← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 75

Sashe 74

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Takardan ta ciro daga cikin aljihun riganta, wanda tun lokacin da Amran ta miƙa mata ta saka shi a ciki bata buɗe ba, ta miƙa mishi tana cewa, "ita ta rubuta wannan da hannunta, ban san dai mai ta rubuta ba amma tunda kai ne Mijinta shiyasa zan baka, ita tace in baka."

Hannunsa har rawa yake yi wajen miƙa hannu ya amsa, amma sai ya dakata sabida yanda ya ji zuciyarsa tana buga wa yana jin wani irin yanayi yana baƙuntarsa, daƙyar ya idasa miƙa hannun ya amsa,
Sannan ya damƙe takardan ya juya ya tafi zuwa inda sauran jama'ar ke zaune,
Wuri ya samu ya zauna ɗan nesa da su yayi shiru ya kasa buɗe takardan, daga ƙarshe kuma ya buɗe don ƙosawan da yayi ya ga abun da ta rubuta,
Kansa ya dafe a sa'ilin da ya gama karanto rubutun da ta rubuta, wani irin harba wa zuciyarsa take yi kamar zata yi tsalle ta fito, hankalin sa yayi matuƙar tashi duba da yanda ya fahimci kamar wasiyya tabar mishi, hawaye ne ya soma gudun tsere a kan fuskarsa, sabida kar mutane su fahimci halin da yake ciki, sai ya kifa kansa a jikin ƙafafunsa a hankali yake furta, "a'a Insha Allahu baza ki taɓa tafiya ki bar Ni ba My Amra, ina sonki Allah bazai raba mu yanzu ba, Insha Allahu za ki fito lafiya.."
Kukan da ya ci karfinsa shiyasa ya kasa ƙarisa zancen nasa, ya danne bakinsa yana kukan mara sauti,
Yanayin da yake ciki yasa ya kasa kataɓus gaba ɗaya ya nemi ƙarfin jikinsa ya rasa, haka jikinsa ke rawa yana fatan a fito da Amra lafiya a ce masa bata mutu ba,
Burin sa kenan a wannan lokacin

Zuwan SHAREEF wurin, da maganar da yayi masa, shiyasa yayi saurin É—ago kansa yana kallonsa, yayinda hawayen kan fuskarsa suke sake gudun tsere idanunsa babu kyan gani saboda yanda suka koma

SHAREEF ya rikice ganin halin da É—an uwansa yake ciki, da sauri ya furta, "Hanif, mene ne haka kuma? Kukan mai kake yi a nan?"

Kukan ne ya so kufce masa, amma sai ya dage ya tamke bakinsa yana mai lumshe idanunsa tare da ƙoƙarin saisaita numfashinsa

Hankalin SHAREEF a tashe yake dubansa, ya kamo hannunsa duk ransa a jagule cike da tausayinsa yace, "don Allah ka kwantar da hankalinka Hanif, babu abun da zai same ta fa, aiki za a yi mata kuma lafiya lau zata fito da ikon Allah, idan ka shiga wannan wannan yanayin; baka san halin da su Momy zasu shiga ba suma, lafiya lau za a fito da ita Insha Allahu. Just prayer for her."

Idanunsa ya buɗe yana kallonsa, amma sai dai har yanzu hawayen cikin eyes ɗin sa basu bar zuba ba, a tsorace yake a yanzu, a jikinsa yana jin kamar zai rasa Amra ne, don haka ya miƙa masa takardan yana mai faɗin, "ka ga fa abun da tabar min, taya ya hankalina zai kwanta bayan ta bar min wasiyya? ji nake yi kamar baza a fito min da ita a raye ba."

Amsar takardan SHAREEF yayi ya soma karanta wa

Ko kafin ya ƙarisa sai ga Likitan ya fito sun ji hayaniyar su Momy da ke tambayar Likitan,
Da sauri suka tashi suma suna matsa wa inda suke domin jin halin da ake ciki

Innalillahi wa'inna ilaihi taji'un! Tabbas Allah yayi alƙawarin kowa sai ya ɗanɗana mutuwa, before a yi wa Amra aikin ne sai ga haihuwar ta zo mata gadan-gadan, dayake rabo ne kuma shi Allah shi ke fitar da mai rai a jikin matacce, kafin mintina biyu kacal Amra ta fitar da abun da ke cikinta, kuma kamar ƙiftawar ido ko kafin ta buɗe idanu ta san inda kanta yake; Allah ya amshi abun sa

Innalillahi wa'inna ilaihi taji'un! Rai baƙon duniya, tabbas bazan iya misalta muku halin da mutanen nan suka shiga ba,
Amma nan take Hanif ya zube ƙasa yana fitar da wani irin numfashi mai wahala, kuka yake yi wanda ya sarƙe shi nan take ya sume a wajen

Mamanta ma zube wa tayi ta sume gau a wurin, har Afra,
Yayinda Salma ta rusa uban ihu tana kiran sunan Æ´ar uwanta

Ihun ta da Salatin su Momy shi ya jawo hankalin jama'ar asibitin, kowa ya san babu lafiya a wurin

Allah Sarki! Rai baƙon duniya,
Tabbas makusantan ta sun ji mutuwar Amra ba kaÉ—an ba a wannan ranan, kowa kuka yake yi sabida rasa ta da kuma tsoron Allan da ya mamaye su

Su Mama sun farfaÉ—o amma Hanif bai farfaÉ—o ba har aka haÉ—a gawan a asibitin aka bayar za a tafi da ita gida,
Ikon Allah kuma Jaririn lafiya lau yana nan cikin ƙoshin lafiya sai tsala kuka yake yi yana neman abincinsa yana lashe baki,
Ƙarshe dai a asibitin Likitan ta rubuta musu madaran da za a iya ba shi, tun a nan aka nemo aka fara ba shi ya soma sha

Rai baƙon duniya, kowa yayi ɗammara don duniya to ya kwance, duk wanda ya zo zai tafi, mutuwa rigan kowa, babu wanda ya fi ƙarfin saka ta, basu da yanda zasu yi duk son da suke mata Allah ya karɓi abun sa, sai haƙuri, hakurin shi zasu runguma

Ƙarshe dai halin da Hanif ya shiga a asibitin ya kwana don ya kasa tashi bare a je a yi jana'izar da shi, kuka ya dinga yi kamar ƙaramin Yaro, duk hakurin da ake ba shi abun ya cutura,
Tunda Amra bata kwana ba tun a ranan aka rufe ta

Maryamu bata da labari tunda mutanen gidan babu wanda ya dawo sai can dare suka dawo, SHAREEF kuma sai dai ya kwana a wurin Hanif, shi yake tausan sa yana ba shi haƙuri,
To lokacin tayi barci bata san da dawowarsu ba, kuma ta sha kiran SHAREEF but bai sanar mata ba ya ɓoye mata saboda ganin halin da take ciki itama,
Kamar kuwa ya san zata shiga wani halin, tunda a washe garin ranan ta ji Momy tana waya tana sanar da wasu daga cikin Æ´an uwanta da basu sani ba,
Ai a take ta É—aga hankalin ta, bare dama tana da ciki itama haihuwa ko yau ko gobe, Allah Sarki! Sai jikinta ya rikice ta faÉ—i a nan tana kiran Cikinta

Momy fa hankalin ta ya tashi, da gudu ta rugo wajenta tana kiran sunanta , tana tambayarta mene ne? Sai kuma ta koma kiran sunan Dady tunda bai rigada ya fita zaman makoki ba, kasancewar a can gidan su Amran ake yi

Kiran da take mishi ne ya fito da Dady ya zo ya tarar da abun da ke faruwa, wani sabon tashin hankalin kuma,
Ai babu ɓata lokaci suka wuce da ita asibiti,
Amma a cikin su babu wanda ya faÉ—a ma SHAREEF sabida kar hankalin sa ya kara tashi, ana wata ga wata, itama ga Maryamu cikin wani hali, asibiti É—aya kuma suke amma basu neme sa ba, don su kansu a halin da suke ciki tashin hankalin su bazai iya misaltuwa ba

Momy har da hawayenta tana cewa, "innalillahi wa'inna ilaihi taji'un! Ya Allah ka tashi kafaÉ—an baiwar nan naka, kar kuma a maimata wani tashin hankalin, ya Allah ka sauke ta lafiya."

Dady ya amsa yana cewa, "ki zauna don Allah a nan, addu'ar mu kawai take bukata, Allah zai bata lafiya. Zauna a nan kar ki faÉ—i."

Zama tayi, shi kuma yana tsaye yana ta zagaye

Kusan mintina talatin Likitan ya fito a ruÉ—e, wani abun mamakin sam sun nemi cikin Maryamu sun rasa, ita dai bata a cikin hayyacinta ta sume, amma kuma da suka duba cikin ko haihuwar ne, an yi scanning babu ciki amma ga tulelen cikin, abun ya É—aure musu kai, kuma duk abun da zasu yi don su ga cikin but babu shi,
Ikon Allah kenan!

Bayanin da Likitan ya yi musu su kansu sun ruɗe, ba ƙaramin tayar musu da hankali yayi ba, amma duba da halin da take ciki na fama da aljanu sun san bazai wuce aikin su bane, innalillahi... Kenan har yanzu dai suna a tare da ita basu barta ba? Duk maganin da ake mata? Wannan wanne irin bala'i ne?

Haka dai aka kira Malam tunda dai sun san bazai wuce wannan matsalar nata bane, bayan an kira shi aka sanar da SHAREEF shima,
A lokacin ma Hanif jikin nasa da ɗan sauki amma har yanzu ba ya iya magana sai dai shiru yana faman tunani sai hawaye, ana ta mishi ƙarin ruwa don jininsa ne yayi mugun hawa, kuma bazai iya tafiya ba koda ya nemi a sallame shi ya koma gida

Likita yace, "dole ya zauna na É—an wanin lokacin tukunna."

Sai ga shi kuma an kawo Maryamu asibitin,
Itama Maryamun ta farka tana ta kuka sabida mutuwar Amran ya taɓa ta, abun ya bata tsoro musamman ganin itama tana da cikin, ta yiwu itama mutuwar zata yi, shiyasa hankalin ta ya tashi tana ta cewa, "a kira mata Iyayenta da Mijinta su gana, wataƙil mutuwa zata yi itama."
Ta gaza kwantar da hankalinta duk yanda aka so a rarrashe ta

Sai da SHAREEF ya zo ne sannan ta rungume shi ƙam tana kuka sosai da sambatu, abun gunun tausayi, don ma wai bata san halin da take ciki bane,
Sai da Malam ya zo tukunna take jin abun da ke faruwa da ita, ai nan ta sake ɓarkewa da wani sabon kukan, ita kuma nata jarabtar kenan, daga wannan sai wanann

SHAREEF ke ta faman rarrashinta yana faÉ—a mata, "babu abun da zai faru da ita da babynsu, za a nemo musu cikinsu."
Shi kansa maganar yake yi kamar zai yi kuka don tashin hankali da rashin natsuwar zuciya

Malam yayi musu bayanin, "sau da dama ana samun hakan, yawanci Aljanu ne suke sace cikin Mace sai a nema a rasa, wasu sai ya girma ta zo haihuwa sai a ga babu cikin, wasu kuma tun bai gama girma ba daga nan ya sha ruwa kenan, wasu kuma asiri ne ake musu hakan ke faruwa, amma Insha Allahu zai basu taimako da ikon Allah cikin zai dawo, tunda ya sha samun cases É—in nan a kwanakin nan, don haka kawai a mayar da ita gida zai fi."
Chapter 74 · 0% Book details