← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 75

Sashe 21

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

__________
*BOOK2*
_______________*PAGE11*
_____This video that they saw, they were very happy, ko banza yanzu sun samu hujja,
Musamman SHAREEF yayi farin cikin ganin bidiyon nan, alamu ya nuna zai yi nasara a kan su Alhaji Inuwa, kwana kusa zai nuna musu ainihin wane ne shi, domin duk yanda suka kai ga wayon su; zasu girbi abun da suka shuka, asaran da suka sanya su ya É—auki alkawarin sai sun biya su,
Take ya kira Mahmud É—in yana sake tambayarsa abun da ya faru

Nan yayi masa bayani har mutumin da ya sani a ciki, wanda ya taɓa ganin su tare da Shuraihu a nan Company, kuma da alamu suna da relationship mai ƙarfi

"Ok duk yanda za a yi gobe ka dawo Mahmud, kabar su PA a nan ka dawo sabida ka binciko mana inda Mutumin nan yake, before mu danƙa komai a wurin ƴan sanda dole muna bukatar hujja, sai mun saka su sun yi magana we will get proof and then we will take it to the police, idan wannan guda ɗayan ya zo hannun mu sauran ma zasu zo."

Mahmud yace, "ok whatever you say it will be done, na san bazai bani wahalar nemowa ba insha Allah, zuwa gobe ina kan hanya."

Bayan sun gama wayan; Hanif da ke sauraron su yace, "No bro, meye zai haɗa mu da aikin da yakamata police ne zasu yi? Ni ina ga idan an kama su just mu miƙa su wurin hukuma, a wurin su zasu yi bayanin waɗanda suka saka su, amma wannan aikin ba hurumin mu bane."

Dubansa SHAREEF yayi yace, "bazan yi irin wannan saken ba Hanif, baka san yanda ƙasarmu ta lalace ba ko? Dole sai na samu ƙwaƙƙwaran hujja a hannuna before in miƙa su wurin ƴan sanda, don gudun samun matsala, waɗannan hatsabiban mutanen komai zasu iya yi."

Shi kansa Hanif ya fahimce sa, shiyasa ya gyaÉ—a kai yace, "well, hakan za a yi kuwa, to shikenan Allah ya bamu Sa'a a kansu."

Daga haka suka ci gaba da tattaunawa a kan maganar, har suka gama shirin su na kwanciya suka kwanta.
***

_____Zuwa washe gari ƙarfe goma Hanif ya tafi gidan su Amra, domin ya kaisu gidan da Dady ya ba su

While SHAREEF tun safe ya wuce wurin aiki,
Tare da tsumayen dawowan Mahmud

Shima dayake ya bugo sammako, kafin sha biyun rana ya shigo Kanon,
Direct Companin ya wuto suka haÉ—u da SHAREEF,
Sai da suka tattauna before ya wuce gida yayi uzurin sa,
Daga nan fa ya soma bincikar yanda zai yi ya ga mutumin,
Farko Companin Alh. Inuwa ya soma zuwa, cikin dabara ya soma bincika wa ko Allah zai sa ya haÉ—u da shi, kasancewar ya san a nan Shuraihu yake aiki shiyasa yake taka-tsan-tsan kar su haÉ—u,
Bai wani samu abun da yake nema ba, dole ya koma Companin Honourable Ja'e can ma ya gama shawagin sa,
Daga karshe ya kira SHAREEF suka yi magana da shi

Shi ya ba shi shawaran, "ya riƙa bibiyan Shuraihun dole zai iya ganin su tare."
Sannan ya faÉ—a masa, "ya shiga WhatsApp yana nan ya tura masa hoton mutumin wanda aka yi editing a videon, zai taimaka masa."

A taƙaice dai ranan ta wuce Mahmud bai ci nasaran samo mutumin ba,
Haka ma washe gari ya É—aura da neman sa, babu inda bai je ba don ya samu damar da zai samo shi, a Companin Alh. Inuwa ya wuni yana bibiyan Shuraihu ko zai dace,
Ganin har yamma tayi dole yayi kasada ya samu mataimakin Shuraihu a cikin sirri ya faÉ—a masa abun da yake so yayi masa, tare da yin masa alkawarin kuÉ—aÉ—e masu yawa

Bayan ya nuna masa hoton mutumin, sai ya faÉ—a masa, "ya sanshi, amma bai san inda yake zaune ba, ya ba shi nan da anjima cikin dare ko gobe zai iya binciko masa komai a kansa."

Mahmud ya ji daÉ—i yanda mataimakin Shuraihu ya amshi tayin sa bai nuna ja ba, don haka ya tafi yana saka ran dacewa, bai sanar da su SHAREEF ba don ya fi so sai ya kawo masa bayanan before ya faÉ—a musu nasaran da aka samu.

🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆

     
_____Yau Haseena ta dawo hutu, kasancewar tun bayan tafiyan da tayi after an ɗaura musu aure da SHAREEF, bata sake zuwa ƙasar ba, sai wannan lokacin

Driver da Haajara suka je É—auko ta,
Abun mamakin yanda Haajara ta ga ƴar uwan nata ta sake sauya wa, kamar ba ita ba, gaba ɗaya tayi wani irin haske tayi jazur kamar jini zai fita a jikinta, dama tun farko Haseena tana shafe-shafe wanda hakan ne ya mayar da skin ɗin ta fara, but yanzu man da ta sauya ga gyara da take yi wa jikinta; ta ƙara sauya wa sosai, don ko SHAREEF da yake jawur idan ya tsaya a gabanta sai ya dishe, har da hujin hanci tayi irin na Nana, sai dai nata guda ɗaya ne kuma bata yi a baki ba

Baki kawai Haajara ta saki tana kallonta, musamman yanda ta ga ta zuba zobuna a hannayenta sai shining suke yi kamar na zinare, ga farata a yatsunta masu tsayi sun sha kala, riga da wando ne a jikinta matsatstsu tamkar ba Æ´ar musulma ba haka ta koma, don har kanta ta bari a buÉ—e ta sha gashin attachment maroon colour,
Kasa haƙura Haajara tayi tace, "wai Aunty Haseena anya kin ga shigan da kika yi kika taho nan? Kinga yanda kika koma kuwa?"

Wani kallo ta watsa mata tana faman taunan chewing gum da ke bakin ta, sai wani ƙaras-ƙaras take yi kamar wata ƙasurgumar karuwa,
Take ta shige cikin motan da aka zo daukar ta, ta ƙame a back sit ƙafa ɗaya kan ɗaya tana faman latsa tafkekiyar wayan da ke hannunta

Motan Haajara ta shiga kusa da ita, sannan drivern ya ja motar suka tafi, since tuni ya zuba Jakar kayanta a Boot

Duban ta Haajara ta sake yi bakin ta ya ƙi rufuwa don mamakin yanda ƴar uwan nata ta koma, ko ita da take bala'in son ƙananun kaya tun farkon ta, baza ta iya saka kayan da Haseena ta sa yanzu ba, bare har ta taho tun daga wata uwa duniya ta zo ƙasar su mutane na kallonta a haka, domin kayan da ta sanya dasu da babu duk ɗaya don bata ga amfanin saka su ba a yanda suka fitar mata da halittar jikinta, uwa uba yanda tayi mugun ƙiba komai na jikinta yayi ɓul-ɓul gunun sha'awa, koda gani Hutu da jin daɗi sun ƙara bayyana a tattare da ita,
"Aunty Haseena, meyasa kika taho a haka bayan kin san nan ƙasar tamu daban da can inda kike? Idan kina wannan shigan a can bai kamata ki taho a haka ba, don wlh idanun mutane sai sun yi yawa a kanki, sai kin gummace ba ki taho a haka ba, bare kin san mutune ba a iya musu..."

"Please shut your mouth, you are bothering me with this nonsense of yours." Ta jefa mata harara

Tura baki Haajara tayi tana cewa, "ai gaskiya na faÉ—a Aunty Haseena."

"To ki ci gaba da maganar, I will annoy you now."
Ta ja tsaki tana ci gaba da latsa wayan da ke hannunta, face É—in ta babu walwala wacce ke tattare da tsananin damuwa; sakamakon abun da suke discussing a kai ita da Nana,
Kwata-kwata hankalinta ba ya kan Haajara da ta ƙi yin shiru ta ci gaba da maganar,
Hankalinta a tashe yake a yanzu sabida jin abun da Nana take faÉ—a mata,
Take zufa suka soma keto mata zuciyarta na tsananin buga wa sabida ruÉ—u da tashin hankalin halin da take ciki,
Bata san ma an kawo gida ba sai da Haajara tayi mata magana,
A firgice ta É—ago tana kallonta

Ita kanta Haajara ta ga yanayin ta ya sauya gaba É—aya ba a yanda ta zo ba,
Shi yasa cikin damuwa take tambayarta, "Aunty Haseena mai kuma ya faru kika shiga wannan halin? Wani abun ne ke damun ki?"

"Nothing."
Ta amsa mata tana ƙoƙarin bude kofan ta fice.
***

_____Haseena tayi ƙoƙarin ɓoye halin da take ciki sabida ganin Iyayenta,
Sun yi murnan ganin ta but sauyawan nata yayi mugun basu mamaki suma,
Har sai da suka kasa shiru suka hau ta da tambaya; musamman yanda ta taho har wani uwa duniya a haka da irin wannan shigan,
Basu yi mata wani faÉ—a ba tunda dama ita Æ´ar gaban goshi ne, soyayyar da suke mata yasa ba sa ganin laifin ta,
Kawai Abbansu ne yayi mata maganar shigan nata, yace, "kar ta ƙara zuwa a haka, nan da can ba ɗaya bane, ai yanzu kiwon mutane ake yi ba dabba ba, yanzu sai ya zama abun magana."

Daga nan bayan sun gama gaisawa sai ta wuce ɗakin ta don yin wanka kasancewar a gajiye take, bare tana son keɓewa don ta samu mafita a kan maganganun da Nana ta faɗa mata,
Ina gaskiya sam baza ta taɓa yarda da wannan sharaɗin ba, tun farko maiyasa ba a faɗa mata ba sai yanzu za a ce mata ana buƙatar wani daga cikin dangin ta, to wa zata bayar wa ƙungiya? Gaskiya bazai yiwu ba, hankalinta ya tashi ne da Nana tace mata, "a cikin Iyayenta dole ta zaɓi ɗaya ta sadaukar wa da ƙungiya, tunda haka ake yi sai kana bada jini, bazai yiwu kai kana shan jinin wasu ana biya maka bukatunka da na wasu ba; but kai baza ka bayar ba."

Daƙyar tayi wanka ta sauya kaya ta koma Falo, kasancewar Umma ta dame ta ta fito ta ci abinci, hankalinta ba a jikinta yake ba don ta ƙosa ta samu damar da zata kira Nana suyi magana ta tsakani da Allah, domin bata yarda da wannan hukuncin ba, zata iya bada kowaye ne a cikin dangi ban da Iyayenta,
Da wannan tunanin ta É—an saki jikinta after ta ci abinci sun É—an yi hira, sai tace, "zata je ta kwanta ta huta."
Chapter 21 · 0% Book details