufa mata jikinta dashi, ya rufe mata ƙirjinta da ke buɗe; tunda har yanzu rigan barci ne a jikinta

Tahowa Hanif yayi ya zauna a bakin gadon shima, sannan ya kalli SHAREEF yace, "ya jikin nata?"

"there is no easy, but please bless us with prayer, she still hasn't woken up, she still hasn't moved, and ji be yadda ƙafarta ta koma."
Ya yaye mishi blanket ɗin yana buɗe masa ƙafarta

Ba ƙaramar tsorata Hanif yayi ba, wani irin mugun tausayinta ya kama sa har tsigan jikinsa yana tashi da ganin yanayin ƙafar, don ma wai ba tun jiya ya gani ba tunda yau da sauƙi za a iya cewa; ya saɓe sosai ba kamar da ba,
Yayinda ya É—auke idanunsa da sauri yana duban SHAREEF É—in, shi kansa yanda ya ga SHAREEF ya sauya mishi a É—an wannan lokacin ya tabbatar yana cikin damuwa, tunda ga shi nan fuskarsa ta nuna, har ya zurma tunda ko abinci bai ci ba daga daren jiya zuwa yau,
Kuma su Momy sunyi-sunyi ya taso ya karya ya ƙiya,
"I'm so sorry Bro, insha Allahu Allah zai bata lafiya, sai dai wannan maganar ba na jin zamu barta a tsakaninmu, yakamata mu sanar da su Momy su san cewa ga abun da muke tunani, tunda zahiri ya nuna dole akwai maƙarƙashiya a cikin wannan abun, kuma ba wanda zai yi mata haka sai Haseena, Haseena ce masoyiyarka, a yanda ku ka so juna komai zata iya yi domin kai, yanzu hankalinka ba ya kanta; dole zata nemi ta dawo da kai gare ta."

"Yes i know..." Sai kuma yayi shiru ya kasa ƙarisa maganar yana mai ɗaura hannunsa a saman goshin Maryamu,
A haka kamar zata yi magana, sai dai har yanzu ba ta motsawa sai numfashi da take sauke wa kaÉ—an-kaÉ—an,
Wani irin ɗaci yake ji a zuciyarsa, ji yake yi tamkar ya dawo da ciwon da ke jikinta jikinsa, bai taɓa tunanin akwai lokacin da zai damu da damuwar baiwar Allan nan ba, sai ga shi komai ya sauya, ta shiga zuciyarsa, yana mata soyayya; soyayyar da bai taɓa yin ma wata ƴa mace a duniyar nan ba, yanda yake jinta a zuciya yana jin zai iya sadaukar mata da komai da kowa nasa in har zata yi farin ciki; har ransa yana jin zai iya sadaukar mata domin ya ga ta kasance cikin farin ciki, a duk second ɗaya da wucewar minti ƙaunarta da tsananin tausayinta ne yake ratsa mishi zuciya, shiyasa farin cikin sa gaba ɗaya ya ƙaurace mishi, ba ya jin daɗi in ba ya ga ta samu lafiya ba, duk inda magani yake in har zai sama mata lafiya zai iya zuwa ya nemo mata, idanunsa sun kaɗa sun yi jazur sun ƙara ƙanƙance wa sabida kukan da yayi jiya; da kuma rashin barci da bai samu ba, uwa uba tashin hankalin da yake ciki,
"Wlh in har wani abu ya samu Maryama; bazan taɓa ƙyale Haseena ba, tabbas zata yi dana-sanin sanina a cikin rayuwarta, domin Maryama ita ce farin cikina a yanzu, ita ce jin daɗina da komai nawa a duniya, ina matuƙar son Maryama! kuma zan so ta har numfashina ya ɗauke, zan bauta mata a dukkan rayuwata!"
Ya ƙare maganar hawaye suna ɗiga a kan kuncinsa, yayinda suke sauka saman nata fuskar kasancewar yayo kusanci da ita sosai; still hannunsa na a saman goshinta yana shafa har saman dunƙulallen gashin kanta da ke narke kamar kan Maza

Hanif kuwa shiru yayi yana kallonsa yayinda yake jin sanyi a cikin zuciyarsa, tabbas ranan da yake jira ne ta zo, ranan da zai ga SHAREEF ya so Maryamu ya tausaya wa rayuwarta, sai ga shi yana ganin tsagwaron soyayyarta a cikin idanunsa, wanda bai taɓa tunanin son nata har yakai hakan a zuciyarsa ba,
Hannu yasa ya dafa masa kafaɗa before yace, "zata samu lafiya da yardan Allah, ka zama mai ƙwarin gwiwa My Brother, zan je in sanar da su Dady abun da ke faruwa, don bazai yiwu mu ɓoye musu ba, and ka zo mu je tare please."

Kamar zai ce mishi a'a, sai kuma ya ɗauke hannunsa daga jikinta yana mai share hawayensa, ya miƙe ya bi bayansa suka fita

A hankali ta soma motsa ayes ɗinta tana ware yatsun ƙafarta, idanunta a rufe suke sai dai tun lokacin da SHAREEF ya soma magana ta farka, kasa motsi tayi sai da suka bar ɗakin before a hankali ta fara moving tana mai ware manya-manyan idanunta da suka canza kala gaba ɗaya, suka yi wani irin luhu-luhu suka ƙara fitowa kamar zasu faɗo,
Take ta mayar da idanuwanta ta rufe sabida yanda take jin jikinta tamkar ba nata ba, babu wani sauran farin ciki a tattare da ita sabida duk yanayin ya sauya mata, kanta ma ta kasa ɗagowa bare ta motsa ƙafafunta, musamman mai ciwon da take jin kamar ba a jikinta yake ba, zugi yake mata tun daga can cikin namanta wani irin azaba na ratsa ta, ga kanta kamar zai ɗaɗɗage,
Daƙyar ta iya ɗago hannunta ɗaya tana kama goshinta ta ƙanƙame bakinta tana juya kan, nan da nan wasu zafafan hawaye suka soma gudun tsere a kan kumatunta, da ta kasa jure wa kuma sai ta fashe da kuka babu mai jinta a lokacin; domin muryanta tayi ƙasa ta dishe sosai ba ta iya yin kukan da ƙarfi sabida azaban ciwon kai.
***

Su Momy sun sha mamakin abun da Hanif ya gama sanar musu,
Ita Momy dayake tana da saurin hawa nan da nan ranta ya ɓaci kuma hankalin ta ya sake tashi ainun, nan take cewa, "tabbas idan haka ne dole mu ɗauki mummunar mataki a kan yarinyar nan, don baza ta zo ta shiga rayuwarmu sannan tace zata muzguna mana ba, mai Maryam tayi mata da zata cutar da ita? Idan ta kashe ta ita don Ubanta zama zata yi tayi gadin duniyar? Ai kuwa komai zata yi in har ina numfashi baza ta sake zama da igiyar auren ɗana ba, in har Ni na haife shi kuma ina numfashi wlh sai na nuna mata bata isa ba tayi kaɗan ko me zata yi."

Dady yace, "ya isa Deeja, wannan maganar fa zargi ne ba a tabbatar ba, sannan zato zunubi koda ya kasance gaskiya, babu ta yanda za a yi mu zarge ta bayan bamu da masaniyar cewa ita ce tayi hakan ko ba ita ba?"

Momy tace, "wanne tabbatar wa ya rage kuma Alhaji? Kana dai jin abun da wannan Aljanin ya faɗa, cutar da ita aka yi a kan SHAREEF, sannan ita Haseenan ita ce wacce ya aura, sannan ga ƙudirin da take shirin aikata wa a kansa, ba don Allah ya tsare da addu'ar da yake yi ba ai da tuni ta ci galaba a kansa, tunda ai yanzu ya rabu da ita meyasa ya ci gaba da jin soyayyarta? Sannan maiyasa ta dawo rayuwarsa? Da yanzu wani zancen ake yi tunda muna ji muna gani zai bi ta wata ƙasar idan ta gusar mishi da hankali, yanzu in bamu san hakan ba sai dai muyi fushi dashi daga ƙarshe ta raba shi da kowa nasa."

Jinjina kai Dady yayi yace, "haka ne, amma duk da haka mu bamu da hujjar ɗaukar mataki a kanta, Allah Ubangiji ya mayar mata da abun da tayi mana in har tana da hannu a ciki, mu namu addu'a ne musamman kai SHAREEF, yana da kyau ka sake dagewa da ibada da addu'a domin shi ne takobin kowanne mumini, muma zamu taya ka da shi insha Allahu, sannan a kan Maryam kuma insha Allahu zamu sake tashi tsaye a kanta wurin samun lafiyarta, Allah zai shige mana gaba kuma mun yarda shi ne mai yi ba wani Mutum ba, don haka mu saka a ranmu babu wanda ya isa ya cutar damu in har ba Allah ne ya ƙaddara hakan a kanmu ba, mu bar maganar nan a tsakaninmu mu fauwala wa Allah komai, Allah ya bata lafiya."

Dukkansu suka amsa da Amin

While Momy da ta ga SHAREEF yana shirin tashi, sai tace mishi, "ya koma ya zauna ya karya."

Cike da damuwa yace, "Mom, bazan iya cin komai ba har sai na ga Maryama ta farka, zan je in duba ta."

"No koma ka zauna My son, idan baka ci abinci ba kaima so kake yi ka rafke mana? Ji be har ka zurma duk ka mutsutstsuke, addu'a zaka riƙa yi ba wai saka damuwa a ranka ba, ka koma ka zauna ka ci abinci sai ka je ka duba ta."
A cewar Dady kenan yana kallon sa
Chapter 67 · 0% Book details