Sashe 65
Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Inda Doctor Abbas ya soma ƙoƙarin duba ta yana son ya tabbatar tana da rai ko kuwa?
But bai gane hakan ba, cus har lokacin babu inda nata yake motsi, duk wani wurin da ake gane mutum yana da rai ya taɓa ya ji shiru, shi kansa hankalinsa ya soma tashi; ga SHAREEF da ya tasa sa a gaba sai faman tamabayarsa yake yi yana cewa, "ya taimaka masa."
Shi kansa abun ya soma basa tsoro sabida a halin da ake ciki ya soma tunanin babu rai a jikin Maryamu, don a yanda jikinta ya saki yayi sanyi ƙalau komai nata ya dena harbawa
"Please Doctor, do something, kar wani abu ya same ta."
Ɗago ido yayi ya dube sa jikinsa a sanyaye, sai kuma ya kasa yin magana ya ci gaba da ƙoƙarin tattaɓa ta, "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!" Abun da ya iya furta wa kenan batare da ya ɗago ya dubi SHAREEF ba
Inda SHAREEF hakan ya sake saka shi a ruÉ—ani, sosai a yanzu jikinsa ke faman rawa, haka ma muryansa da yake kiran sunan Doctor da faÉ—in, "what's going on? Please tell me doctor me ke faruwa?"
Huci ya ja sai ya kalle sa yana faÉ—in, "Im so sorry..."
"Noo kar ka faɗa min rubbish Malam, meke damun ta? Ka duba ta ka tsaya kana kallonta taya ya zaka san me yake damun ta?" Ya katse sa cikin tsawa a haukace cikin rikicewa; saboda kar ya ji abun da zai furta masa, wanda tuni har ƙwalla sun soma taruwa a idanuwansa sabida halin da yake ciki, lallai bazai iya yarda da cewa Maryamu ta barsa shi kaɗai ba, wannan ƙarya ne.
[08/05, 6:52 PM] Ù†Ùيسة OumÆŠahira: 🌱🌱🌱🌱🌱
    *SHAREEF*
      _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱
_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_
*Littafina na kuÉ—i ne, ki biya ki karanta, zaku iya samu na a kan wannan numban wayan. 07065334256.*
__________
*BOOK2*
_______________*PAGE34*
_____Ganin yanda SHAREEF ya ruɗe, dole Doctor Abbas ya ci gaba da bata taimakon gaggawa sabida samun ganin tana da rai ko babu, wanda daƙyar ya iya ganowa wani jijiyarta a hannunta yana motsa wa, shima sai da yayi da gaske before ya gane sabida sai ya ɗauki some minute's yake jin jijiyar tana harbawa,
Da sauri ya ce wa SHAREEF, "ina ga tana da rai, calm down please SHAREEF, go and set komai zai daidaita."
Har SHAREEF ya ji sanyi a cikin ransa, amma ya kasa zama yana tsaye a wurin yana kallon yanda yake aikinsa cikin ƙware wa,
Daga karshe ya kira wata nurse ta sake kawo masa wasu kayan da yake bukata har drip aka sanya mata, aka yi mata allurai a cikin ruwan
Kamar shuɗewar seconni sai gani suka yi kamar zata farfaɗo, numfashin ta ya dawo amma yana sama-sama zai ɗauke tana wani irin ƙara kamar mai cutar athma
Hankalinsu ya ƙara tashi abun ya cutura, iya ƙoƙarin Doctor ya rasa abun da zai yi mata, ga shi duk wani taimako sun bata amma still tana nan a yanda take; numfashin ta na ƙoƙarin fice wa har ta soma fizge-fizge zata faɗo a kan gadon,
Sai lokacin ma suka kula da ƙafanta ɗaya yanda diddigen ya kumbura suntum
Doctor Abbas ne ya soma kula da wurin, ya ja salati a tsorace yake nuna wa SHAREEF wurin
A ruɗe SHAREEF da ya tallabo ta jikinsa yake kallon wurin, shi kansa ya tsorata fiye da tunani, ga kuma halin da ya ga ta soma yi tana fizge-fizge har wannan lokacin ba ta hayyacinta, lokaci ɗaya ta tsandara uban ihu tana son ƙwace wa a jikin SHAREEF, a wannan lokacin ya rigada yayi tunanin tabbas bazai wuce Aljanunta bane, tunda ya san tana dashi don haka ya dubi Doctor yace, "zan wuce da ita gida, bazai yiwu mu zauna a nan ba."
Da sauri doctor yace, "No, ina zaka kAita kuma ban da nan? Please ka bari mu duba ta da kyau na san bazai wuce wani abun ne ya cije ta ba, tabbas hakan ne don ga alamu nan."
Girgiza kansa yayi fuskarsa cike da damuwa yake cewa, "No, gwara in kaita wurin su Momy, cuz tana fama da jinnu I think su ne gaskiya, don haka take yi, ina ga bari in wuce da ita kawai."
Shi kansa Doctor ya tausaya mata, don haka ba ɓata lokaci ya basa damar tafiya har wajen mota ya raka sa
Mutane sai kallonsu suke yi sai dai basu san mai ke faruwa ba, amma tunda asibiti ne sun san dole majinyaciya ce; tunda a yanda suka ga an fita da ita tana ihu da bige-bige
Doctor bai bar wurin ba har sai da ya ga tafiyar SHAREEF ya shiga cikin hospital É—in, dama already ya tashi aiki zai koma gida ne kuma ya hangi SHAREEF, don haka ya je ya harhaÉ—a kayansa ya rufo office din sa
Yayinda SHAREEF tuni ya isa gidan su, don a yanda yake tsula gudu a cikin daren nan burin sa kawai ya gansa a gida
Time ɗin har ma'aikatan gidan sun kwanta, har Mai gadi ya rufe dakinsa, amma jin horn sai ya fito da sauri, dayake akwai hasken lantarki bai yi amfani da wayansa ba, sai da ya leƙa ta ƙofa ya hangi motan SHAREEF wacce ya shaida ta, don haka tuni ba ɓata lokaci ya zaro key din kwaɗo daga aljihun sa ya fito dashi ya buɗe kwaɗon da ya garƙame gate ɗin,
Nan da nan ya buÉ—e masa jiki na rawa; don a yanda ya addabi gidan da horn ko su Momy suna jiyo wa
Da gudu ya shigar da motan ya dakatar da ita a tsakiyar gidan, sannan ya buɗe murfin motan ya koma ta baya don ciro Maryamu da har yanzu tana nan cikin wannan fitan hayyacin, sai kukan ta ma da ya ƙaru tuni ta gama tuttuge gashin kanta, rigan barcin jikinta kuma tuni tayi sama ta kusa cire ta, Allah yasa akwai pant a jikinta,
Don haka sai da SHAREEF ya gyara mata rigan daƙyar ya fito da ita saboda yanda take zille wa
Dama su Momy da ke zaune a falo already sun ji ƙaran horn din, hakan kuma ya ɗarsa musu zargin ba lafiya ba har Dady yana tambaya,
Yayinda ya rage ƙaran Tv yana ƙoƙarin miƙe wa a wurin,
Daga nan ne suka soma jin kamar ihu yana ratso su
Dalilin da yasa suka tashi kenan, suka nufi bakin ƙofan har da haɗawa da ɗan gudun su,
Fitan su ke da wuya; suka hangi SHAREEF rungume da Maryamu a jikinsa shima ya nufo gidan,
Dukkannin su sai da gabansu ya faÉ—i ganinsa a haka da tuni sun tabbatar da Maryamu ce a hannunsa
"Lafiya SHAREEF; me ke faruwa?" Gaba ɗaya suka soma jero masa tambayoyin hankalin su a matuƙar tashe
Yayinda SHAREEF ya soma ƙoƙarin kora musu bayani a ɗan ƙanƙanin lokaci
Tuni Dady yace masa, "ya mayar da ita mota su wuce da ita wurin Malam."
Don a lokacin sun fahimci cewar ciwon ta ne ya tashi,
Nan Dady ya koma ya sako takalmansa yana cewa Momy, "ta jira su; su je su dawo."
But Momy tace, "a'a su tafi tare kawai."
Don haka gaba ɗaya suka koma cikin motan SHAREEF, Momy ta riƙe Maryamu a bayan mota, su kuma suka shiga gaba suka bar gidan,
Tun a hanya Dady ya nemi wayan Malamin da yake duba ta yayi masa kira,
Sai a kira na uku sannan ya same sa,
Nan ya zayyane masa halin da ake ci ya faÉ—a masa, "suna nan tafe a hanya yanzu."
Malam yace, "to shikenan yana jiran su sai sun zo."
Dukkansu babu natsuwa a tattare da su, musamman Oga SHAREEF wanda tuni ya daÉ—e da rasa natsuwarsa ga tashin hankali, Dady yake masa kwatancen gidan har suka isa kofar gidan Malamin
Already har ya fito yana jiran su a waje,
Don haka shi ya jagorance su zuwa ciki,
Inda SHAREEF ya ɗauko Maryamu daƙyar ya shiga da ita ciki
A gabansu Malamin yasa aka kwantar da Maryamu a saman tabarma, sannan ya fara gabatar mata da karatun Alkur'ani bayan ya riƙe ta sosai
Da farko kukan kawai take yi mai tayar da hankali, amma daga karshe sai ta koma ihu ta ci gaba da fizge-fizge tana shirin kamar zata tashi
Nan Malamin ya sanya SHAREEF ya zo ya riƙe ta gam, dayake yanzu babu tsoron don ta lafiyar Matarsa yake yi, nan kuwa ya zo ya rungume ta ya manna kanta a ƙirji ya haɗa da hannayenta yayi mata mugun riƙo irin nasu na Maza, gaba ɗaya ƙarfin sa ya samu ya danna mata amma duk da haka ya gaza riƙe ta, don abun yayi worst da yawa,
Sai da Dady ya taimaka tare da Malamin ya ci gaba da zuba mata karatu
Dama can tun farko bata taɓa magana ba duk karatun da za a yi mata ba sa magana sai dai tayi ta ihu, amma abun mamakin yanzu sai ta fara maganganu tana faɗin, "su sake ta ba ta son karatun, kar su kashe ta su taimaka mata."
Nan fa Malamin ya ƙara ƙoƙarta wa wajen ci gaba da karatun da ƙarfinsa yana yi yana karanto ayatul kursiyyu, sai da ya galabaitar da ita sosai before ya dakata ya fara tambayarsu dalilin shigan su jikinta?
Tana haki idanunta suna zubar da ruwan hawaye kamar ana kwarara mata ruwa, gaba ɗaya ta jiƙe da zufa idanunta sun kaɗa sun yi jazur sun sake manya har wani nama-nama suke yi na ja,
Da farko ta ƙi magana sai da ta ji yana ce mata, "zai ci gaba da karatun." Sannan daƙyar ta buɗe baki ta soma magana da muryan Maza, maganar nata na fita ɗaiɗai tana kuka sosai take cewa, "bazan yarda ba wannan karon, tunda suka illata ni da abun da na fi ƙauna, sun so kashe ta a lokacin da nake jikinta, sun yi min illa ba kaɗan ba, bazan taɓa yarda ba sai na ɗauki fansa; domin baza a taɓa min ita in ƙyale ba, duk wanda ya so cutar da ita sai mun ɗauki mataki."
"Kai meye haÉ—in ka da ita har ka shiga jikinta? Ban muku iyaka ba ashe har yanzu kana jikinta?"