← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 75

Sashe 42

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Koda ta kawo tea ɗin babu shi, baƙin cikin yanda Ammee tace mata, "takai mishi yana ɗaki."
Kamar ta kurma ihu, amma sai ta juya ta wuce saman zuwa dakin nasu, ko sallama bata yi ba ta zura kanta ciki fuskarta a haÉ—e babu fara'a,
Ganin sa tayi zaune a kan sofa yana faman latsa wayansa,
Wurin sa ta nufa ta ajiye mishi a saman Centre table tana ƙoƙarin juya wa,
Sai jin murynsa tayi ya tsayar da ita, kamar kar ta tsaya, sai kuma ta ja ta tsaya tana juya wa da duban sa, ido cikin ido suke kallon juna babu tsoro ko shakkar sa a tare da ita, don a yanzu yadda take jin muguwar tsanar sa komai zata iya faɗa mishi babu kunya bare tsoro, har da wani kama ƙugu tana karkaɗa jiki da jiran abun da zai faɗa mata

Shi kuma dayake bai da bakin magana, bai ma san mai zai ce mata ba, kawai dai ya dakatar da ita ne don ya ci gaba da kallonta yana ƙare wa halittar jikinta kallo, wanda ba ƙaramin tafiya dashi tayi ba da shigan da tayi,
Atamfar da ta sanya yayi mata kyau ainun, riga da skirt ɗinkin wanda yayi mata cif kamar an zana a jikinta, dayake farar atamfa ce da ratsin orange colour kuma ɗinkin zamani, sannan tayi ɗaurin ture kaga tsiya, skirt din ya fitar mata da shape ɗin ta hips ɗin ta ya bayyana gunun ban sha'awa, face ɗinta tayi fresh sosai babu ko ɗigon tabo a kan fuskarta, sai idan tayi magana dimples ɗin ta su ƙara bayyana tsantsan kyawun ta, a wannan karon shi dai gani yake yi bai taɓa ganin bak'ar fatan da tayi wa wata Mace kyau irin Maryamu ba, very smooth and fresh haka skin ɗin ta yake glow da ɗaukar ido sabida sauyin yanayi da hutun da ta samu, ga manyan idanuwanta gulu-gulu da suka ƙara mata sihirtaccen kyau, sai yanzu yake ganin ainihin kyawun ta da ya kasa fahimta; sai yanzu da babu tsanar ta a zuciyarsa, tabbas ya yarda da maganar Hanif da yace, "there are different between Haseena and her."

Ita kuma ganin ya zuba mata idanu yana ƙare mata kallo babu kunya babu tsoron Allah, hakan ne ya bata haushi ta watsa mishi kallo tare da juya wa ta fice a ɗakin bata sake waige ba

While SHAREEF kamar ta tafi da farin cikin sa, jiki a sanyaye ya ɗauki cup ɗin ya soma shan tea yana faman tunano ta a zuciya, musamman surar jikinta da ya fi tsaya mishi a rai, Allah ya bata ƙira mai kyau, a fuskar duk wanda ya ganta, sam babu ƙiyayyarta a ransa yanzu, sannan kuma babu soyayyarta sabida har yanzu yana jin kamar Haseena kaɗai zai so a duniya, duk da a yanzu soyayyar da yake mata ba kamar da ba, haƙiƙa ya ga sauyi sosai da yake dagewa wajen addu'a, yana roƙon Allah ya rage masa soyayyarta, ga shi yanzu kusan sati biyu kenan rabon su da waya, kuma bai damu kamar baya ba, kamar yanda ta share shi shima yana ƙoƙarin share ta, idan da hali bai ƙi Allah ya musanya mishi da soyayyar Maryamu a cikin zuciyarsa ba, domin a yanzu bai da masoyiya mai ƙaunarsa kamar ta, tayi abun da ba kowa zai yi masa ba, a kullum yana dana-sanin abubuwan da yayi mata, har yana jin zai iya faɗuwa a gabanta domin neman yafiyar ta, tabbas ya yarda ya amshi failed in dai a kanta ne, duk wani cika baki a baya da yayi a yanzu yana dana-sani, musamman yanzu da yake ganin kamar babu shi a gabanta, amma yana ji a ransa har yanzu tana sonshi, kawai ta ɓoye hakan ne domin ta ƙuntata mishi, sai yayi murmushi a fili ya furta, "bakin da ya furta so, har abada bazai taɓa furta ƙiyayya ba, a yanzu na shirya tsab domin kasancewa da ke, kuma dole zan sanar da Dady haka, babu amfanin ci gaba da wannan damuwar, bayan ga ki ina kallo a cikin idanuwana kin haɗa komai inda zan samu biyan buƙata."
Sai ya rufe idanuwansa yana jan numfashi mai ƙarfi, "ina matuƙar sha'awarki Maryam, kin soma burge Ni a halin yanzu."

Yana nan zaune yana sambatun sa da tunanin banza da hofi, Hanif ya zo ya kira sa a kan Dady na kiran sa,
Tare suka koma suka sami Dadyn zaune a falo shi kaÉ—ai,
Dayake dare ya É—an ja kowa ya tafi ya kwanta

Shima Dady don yayi magana da su ne shiyasa ya zauna, a kan maganar auren SHAREEF É—in, yace masa, "wanne hukunci ya yanke? Ya samo wacce zai aura ne ko zai zauna da Maryam É—in?"

Babu musu SHAREEF ya nuna amincewar sa a kan zama da Maryamun

Shi kansa Dady yayi mamakin jin furucin sa, sai da ya ƙara maimata masa yace, "ka ce zaka zauna da ita? Ka amince a baka Matarka?"

SHAREEF ya sake amsa mishi tare da neman afuwan sa a kan rashin musu biyayya da bai yi ba tun farko, yace, "Dady don Allah kayi hakuri, amma a yanzu a shirye nake da in muku biyayya na amshi zaɓin ku, kawai a haɗa auren mu tare da Hanif itama ta tare, ina buƙatar Matana."

Ba ƙaramin dad'i ne ya cika Dady ba, lallai ya yarda SHAREEF ya soma hankali, domin wannan maganar ya faranta masa rai matuƙa, yace, "shikenan Insha Allahu babu damuwa za a haɗa bikin kamar yanda ka buƙata, zuwa ranan asabar ɗin za a haɗa bikinku gaba ɗaya, ka ga yanzu sai ka zaɓi gidan da zaku zauna tunda shi Hanif ɗan uwanka ya zaɓa nasa, inyaso gobe a je a fara gyara a duba duk abun da babu, Allah ya yi muku albarka gaba ɗaya, ku je zan yi magana da Momyn naku, abun da muka yanke gobe zan sake tuntuɓan ku."
Daga nan ya sallame su suka tafi,
Bayan sun tafi shi kuma ya saka waya ya kira Momy yace, "ta zo tare da Surayya akwai maganar da zasu yi."
After sun zo ya zayyane musu komai abun da SHAREEF ya faÉ—a

Dukkansu sun yi farin ciki kuma sun yi mamakin lokaci guda da ya nuna zai zauna da Maryamu, abun da suke fata kenan amma ga shi lokaci ɗaya Allah ya amshi roƙon su

Sai dai Momy ta ƙi goyon bayan tariyan Maryamun, tunda a cewar ta, "gaskiya bai kamata a daƙile mata karatun ta ba bayan ta kusa kammala wa, kawai yayi hakuri ta ƙarisa."

Dady yace, "a'a, ai kuma bazai yiwu ba, kin san dai yanda muka yi fama da Yaron nan tun a baya bai amince ba sai a yanzu, tunda yana son Matarsa ai kuwa bazai yiwu mu hana sa ba, bare kin san halin da yake ciki ba tun yau ba, da irin ciwukan da yake fama da shi duk dalilin rashin Mata, yanzu kuma ya gane Annabi ya faku ya yi wa kansa faÉ—a kuma mu ce zamu hana sa? a'a, Insha Allahu Matarsa zata tare a wannan lokacin babu ja da baya, karatunta kuma tunda SS 3 zasu shiga ba sai ta koma ba; idan an zo zana jarabawar fita zata iya zana wa ko a nan ne, shikenan hakan ya fi."

Ammee tace, "gaskiya ne Yaya, nima na goyi bayan ka, kawai ta zana jarabawar fita ba sai ta koma makarantar ba, ai abun farin ciki ne wannan."

"To shiyasa na kira ku muyi shawara gaba É—aya, don haka zan sanar da Iyayenta don su san da maganar tariyan Æ´arsu, inyaso gaba É—aya Æ´an uwanta sai su taho a yi bikin da su Ni zan É—auki nauyin zuwan nasu da komawar nasu, itama Maryam Ni zan faÉ—a mata zan zaunar da ita in fahimtar da ita."

Duk sun yi na'am da maganar Dadyn, don haka babu wanda ya ja zancen, bayan sun gama tattauanawa suka wuce suka kwanta.

A kwana biyu kuma gidan ya kuma cika ƴan uwan Momy duk sun cika gidan tsaki da ƙwarƙwatan su, dama ba baya ba wurin yawa Ahalin su, bare gidan maiƙo ne babu wanda ya haƙura sai ana gobe biki ko ranan biki, haka suka zo suka cika gidan tun a ranan aka fara hidima da su, komai na biki da ciman da za a ci an fara tanadar wa ana ta aiki a kai

The following day kuma sai ga Æ´an uwan Dady suma sun zo tsaki da kwarkwatan su, su Aunty Ummita, su Bashir, Matan su Yaya Faisal gaba É—aya sun tarkato har Yaransu, tunda a kyauta aka taho da su, har can Dady ya aika da Mota yace, "duk wanda zai zo ya zo bai É—auke wa kowa ba." Tunda ma ya faÉ—a musu har da tariyan Maryamu, shiyasa suka taho dukkansu, har da Bintu da su Umma Jummai, Innan su Maryamu ma ta biyo su duk da a baya ta nuna baza ta je ba; dalilin sanar musu da aka yi da tarewan Maryamu, amma Dady yace, "ta zo don Allah."

Iya Samira ce kaɗai bata zo ba sabida ciwon ƙafa da ya matsa mata, sakamakon hawan jinin ta da ya ɗan tashi a kwanakin, amma zata biyo su Baba in zasu zo a ranan bikin; su da su Yaya Ashiru, su a ranan bikin zasu zo

Zuwa sakaliyar la'asar sai ga su sun fantsamo gidan, gida fa ya ƙara cika maƙil

A lokacin babu su Aunty Fatima suna can sun je zaɓo wa Maryamu kayan daki, tunda abun ya zo a ƙurarren lokaci,
Na Amra kaÉ—ai aka yi tunda Dady ne yayi mata komai, an shirya mata gidan ta tamkar na Æ´ar gata,
Yau kuma aka tafi siyo na Maryamu wacce har wannan lokacin bata san da labarin da ita za a tare ba, za a miƙa ta gidan SHAREEF masoyinta, buri ya cika, sai kwanya ta faɗa. 😳😂💃💃💃
[20/04, 7:17 PM] نفيسة OumƊahira: 🌱🌱🌱🌱🌱

       *SHAREEF*
           _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱

_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*Littafina na kuÉ—i ne, ki biya ki karanta, zaku iya samu na a kan wannan numban wayan. 07065334256.*
Chapter 42 · 0% Book details