← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 75

Sashe 41

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi kuma jikinsa yayi sanyi idanunsa sun sake kaɗa wa domin har lokacin hawayen ciki basu dena zuba ba, tabbas a yanzu babu wannan tsana da jin haushin da yake mata, tun lokacin da Hanif ya faɗa mishi cewan ita ta sadaukar da ƙodan ta har aka sanya mishi; daga lokacin ya dena jin tsanarta a ranshi, haƙiƙa a wannan lokacin yana tsananin nadamar abubuwan da ya aikata mata, amma bai san ta yanda zai yi ya gyara ba, shiyasa ya binne abun a ransa har zuwa wannan lokacin abun na cin sa a rai,
Shiru yayi yana jin zuciyarsa tana kai kawo tare da bugawa da ƙarfi, yana sauraron zantukan Hanif da ke ta ba shi shawarwari na tsawon lokaci ya gaza yin shiru,
Bai da kuma wani buri a yanzu da ya wuce ya rabu da soyayyar Haseena ko zai samu salama a ransa,
Yana son ko ya ya ne ya saka soyayyar Maryamu a cikin ransa, duk da a yanzu babu sonta amma babu ƙiyayyarta, tabbas ta cancanci ya so ta ya ajiye komai a gefe

To daga wannan ranan sai SHAREEF ya soma fafutuka domin ya ga ya rabu da Haseena, sabida a yanda yake jin soyayyarta ba ya jin zai iya son wata Mace har ya haÉ—a su wuri É—aya a cikin zuciyarsa, wannan dalilin ne yasa da kansa ya yi wa kansa faÉ—a wurin gyara ibadarsa da Allah,
Ada ba ya zama yayi wata doguwar addu'a don yayi sallah, sallan ma ba ya yin ta a kan lokaci sai idan ya ga dama, amma a kwanakin nan sai ga SHAREEF ya sauya sosai, don shi kansa yana jin baƙin cikin yanda ya kasa manta wa da Haseena, koyaushe soyayyarta ƙaruwa take yi, kamar yanda Hanif ya ba shi shawara ne, idan ya tashi tsaye wurin roƙon Allah Allah zai yaye mishi damuwarsa,
To SHAREEF dai ya soma hankali, har idan yayi Sallah zaka ga ya zauna yana kai kukansa wurin Allah subhanahu wata'ala domin ya yaye masa abun da ke damun sa,
Duk da babu wani canji amma ya soma samun natsuwa ba kamar baya ba da kullum bai da sukuni zuciyarsa tana mishi zafi da ƙunci, amma yanzu yana iya jure komai yana samun sauƙi a zuciya,
Kuma a yanzu ya gama yanke hukuncin amsar zaɓin iyayensa hannu bibbiyu, don yana ji a ransa Maryamu kaɗai ta dace ya zauna da ita ko domin yin ma iyayensa biyayya,
Duk da yanzu Dady bai sake mishi magana ba, amma ya yanke shawarar idan ya neme shi zai sanar musu ya amince da zaɓin su

Lokacin da ya sanar da Hanif ba ƙaramin dad'i ya ji ba, har rungume sa yayi ya taya sa murna yana ta jin dad'i, don bai da buri sama da ya ga SHAREEF ya so Maryamu, to a yanzu ga shi komai yayi sauƙi tunda har da bakin sa ya faɗa masa zai zauna da Maryamu zai bi zaɓin iyayensu.***

Yanzu haka saura sati biyu bikin Hanif É—in,
Kuma lokacin yayi dai-dai da samun hutun su Maryamu,
Don haka koda suka samu Hutu gaba É—aya suka taho Kano biki.

[19/04, 7:18 PM] نفيسة OumƊahira: 🌱🌱🌱🌱🌱

       *SHAREEF*
           _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱

_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*Littafina na kuÉ—i ne, ki biya ki karanta, zaku iya samu na a kan wannan numban wayan. 07065334256.*

__________
*BOOK2*
_______________*PAGE21*
_____SHAREEF sai a wurin Hanif ya ji labarin zuwan su Maryamu, lokacin sun taso daga wurin aiki yake faÉ—a masa isowar su, da nufin ya ji ta bakin sa

Amma SHAREEF bai ce komai ba har suka dawo gida, to bai san mai zai ce ba, amma har zuciyarsa yana jin farin ciki da jin labarin, kawai ya maze ne ya nuna kamar maganar bai dame shi ba, nan kuwa cike yake da son ganin Maryamu wacce yake mamakin taimakon da tayi masa duk da irin tsanar da yake nuna mata

Dukkansu suna zaune a falo ban da Dady da shi ba ya gidan a lokacin,
A tare suka shigo Falon dashi da Hanif da sallama a bakin su

Da gudu Na'ilah ta nufo wurin su tana musu oyoyo, amma lokacin da ta iso wurin su sai ta tsaya kuma tana kallon su ta rasa wurin wanda zata je

Hanif É—aukar ta yayi yana shilla ta sama; cikin farin ciki yake cewa, "Oyoyo My Na'ilah, yau ga Na'ilah a gidan mu."

Sai dariya take yi tana washe baki cikin tsantsan farin cikin É—aukar ta da aka yi, dama abun da take so kenan

While SHAREEF kuma ciki ya nufa idanunsa tuni sun sauka a kan Maryamu

Wacce suke zaune su uku a saman three sitter, Aakifah na tsakiya, ita da Yusaira suna gefe suna taÉ—in su cike da nishaÉ—i,
But ita tunda ta ga shigowar su sai ta kawar da kanta a wurin su bata sake kallon inda suke ba

Aakifah tare da Yusaira suka yi wa SHAREEF sannu da zuwa tare da gaishe shi dukkansu fuska a washe

Ya amsa su shima face É—in sa a sake, before ya nemi wuri ya zauna yana gaishe da Ammee

Ta amsa itama da fara'a tana cewa, "kun ga baƙin bazata, kuna wurin aiki ko huta wa ba kwa yi, har da kai Ango? Maimakon mu tarar da kai a gida wato?"
Ta ƙare maganar tana kallon Hanif da ya iso wurin su ya sauke Na'ilah,
Sai ta nufi wurin SHAREEF ta ƙanƙame shi tana dariya,
"Ammee ina wuni kun zo lafiya?"

"Alhamdulillah Hanif, ya shirye-shirye ya kuma aikin?"

Yana shafa kansa cike da kunya yace, "Alhamdulillah Ammee, ina Abee bai zo ba?"

"Abee ai ba yau ba, sai ranan biki zaka ganshi Insha Allahu don yana gari."

Gaishe shi su Aakifah suka yi

Idanunsa ya mayar kansu, sai kuma ya miƙa musu hannu dukka suka tafa har Maryamu

Tana dariya tace, "kai Yaya wlh har ƙyallin angwanci ka fara. Askin nan ba ƙaramin kyau yayi maka ba. So good my lovely Bro."

Dukka dariya ta basu sabida tayi maganar har tana huro mishi kiss

Shi kansa SHAREEF abun ya burge shi, sai dai ko kaɗan bai nuna a kan fuskarsa ba, amma idanunsa yana a kanta yana ɗan satan kallonta, sosai yake mamakin yanda ta ƙara sauya wa fiye da wancan zuwan da tayi, a sace yake kallonta don kar su Momy su gane, kuma ya kasa tashi ya wuce ɗakin su haka nan ya zauna a wurin yana sauraron hiran nasu da ya kasa saka baki a ciki, abun mamakin yanda ya ji Maryamu take ta zuba ta fi kowa surutu a cikin su, shi dai tunda ya santa bai taɓa ganin tana magana sosai ba, zai iya cewa bai gama sanin muryanta ba ma, bai san cewa tana da surutu har haka ba sai yau da dalili yasa shi zama yana sauraron ta, dalili kuwa na rashin jin tsanar ta da yake yi a yanzu wanda yasa har burge sa ta fara yi, ya santa da shegen kallo kamar zata cinye Mutum, amma abun mamakin yau yana son su haɗa ido but ko kallon inda yake bata yi ba, in fact ma ko gaishe shi bata yi ba, hakan ba ƙamarin tsaya mishi a rai yayi ba,
Ya kasa tashi bare yabar wurin, yana zaune yana sauraron su, Na'ilah na jikinsa yana mata wasa ya miƙa mata wayansa suna danna wa a tare, babu wanda zai yi tunanin hankalin sa yana a wurin ma

Har aka kira sallan Magriba suna a wurin suna ta hira, sannan suka tashi sabida yin Sallah

Sai a lokacin SHAREEF ya samu ya wuce É—akinsu ya bi bayan Hanif da shima tuni ya shige,
Bayan sun yi alwala suka fita sallah,
Lokacin Dady shima ya dawo shima tare da shi suka tafi masallacin

After sun dawo suka zauna a falo gaba É—ayansu har su Ammee da suka fito sun idar da nasu sallan

Momy kuma ta shiga kichen ita da Maryamu da ta bi bayan ta; don ta taya ta ƙarisa haɗa abincin da suka gama, ba don komai ba don kar ta zauna wurin da SHAREEF yake shiyasa ta nufi wurin Momy tana taya ta kwashe abincin,
Bayan ta zuba a coolers sai ta kwaso takai saman dining, Momy tabar mata sauran aikin ta ƙarisa sannan ta zo ta zauna cikin su

Dady yace, "My daughter taho nan kusa dani ki zauna, nayi kewar ki sosai fa, mun yi magana da su Innan ki ma, suna kan hanya zasu zo bikin suma."

"Don Allah Dady da gaske?" TafaÉ—a cikin farin ciki tana nufan sa

Dariya suka yi,
Dady shi kuma yana ƙara bata tabbacin hakan, "suna kan hanya Insha Allahu haka Babanku yace min, dukkan su zasu zo."

Sosai Maryamu tayi farin ciki, don ta kasa ɓoye hakan a kan fuskarta,
Sai kuma tace, "Dady amma in sun zo zan bi su kawai mu tafi tare, sai in yi hutuna a can."

"Duk yadda kike so my daughter bazan hana ki ba.
Deeja, a kawo mana abincin mu nan mu ci ko, don zai fi dad'i a nan É—in babu takura."

"To." Momy ta amsa mishi tana shirin tashi

Sai Ammee tace mata, "ta zauna, su bari su kwaso." Kallon su Aakifah tayi tace, "ku tashi ku je ku kwaso abincin ku kawo nan."

Umarnin ta suka bi zuwa wurin dining É—in, suka kwaso abincin, ita kuma Maryamu ta É—auko abun shimfida wa; aka shimfiÉ—a a wurin,
Ammee da Momy suka yi save din su

While SHAREEF ne kaÉ—ai ya nuna bazai ci ba, ya fi son tea

Ammee ta dubi Maryamu tace, "Maryam, haÉ—a masa tea mana, sai ki kawo masa."

Sai lokacin Maryamu ta kalli inda yake, a karon farko suka haɗa ido dashi, ganin yanda idanuwanta suka shige cikin nasa shiyasa ta haɗe fuska tana miƙe wa ta wuce zuwa kichen, a ranta tana jin haushin saka ta aikin da aka yi

Shi kuma ganin haka sai ya mike da wayansa a hannu kamar yana waya ya wuce zuwa É—akin sa
Chapter 41 · 0% Book details