← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 75

Sashe 62

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sabida iya taku shiyasa Haseena ta É—auki Umma da taimakon Nana, suka tafi da ita asibiti,
A can ne Uncle É—in su ya je ya tarar da su,
Ko lokacin Likitoci sun gama binciken su sun gano rai yayi halin sa, tunda tuni ta shura, sai dai basu gane takamaiman abun da ke faruwa da ita ba, kawai dai sun É—aura zargin su a kan jinin da ta zubar ne har hakan yasa ta rasa ranta

Tashin hankali dai ba a sa mishi rana, kowa ya ji mutuwar Umma amma ban da Haseena da ta dinga pretending, tun a ranan Abba ya dawo shi kansa yayi kuka sosai, don mutuwar tayi musu diran mikiya ce basu taɓa tunanin hakan ba, babu zato babu tsammani, ga shi mutuwar iri ɗaya dana Haajara duk yanayin abun da ya kashe su kenan,
Sai dai babu hujja bare a yi zargin wani abu

Har washe gari haka mutane suka yi ta cika gidan, a ranan ma aka yi jana'izar ta,
Yayinda Æ´an uwa da Abokan arziki suka ci gaba da zaman makoki

Gefe É—aya kuwa, Nana da Haseena ba abun da ya shalle su, suna dai iya takun su amma ko'ina tare suke kamar tif da taya,
A yanda Haseena ta tashi hankalinta ta damu da tunanin SHAREEF, ko kusa bata damu da mutuwar Umma ba, don yanzu SHAREEF shi ne burin ta a yanzu, bata da burin da ya wuce su samo kansa ya dawo gare ta

Yadda ta damu shiyasa Nana ta amince mata suka soma daukar mataki, suka fara aiki a kansa.
[04/05, 5:53 PM] نفيسة OumƊahira: 🌱🌱🌱🌱🌱

       *SHAREEF*
           _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱

_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*Littafina na kuÉ—i ne, ki biya ki karanta, zaku iya samu na a kan wannan numban wayan. 07065334256.*

__________
*BOOK2*
_______________*PAGE32*
_____Maryamu tsab ta warke sabida kulawar da take samu a wurin SHAREEF, kulawar da bata taɓa tunanin samu ba, dama har da sabon al'amarin da ya gudana a tsakanin su ne, ga kuma abun da ya faru a ranan na tsoratan da tayi, dalilin da yasa zazzafan zazzaɓin ya cafke ta kenan, but lokaci ɗaya komai ya sauya sabida samun kulawa da tattali a wurin SHAREEF, ga wani irin soyayya da yake nuna mata mai tsaya wa a rai, takan manta dukkan wani baƙin ciki idan suna tare, a yanzu ba ƙaramin farin ciki take samu ba,
Don shi kansa ya san cewa yayi sabon aure, lokaci guda ya soma jin rayuwarsa ta sauya fiye da tunanin sa, sabida a yanzu yana tare da wacce take matuƙar ƙaunarsa suna ba juna kulawa fiye da tunani, garɗi da madaran soyayyar da suke shayar da junan su, sai suka ji tamkar su dauwama a haka, ko kuma su kaɗai ne a duniyar babu kowa

A yanda SHAREEF yake samun kulawa wurin Maryamu har ya sauya a cikin ƙanƙanin lokaci, don har Kumari yayi ɗan raman nan ya kufce masa, wuni yana liƙe da ita kamar chewing gum ba ya barin ta ta sarara ko na minti ɗaya, a takaice ma ko samun damar yin girki ko wani gyaran gida ba ya barin ta suyi, idan suka ƙule a ɗaki suna manne a saman gado yunwa kaɗai ke fito da su,
To sai a lokacin ne zai ƙoƙarta ya fita da sauri yayi musu take away, wani lokacin ma sai dai su sha tea

A sanda ya fita shine zata samu ta ɗan gyara gidan before ya dawo don ta san bazai barta ta huta ba, abun har ya soma gundiran ta sabida rashin sabo da kuma naci irin na Bawa, sai dai a yadda take ƙaunarsa ba ta iya mishi musu ko kaɗan, duk abun da yace tayi tana masa don ta faranta mishi rai, tana ganin kamar wannan dama ce da ta samu da ba kowacce Mace bace zata samu irin sa, a kullum tana godiya ga Allah da ya mallaka mata farin cikin ruhin ta, don irin farin cikin da take ciki baki ma bazai iya misaltawa ba, kuma a yanda suka samu kusanci hakan zai sa soyayyarta ta ƙara cusuwa a zuciyarsa kamar yanda itama ta mutu a ƙaunarsa

Yau ma suna manne a tare, duk wunin yau babu inda suka fita ko falo, bare dama har yanzu su SHAREEF basu koma hutun da suka É—auka na wurin aiki ba,
Gwara ma Hanif kwana biyu yana leƙa wa da yamma,
Amma SHAREEF tunda ya samu abun da yake so sai ya manta komai, Maryamu kaɗai yake iya gani a idanunsa, ko kaɗan ba ya iya ɗaga mata ƙafa sabida tsaban jaraba da tsananin muradin ta, sai yanzu ya sake tabbar da wautan sa da kuma kuskuren da ya aikata a baya, da tun farko ya yarda da auren ta da tuni komai ya wuce,
Yanda yake jin ta a zuciya ba irin yanda yake jin kowacce Mace a zuciya bace, duk da mutum ɗaya ya taɓa so amma yana jin ya soma shan bamban dana Haseena, tunda ko misƙala zarratan ba ya son ya jirga a kusa da ita, burinsa kawai su kasance a tare su dauwama a haka sabida nishaɗin da yake samu

Amma kuma abun da ke faruwa yanda ya soma jin tunanin Haseena na dawo masa a ransa, har faÉ—uwar gaba yake fama dashi kwata-kwata sai ya ji farin cikin sa na son kufce masa,
Suna kwance a kan gado ya rungume Maryamu a jikinsa, sun rufe jikinsu da blanket

Inda ta ɗaura kanta a saman ƙirjinsa har barci ya soma kwashe ta sabida samun hutun da tayi, shiyasa ta ɗan soma gyangyaɗa wa before ya tayar da ita da jarabar sa,
Har barcin ta ya soma nisa bata ji ya tashe ta ba, sai ta kara gyara kwanciyarta nan da nan barcin ya fizge ta har da É—an munsharin ta

Hakan ne yasa SHAREEF jin tana damunsa kasancewar yanda yake bukatar natsuwar zuciya da tunanin da ya bijiro masa,
Kasa haƙura yayi; sai ya lallaɓa ya janye ta a jikinsa ya sauka daga kan gadon, rigansa ya ɗauka ya zura a jikinsa before ya fita falo yayi zaman sa a can, duk yanda ya so ya janye daga wannan tunanin da ke faman addabar sa kamar ana ƙara huro masa wuta, amma ya gaza don tunanin ya soma cin ƙarfin sa, har yana jin kamar sabon soyayyar Haseena ce a zuciyarsa ke son azalzalan sa, kuma ga mararin ganin ta da yake bukata,
Tuna lokacin baya da yanda ya sha fama da wahalhalun soyayyarta, da kuma shawaran da Hanif ya basa har ya samu sauƙi, shiyasa ya soma ƙoƙarin karanto addu'o'i a ransa, amma hakan ya gagara, sai ya kama kuma sai ya saki, tsaki ya dinga ja sai kuma ya tashi ya nufi saman dainng ya haɗa tea mai kauri ya shanye, yana sha yana faman tunani ya dafe kansa da hannu ɗaya,
Daga ƙarshe kuma bayan ya gama sai ya miƙe ya koma ɗakin sa, ko kallon inda Maryamu take kwance bai yi ba, ya shige toilet ya faɗa wanka sannan ya fito ya shirya cikin ƙananun kaya, mai ruwan ƙwan riga wacce ta matse shi tayi masa kyau ainun, sannan ya sanya blue jeans tare da combat din sa shima blue, tsab ya fito yayi kyau cikin kwalliyan da yayi, sai ya feshe ko'ina nashi da turarukan sa masu shegen ƙamshi da fizgar hankali,
Daga nan ya fice after ya ɗauki mukullin mota da wayansa, ya fita ya ɗauki motansa yabar gidan tare da nufan gidan su Haseena, don yana ji a ransa idan bai je ya ganta koda sau ɗaya bane komai zai iya faruwa, yana fatan ace tana nan bata bar ƙasan ba; since ya ji labarin mutuwar Mahaifiyarta maybe tana nan bata tafi ba

Inda fitan sa ke da wuya Maryamu ta farka, sabida a ɗan firgice take gaba ɗaya yanayin nata ba ta jin daɗi, wani irin ƙuncin zuciya take fama dashi, yayinda nan da nan kanta ya soma sara mata, musamman da ta buɗe ido ta soma jin ƙamshin turaren SHAREEF ya cika mata hanci sosai, sai ta ji ranta ya soma ɓaci kamar zata yi amai, saurin rufe hancinta tayi tana sake laluba kan gadon jin da tayi kamar babu kowa,
Ta sha mamakin rashin ganinsa, but sai tayi shiru tana tunanin maybe yana toilet ne, amma ganin har lokaci ya ɗan soma ja dole ta miƙe tana dafe da kanta da ke faman sara mata, ji tayi baza ta iya ci gaba da zama a ɗakin ba, shiyasa sai ta ɗauki yaloluwar rigan barcin ta ta fice daƙyar take tafiya,
A falo ma babu kowa, but sai ta tsaya tana kiran sunan sa tana mamakin ina ya shiga, har kitchen ta leƙa bata ganshi ba,
Bakin window ta nufa ta leƙa sai ta ga babu Motansa ɗaya a wurin, hakan ya tabbatar mata da ba ya gidan kacokan,
Dole yasa ta koma ɗakinta amma tana mamakin inda ya je, bata wani tsauwala ba sabida barcin da ke damun ta, ga kuma ciwon kan da ke mata barazana tana jin duk babu daɗi a tattare da ita, kwanciya tayi ta rufe kanta da blanket but ta gaza yin barci, abu kamar wasa ciwon yana ƙara daɗuwa mata, wani irin ciwon kai ne ke kawo mata cafka ga faɗuwar gaba zuciyarta sai buga wa take yi,
Tun tana jin abun da wasa sai kuma abun ya fara cin ƙarfin ta, lokaci guda ta soma fita a hayyacinta manyan idanuwanta sun ƙara buɗewa sun yi wani irin ja kamar zasu fito,
A hankali ta soma sakin kuka tana murkususu kamar wacce hankalinta ya gushe,
Sai ta soma ganin ɗakin ya soma canza mata kala kamar ya koma daji-daji, amma bata da ƙarfin addu'a yayinda gaba ɗaya yanayin ta ya gama sauya wa

Wata ƙatuwar Kunama ne ta faɗo a saman gadon, ƙatuwa ce mai narkeken kai da baƙin jiki, lokaci ɗaya ta ɗana Kunamar ta zata kai mata sara
Chapter 62 · 0% Book details