Sashe 24
Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gaba É—ayansu ta faÉ—ar musu da gaba, musamman ma Haseena da zuciyarta ke faman buga wa tana tsaye babu riga a jikinta sabida tashin hankali, bata tsaya sauraron abun da Umma take faÉ—a ba sai ta sauka da gudu ta nufi hanyar da take nuna musu,
Ko kafin takai ta jiyo Umman su tana faÉ—in,
"Haajara tana kichen ba ta motsi, jini na zuban mata..."
Ai da gudu ta sha kwanan kichen É—in tana ruga wa a guje ta shige ciki, tana ganin Haajara a zube ga jini na kwance a saman tayes É—in, take ta daddaro idanu waje tana rufe bakin ta cikin tsaninanin kiÉ—ima
A lokacin shima Abba ya taho a guje; Umma na mara masa baya,
Gaba É—ayansu suka nufe ta suna kwaÉ—a mata kira zuciyarsu kamar zata buga don tashin hankali
Umma sai kuka take yi tana girgiza ta,
"Alhaji wlh bata motsi. innalillahi..! Ta mutu, Alhaji mu taimaka mata mu kaita asibiti jini na zuban mata."
Maganar take yi cikin fitan hayyaci tana girgiza Haajaran
Shi kansa Abba yanda jikinsa ke rawa kamar mazari ya kasa É—aukan ta ma,
Sai Umma da ta tallabo mishi ita suka É—aga ta zasu fitar da ita
Haseena na tsaye kamar gunki har suka fitar da ita, da sauri ta taka ta fita ta bi bayansu tana sakin wani uban ihu mai ƙara, yanda ta fita hayyacinta sam ta manta a yanda take babu riga sai bra
Su kansu su Umma basu ankare da ita ba har suka shigar da Haajaran cikin motan,
Ma'aikatan gidan duk sun taho wurin hankali a tashe sabida jin ihun Jama'ar gidan, ga yanda aka taho da Haajara na ta zuban jini har yanzu ta bakin ta da hancin ta
Ganin sun shige gaba ɗaya zasu tafi, ga Haseena a haka babu ɗankwali bare riga; babu mai takalma cikin su, sai sharɓan kuka take yi
ÆŠaya daga cikin mai aikin su tayi saurin cewa, "Ma'am, babu riga a jikinki fa, bari in dauko miki rigan."
Tafada da sauri tana juyawa da gudu ta koma cikin gidan
Su kansu sai lokacin suka kula da ita,
Umma tace, "ta sauka kar ta ɓata musu lokaci."
Amma furr Haseena ta ƙi fita tana ta kuka ta haɗa gumi domin ita kaɗai ta san abun da ke damun ta, tabbas tana da tabbacin ƙungiyar su ne suka shanye wa Haajara jini tunda ta ga halin da take ciki
Sai da suka jira mai aikin ta kawo mata doguwar riga before Abba ya ja suka fita, direct sai asibiti
Abun da basu sani ba, ko kafin su isa rai yayi halin sa,
Koda Likitoci suka amshe ta sun shiga sun duba ta but sun gane babu rai a jikinta, har gwaje-gwaje sun yi domin gane abun da yasa take blending amma basu gano komai ba,
Dole yasa suka fito suka sanar da Iyayenta,
Take Umma da Haseena suka yanke jiki suka faÉ—i, sai dai aka É—auke su zuwa dakin emergency don duba halin da suke ciki.
*****
_____After Isha prayer kamar yanda SHAREEF yace ma Haseena zai zo, yana dawowa sallah bai tsaya cin abinci ba ya je yayi wanka ya kimtsa ya dauki wanka cikin ƙananan kaya da suka yi masa kyau, sai tashin ƙamshi yake yi zuciyarsa farin ƙal da farin cikin ganin abar ƙaunarsa,
Har ya gama yana É—aura agogo a hand right din sa,
Sai ga Hanif ya shigo É—akin yana waya,
ÆŠago kai yayi ya dube sa sabida jin yana ambaton sunan Mahmud,
Fahimtar abun da suke tattaunawa a kai ne yasa ya mayar da hankalinsa kacokan a kansa, har ya gama É—aura agogon before ya dawo wurin sa ya tsaya; hannayensa zube a aljihun wandon sa ya tsira masa ido yana kallonsa
Sai da Hanif É—in ya gama wayan before ya dube sa shima yace, "Finally Mahmud ya gama aikin sa, domin yanzu haka ya samo inda za a ga Mutumin, yanzu ya rage aikin mu sai mu san ya za a yi."
Hannu ya tafa ya furta, "Wow!"
Face É—in sa É—auke da murmushi wanda har dimples É—in sa sun bayyana,
Cike da farin cikin jin zancen yace, "very good. I enjoyed this talks Hanif, yanzu ka kira Mahmud ya san yanda za a yi ya samo mutanen da zasu kama mana shi, and ya san inda zai ajiye mana shi zuwa gobe mu fara aikin mu. Now I don't have time, idan na dawo zamu ci gaba da magana."
Ya ƙare maganar da duba wrist watch din sa
Hanif yace, "but you didn't tell me where you are going?"
"Zan je wurin sweetheart ne yau ta dawo."
"Oh! Haka, I forgot Haajara ta sanar min fa."
Sai ya taɓe baki yana miƙe wa da faɗin, "to sai ka dawo, a kula da kai."
Kallonsa SHAREEF yayi, sai dai bai ce komai ba ya juya ya É—auki wayansa da ke saman dressing mirror,
Suka fita a tare but shi ya bi ta benen da zai sada shi da ƙofan baya ya fice a gidan,
While Hanif kuma ya wuce Falo
After ya isa gidan, a bakin gate yayi packing tare da yin horn, sai kuma ya bude murfin motan yana sako da ƙafarsa ɗaya waje, yayinda ya ɗauki phone din sa ya soma latsawa yana nemo numban Haseena, kira yayi tana ring but ba a yi peaking ba, almost 3times yana kira before ya dakata, ya ɗaura hannunsa a sitiyarin motan ya ƙara danna horn da ƙarfi har sau biyu
A time ɗin ne Mai gadi ya leƙo domin ya ga wane ne, don a tunanin shi masu gidan ne suka dawo, sai dai saɓanin haka; motan SHAREEF ya gani a fake,
Da sauri ya fito ya nufi wurin sa yana duƙa wa har ƙasa ya soma gaishe shi
A daƙile SHAREEF ya amsa ba tare da ya kalle sa ba, wanda a lokacin ya ƙara kiran numban Haseenan ne ko zai samu,
Sai ya tsinkayi muryan Mai gadi yana faÉ—a masa abun da ke faruwa,
Da sauri ya juya yana kallonsa, hankalin sa ya É—an tashi ko da jin yanayin yanda yake tambayar mai gadin, "tun yaushe hakan ta faru?"
"Sun yi awa É—aya da tafiya Alhaji."
Bai tsaya sauraron sa ba ya shigar da ƙafarsa tare da ɓame murfin motan, ya tayar da sauri yayi gaba ya je yayi reverse before ya wuce da gudu, although ya san asibitin da suke zuwa that's why ya wuce can kansa tsaye
Ko lokacin da ya je Æ´an uwan su Abba har sun cika asibitin don sun san me ke faruwa,
Lokacin Umma ta farfaÉ—o suna koke-koke
Haseena ce ke can É—aki har time É—in bata farka ba,
Tana can cikin ƙungiyarsu hankalinta a tashe da ta tabbatar da cewa jinin ƙanwarta aka sha,
Sai dai basu bata damar yin magana ba sabida yanda Ogansu ya fusata da ita,
Sai dai yayi mata uzuri ne sabida ganin har yanzu bata cika ƙai'dojin ƙungiya ba, sabida sau tari hakan na faruwa wasu tsoro yana saka wa su fita ko su yi ƙoƙarin tona musu asiri, sai dai da zaran sun fara shayar da shi jinin ɗan uwansa to sun gama da wannan babin, wannan shi ne babban sirrin su da suke ƙara kangarewa idanunsu ya buɗe tsoro ya fita a ransu,
Dalilin da yasa bayan sun gama tsafe-tsafen su; Haseena aka fara ba jinin ta shanye shi dolen ta,
Tun daga nan kuma kanta ya soma juyawa ɓacin ran da ke tare da ita ya soma gushe wa, take ta manta da wani tunanin jinin ƴar uwanta da aka sha, zuciyarta ta ƙeƙashe tana jin komai zata iya yi don jin daɗin ƙungiyar su, bata da wata matsala yanzu,
Ko daga yadda ta bada haÉ—in kai suka gudanar da meeting tuni sun san sun gama da ita, don haka sun san baza ta sake basu wata matsala ba
Sai da suka gama meeting din sannan ta farka a cikin wani yanayi, idanunta sun kaÉ—a sun yi jazur kamar jini ya taru a cikin su
SHAREEF yana É—akin da aka kwantar da ita, don tunda ya san halin da take ciki hankalinsa ya fi na kowa tashi,
A lokacin ma tuni an wuce da gawan Haajara; sai shi SHAREEF É—in da ya zauna wurin Haseena yana jiran ta farka,
Yana ganin ta buɗe ido ya riƙo hannunta yana kiran sunanta,
Amma ganin yanda idanunta suka canza launi hankalinsa yayi mugun tashi; cus a tunanin sa duk sabida rashin Æ´ar uwanta ne ta shiga wannan halin
Ita kuma a wannan lokacin babu wani raɗaɗin rasa ƴar uwanta, don haka ta miƙe zaune tana kallon ɗakin da take, before ta sake kallonsa tace, "dear, me nake yi a nan ne?"
Hannunta ya kama cikin kwantar da murya yace, "tun ɗazu kika fita hayyacinki ba ki farka ba sai yanzu, hankalina ya tashi sosai I thought I'd lose you, please sweetheart ki ɗauki ƙaddara kinji? Mutuwa na kan kowa; kowa zai mutu, Allah ya bamu hakuri da juriya."
Shiru tayi tana É—an tunani, sai kuma tace, "ina su Umma?"
"Sun tafi gida gaba É—aya yanzu, bari in kira likita sai ya duba ki ina zuwa."
Ya furta hakan yana sakin ta before ya juya in quickly ya fice
Tana nan zaune bata motsa ba sabida yanayin da take ji babu daÉ—i a jikinta, sai faman lumshe idanu take yi kamar wata wacce ta sha maganin barci, idanunta a hankali suka soma washe wa tun buÉ—e idanun da tayi
Likita na zuwa ya duba ta yana tambayar inda ke mata ciwo a halin yanzu?
Sai ta nuna, "babu komai, gida zata wuce."
Ganin haka ne yasa Likitan ya sallame su suka fita waje tare da SHAREEF, a motan sa suka wuce zuwa gidan su,
Wanda tuni ya cika maƙil da jama'a duk da dare ne,
Kuma a halin yanzu an bar gawan sai zuwa gobe za a yi jana'izar ta,
Sai koke-koke ake yi gunun ban tausayi
Yayinda Haseena kuwa ko hawaye basu ƙara fita a cikin idanunta ba, babu wanda ma yake gane halin da take ciki tunda dare ne, tana zaune ne kawai cikin ƴan uwa tayi shiru ba ta cewa komai.
***