← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 75

Sashe 6

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

he is sitting on his chair facing her, idanu ya zuba mata yana kallonta har ta zo ciki ta zauna a kan kujera; bai ɗauke ido a kanta ba sabida ganin yanda ta sauya masa a ɗan kwanaki biyun nan, idan idanuwansa ba ƙarya suka yi masa ba ya ga ta rame sosai kamar tayi ciwo, har siraran laɓɓanta sun bushe gefen bakin da hucewar mura,
Wani iri ya ji a ransa duk da bai tabbatar da cewan ga abun da ke faruwa da ita ba, amma har ransa ya ji damuwa da tausayinta

Ita kanta yanda yake mata wannan kallon; yasa ta kasa cewa komai, illa sauke kai ƙasa da tayi tana mamakin irin kallon ƙurillan da yake mata, hakan ne yasa har gabanta faɗuwa yake yi haka kawai ta ji wani irin yanayi a tattare da ita, wanda yasa ta kasa motsi tunda ta duƙar da kanta

"Amrah." Ya kira sunanta cikin wani yanayi ba tare da ya dena kallonta ba

A hankali ta ɗago kanta ta zuba ƙwayar idanunta cikin nasa, sai dai tuni tayi saurin ɗauke su sabida yanda ta kasa jure irin kallon da yake mata, ta rasa wanne irin yanayi ne ke baƙuntan ta a wannan lokacin

Sake magana yayi a hankali kamar yana tsoron wani ya ji, inda ya taso da jikinsa daga jikin kujeran yana É—aura hannayensa biyu a saman teburin tare da furta, "ciwo kika yi ne haka; na ga kin rame ne kamar kin yi ciwo? What's wrong with you?"
Sai ya janyo Memo da ke gabansa ya haɗa da bairo ya miƙa mata tare da furta, "oya tell me, me ke faruwa ne?"

Hannu tasa ta ɗauki Memon batare da ta ɗago ta kalle sa ba, kamar baza tayi rubutun ba kuma sai ta soma rubuta mishi, "bani da lafiya ne, amma na ji sauƙi."
Bayan ta gama sai ta tura masa gabansa tana kallonsa

Karanta wa yayi yana duban ta, tuni face ɗin sa ta sauya cikin ƙanƙanin lokaci, cike da tausayin ta yake faɗin, "eyya sorry, I didn't know you were sick, da nazo har gida na duba ki, kuma na san kina da numbana meyasa ba ki kira Ni ba?"

Shiru tayi tana duƙar da kanta da barin kallonsa

"Kin yi shiru tell me? Ko dai ma bani da matsayin da za a iya ajiye numbana ne?"
Ya ƙare da ƴar barkwancin sa yana son jin mai zata ce, yayinda ya sanya hannu a aljihu yana ɗauko wayansa ya sake duban ta da faɗin, "kin yi shiru; maganata ta zama gaskiya kenan?"

Murmushi tayi tana girgiza masa kanta alamun a'a

Numban ta ya nemo a wayansa yana miƙa mata tare da cewa, "Ni kinga me nasa a numban ki, sabida matsayin da na ba ki My sister na rubuta."

Kallon wayan tayi tana murmusawa, har zuciyarta ta ji daÉ—in sunan bata san meyasa ba

"Amma ke na san maybe ma ban samu matsayin suna ba, cuz na san haka Mata kuke yi, don haka ina son sanin me aka sa min a sunana?"

Ɗan waro ido tayi tana dariya wadda ya bayyana jerin haƙoranta, sai kuma ta duƙar da kai sabida kallon da yake mata cike da kunya

Shima murmushin yayi har ransa ya ji dadin yanda ta saki jikinta, hakan ne yasa ya ƙara cewa, "ki bani in gani mana, sai kin nuna min fa."

Maƙe kafaɗa tayi da sauri

Shiyasa ya bushe da dariya yana cewa, "ba ki da gaskiya ko?"

Rufe idanunta tayi da hannayenta sabida kunya

Shi kuma sai yayi shiru bai sake cewa komai ba, amma ya kafa mata idanu yana jin wani irin farin ciki a ransa, bai san meyasa yarinyar ta tsaya mishi a rai ba a yanzu yake fama da tunanin ta, ji yake yi kamar su dauwama a haka sabida yanda yake jin nishaÉ—i,
Ɗago kan da tayi suka haɗa ido, sai tayi saurin mayar da kanta, murmushi shi kuma yayi yana cewa, "please don Allah ki bani matsayin ko Yaya ne a zuciyarki, ina son ki taimaka ki bani wannan matsayin, duk sanda ba ki da lafiya irin haka ki yi ƙoƙarin kirana; ko ba komai na san zan iya taimaka miki, ba sai kin zo office ba, i know daga ganin ki ba ki samu sauƙi sosai ba amma kin zo, kar ki sake irin haka kinji?"

Ɗago kai tayi tana duban sa tare da gyaɗa masa kanta cike da girmamawa, ba ƙaramin daɗi ta ji ba da furucin sa

Murmushi yayi mata yana duban agogon hannunsa, sai ya sake kallonta yace, "secretary he not come today, and we have a meeting now, zamu iya tafiya yanzu."

Miƙe wa suka yi a tare, ya soma yin gaba sannan ta bi bayanshi har zuwa hole ɗin da suke taro,
Sai dai a tunanin Hanif zai ga SHAREEF ya zo since ya bar sa a gida ya ƙi biyo sa, amma ga shi bai zo ba, yana can gida ya ɗaura wa kansa damuwar Haseena, shiyasa da ya gaji da lallaɓa sa ya taho abun sa,
Yanzu kuma ga shi zasu yi meeting na amsar wasu sabbin gwangila but bai zo ba,
Ba yanda Hanif ya iya dole suka yi taron,
Sun É—auki kusan awa É—aya before su kammala kowa ya watse suka koma bakin aiki.
[31/03, 4:32 AM] نفيسة OumƊahira: 🌱🌱🌱🌱🌱

         *SHAREEF*
             _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱

_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*Littafina na kuÉ—i ne, ki biya ki karanta, zaku iya samu na a kan wannan numban wayan. 07065334256.*

__________
*BOOK2*
_______________*PAGE4*
_____After Hanif ya tashi, bai bari Amra ta tafi ba yau da kansa yace, "zai kaita domin ya ga gidan su, ko don idan wani abu ya taso."

Da farko ta ƙi amincewa since bata so hakan ba,
Amma da ya matsa mata dole ta yarda ta kasa ci gaba da masa musu, haka ta haÉ—a komai sannan ta É—auki Jakarta ta saka shi a hammata ta bi bayansa zuwa bakin motansa,
Gaba ya bata umarnin ta shiga after ya buÉ—e mata,
Bayan ta shiga ya ja motar suka wuce

Sai da ya fitar da motan ya daidaita ta a kan kwalta, sannan ya tambaye ta inda zai bi

Hannu ta sanya a Jakarta ta ciro address ɗin gidan su ta miƙa masa

Amsa yayi ya duba, ya san sunan anguwan a baki, but bai san a ina ne ba tunda ba wai ya cika yawo bane shi tun usuli,
Don haka yace mata, "bai san hanyar da zai bi ba amma ta riƙa nuna masa koda da hannu ne."

To a haka ne har suka ƙarisa anguwan nasu, ya tsayar da motan a dai-dai lungun gidan su,
After ya dakatar da motan; sai ya zuba mata ido yana kallonta kamar kar ya É—auke ido a kanta

Ita kuma murmushi tayi tare da mishi godiya da hannunta tana shirin buɗe ƙofan ta fice

But tuni ya dakatar da ita wurin furta, "har yanzu ba ki bani wayan naki na gani ba? Please ki bani mu gani."

Kallon fuskarsa tayi, ganin yanda ya kafe ta da kallo shiyasa tayi ƙoƙarin ciro wayan daga cikin Jakarta, zaro Jakar tayi a hammata before ta buɗe ta ciro ƴar ƙaramar wayanta da ta ji jiki ta sauya kamanni, sanadin hakan ne yasa har yanzu take tare da wayan batare da ta siyar ba,
Miƙa masa tayi a kunyace

ya amsa yana duba wa, murmushi kawai yayi a zuciyarsa yana furta, "Allah Sarki! Baiwar Allah, maybe sabida yanayin wayan ne yasa ta ƙi nuna min."
Sai ya É—auki wayansa da ke ajiye ya soma buÉ—e wa, bayan ya buÉ—e ya cire simcards É—in sa tare da buÉ—e nata itama ya ciro

Tana kallo ya sauya layin ciki ya saka nata a babban nashi, bata iya cewa komai ba har sanda ya miƙo mata wayan, amma kuma ta kasa amsa sai ma idanu da ta zuba mishi don bata fahimci mai yake nufi ba

"Karɓi mana, na ba ki ne, ki yi amfani da nawa zai fi miki daɗin aiki, wannan kuma sai ki kyautar."
Ya haɗa da natan ya miƙa mata,
Ganin ta ƙi amsa still shiyasa yayi maganar in serious face

A sanyaye ta saka hannu ta amsa wayoyin, bata da bakin magana shiyasa tayi shiru godiyar ma ta kasa mishi don bata san me zata ce ba

"To zan wuce, but Insha Allah tunda na ga gida wani lokacin zanna riƙa zuwa ina ɗaukar ki kawai; since hanyar mu ɗaya ai, baza ta bani wahala ba zuwan."

Kallonsa tayi suka haÉ—a ido, sai tayi mishi murmushi tare da É—aga hannayenta ta soma mishi godiya

Duk da shi bai fahimci mai take cewa ba amma ya gane kamar godiya ne, yace, "kar ki damu yanzu kin zama Ƙanwata, komai kike so ki yi min magana kanki tsaye, yanzu ki tafi kar a ji ki shiru sai gobe in mun haɗu."

Hannu tasa ta buɗe motan, tana shirin fita ta hango Jabir ya fito lungun gidan nasu yana layi irin tafiyar nan nasa ta mashaya, da sauri ta dakata nan da nan gabanta ya faɗi, sai ta diririce lokaci guda ta mayar da ƙofan ta rufe tana zare idanu

Mamaki ne ya kama Hanif ganin yanda ta ruÉ—e lokaci É—aya, inda take bi da kallo ya bi da idanunsa yana kallon Jabir; da ya zo ya gibta ta wurin Motan bai ganta ba,
Sai kuma ya mayar da kallonsa gare ta ganin yanda take sauke ajiyar zuciya kamar wacce tayi gudun tsere, alamun tsoro ya bayyana a tare da ita, buÉ—e baki yayi yace, "lafiya Amrah? Me ya faru ne?"

Saurin kallonsa tayi a tsorace tana ƙanƙame jikinta, cikin yanayin da babu natsuwa a tare da ita ta soma girgiza mishi kai alamun babu komai, sai kuma ta buɗe kofan ta fice da sauri; ba tare da ta waiwaya ba ta nufi hanyar gidan nasu da ɗan saurin ta, har da haɗawa da gudu
Chapter 6 · 0% Book details