← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 75

Sashe 11

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dayake sun san da zuwan nata tunda sun san tana garin, amma basu san cewa ta zo ƙauyen ba, shiyasa Indo ta sha mamakin ganinta a yanzu din, tace, "kai Maryamu, ke ce haka?"

Dariya tayi tana cewa, "wlh kuwa Aunty, zuwana kenan nace bazan zauna ba bari in je mu gaisa."

"To shiga ciki, bari in kwashe ruwan nan don Allah in zo."

Wuce wa Maryamu tayi ta shiga É—akin Indo, wanda sasan ta daban ne da sauran mutanen gidan, babu Yaran ma a gidan shiyasa Maryamu ta É—aga murya tana cewa, "halan Yaran ba sa nan ne?"

"Eh wlh suna islamiyya, Salim kuma yana gareji sai dare zasu shigo da Babansu."

"Wai Aunty har ya fara zuwa gareji ne?"

"Wlh kuwa, to ya ƙi makarantar ba ya son islamiyya, shiyasa Babansu yace gwara ya riƙa bin sa tunda karatun ne bai so, wai shi yayi girma kin san halin Yaran nan Maza, da zaran sun yi tsawon ƙafa sai ki ga suna gudun Islamiyya."
Ta ƙare maganar tana shigowa cikin ɗakin; tare da share hannunta jikin zanin ta,
Zuwa tayi ta zauna a gefen Maryamu tana kallonta cike da fara'a, "wai Maryamu haka kika sauya? Ko dai mun samu ƙaruwa ne?"

Waro ido Maryamu tayi tace, "kamar ya Aunty?"

Indo kuma hararanta tayi tace, "ban sani ba, ai kin san me nake nufi; ko har yanzu halin nan naki na nan na rainin wayon?"

Dariya ta kwashe dashi tace, "kai Aunty, wlh ban gane me kike nufi ba, yo na san meye ƙaruwan da kike magana a kai?"

"To ciki nake nufi, tunda na ga kin sauya ɗin nan kin yi kumatu alamu ya nuna mun samu ƙaruwa ne."

Maryamu baki ta hangame da ƙarfi tace, "tab ɗijam! Wanne ƙaruwa Aunty? Wa ya faɗa miki a gidan Miji nake? Ina fa Abuja ina zaune a can nake karatu na."

"Ke don Allah? FaÉ—a min gaskiya?"

"Wlh kuwa Aunty, Ni ina Abuja ina karatu wurin ƙanwar Momy, babu wani ciki a jikina zaman dad'i ne kawai da Hutu shiyasa kika ga na ajiye tumbi; in ma wannan kike magana." Ta ƙare maganar tana shafa cikin ta tana bushe wa da dariya

Bugun ta Indo tayi tana dariyan itama, tace, "Maryamu kenan! Baki ya san daɗi an samu abun da ake so, har yanzu hali na nan, wlh mun yi kewar ki, kuma hutun sai ya amshe ki sosai, gaskiya ba ƙaramin kyau kika yi ba, har fa wannan baƙin da kika fi mu duk ya shige kin yi fresh abun ki."

Tura baki tayi gaba tace, "kai Aunty! Aina na fi ku baƙin? Wlh ban fi ku ba."

"Ai sai ki yi, kowa ya san kin fi mu baƙi, baƙin ki kamar gawayi, Allah ina ganin Shatima ne kawai ya biyo ki amma kaf gidan mu kin fi mu baƙi."
Ta ƙare da dariya; tunda dama tayi ne don tsokana

Ilai kuwa Maryamu tuni ta ɓata fuska, don a rayuwa ta tsani su ce mata ta fi su baƙi, kaf gidan ita ce baƙa

Sai da ta ga ta soma kumbura fuska shiyasa ta koma rarrashinta tana faÉ—a mata, "da wasa take yi."

Haka dai suka ci gaba da hiran nasu gunun ban sha'awa,
Tana shirin ma tafiya ne Ummita ta zo gidan, since ta ji labarin zuwan nata shiyasa ta tafi gida aka ce mata Maryamun ta fita zuwa gidajen su,
Maimakon ta wuce gida sai ta biyo ta gidan Indo don ta san baza ta wuce gidan ba ƙila, ko kuma gidan Bintu, ta fi gasgata dai ƙila tana gidan Bintu, amma bata wuce ba tace bari ta soma duba gidan Indo tunda nan ne kusa,
Ai kuwa tana shigowa ta tarar da ita,
"Dama kamar na sani, nace bari in fara shigowa nan ko Allah zai sa in ganki, ashe kina nan?"

Tashi Maryamu tayi ta rungume Ummita kamar zata ka da ita don murna

Sai da tayi da gaske ta ture ta tana cewa, "ban san sakarci fa, meye haka kamar ba ki girma ba?"

"Allah murnan ganin ki nake yi Aunty, dama yanzu zan wuce muje gidan naki."

Indo na dariya tace, "kinga yanda Meramun Bashir ta canza tayi kumatu ko? Kamar ba ita ba."

Ummita ta kama haɓa tana kallon Maryamu da ke ta wangale baki, kallon sama da ƙasa tukunna tace, "abun da na gani kenan na kasa magana, Allah mai iko! Kamar ba ita ba wlh, rayuwa kenan!"

Haka dai suka dinga maganganu suna tsokanar Maryamun sai dariya take musu, don ita farin cikin ganin ƴan uwanta ya fi mata komai a wannan gaɓar, ba ƙaramin kewar su tayi ba, ƙarshe ma a nan suka zauna basu tafi ba har Yaran Indo suka dawo suma sai faman murnan ganin Maryamu suke yi,
Haka ta tasa su gaba ta buge wannan ta mangare wancan tana cewa, "sun ƙara ƙaton kai na rashin ji."

Sai da aka kira Magriba sannan suka fita, Ummita zata wuce gida ita kuma Maryamun zata wuce gidan Bintu,
Tace mata, "ta nuna mata gidan Bintu can zata tafi."

Ummita tace, "kawai ta haƙura zuwa gobe sai ta je, tunda yanzu Magriba tayi gwara ta koma gida."

But Maryamu ta ƙi, a cewarta, "tana son zuwa yau, ko ba jima wa zata yi ba gobe zata sake koma wa, baza ta iya kwana bata ga Bintu ba zata iya mafarki, tunda ga baki ga hanci wlh sai ta je zata samu sukuni."

Duk yadda Ummita ta so ta hana ta don ta koma gida, amma ta ƙiya, shiyasa tayi mata kwatancen gidan; since babu nisa da gidan Kakannin su.
[31/03, 4:32 AM] نفيسة OumƊahira: 🌱🌱🌱🌱🌱

       *SHAREEF*
           _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱

_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*Littafina na kuÉ—i ne, ki biya ki karanta, zaku iya samu na a kan wannan numban wayan. 07065334256.*

__________
*BOOK2*
_______________*PAGE7*
_____Lokacin da Maryamu ta je gidan Bintu, Mijinta ya dawo a time ɗin, shi ne ma a waje yana ƙoƙarin yin alwala ya fita, Bintu ta shiga ɗaki ɗauko masa hulan sa, sai jin sallaman Maryamu tayi, duk da bata yi tunanin ita bace amsa sallaman kawai tayi

AbdulHadi da ke faman kuskure baki, bai kai ga amsa sallaman nata ba tunda ya saka ruwa a baki, yana bin ta da kallo da mamakin ganin ta ya tofar da ruwan yana cewa, "kamar Maryamu nake gani?"

"Ni ce, ba kama ba."

"Ikon Allah! Yaushe a garin?"

"Yau, ina Bintu take?"

"Bintu... Bintu."
Ya soma kwaÉ—a mata kira da saurin sa

Amsa mishi tayi tana fitowa rike da hulan, amma ganin Maryamu a tsaye tana kallonta da dariya a kan face É—in ta, sai ta washe baki ta kwatsa ihun murna tana kiran sunan ta,
A guje kuma ta nufe ta; ba tare da ta damu da É—an cikin da ke jikinta ba, wanda tuni ya fito ana ganin sa, ta nufe ta ta rungume ta tana ihun murna

Itama Maryamun farin ciki take yi tare da ƙanƙame ta suna tsalle a tare

AbdulHadi na tsaye yana washe baki yana kallonsu, sai dariya yake musu ganin yanda suka ƙi sakin juna, wannan ta kira sunan wannan; wannan ta kira sunan wancan,
Sai da ya ga sun saki juna yake mata sannu da zuwa tare da tambayarta hanya?

Bayan sun gaisa sai ya ci gaba da alwalan sabida an kusa shiga Masallaci,
Su kuma suka shiga cikin daki

Maryamu sai kallon Bintu take yi tana kama haɓa, can kuma sai ta tuntsire da dariya tace, "ikon Allah! Wai dama ciki kike dashi Bintu babu labari? Sai da na zo na gani?"

Hararanta Bintu tayi tace, "to ya son ranki?"

"Raina sakayau wlh, gaskiya nayi farin cikin ganin ki a haka, ki ce babu jimawa zan sake dawowa suna, don wlh nayi farin cikin ganin wannan cikin ba kaÉ—an ba."

Murmushi kawai Bintu tayi tana kallon Maryamun gunun sha'awa, sai ta miƙe ta ɗauko mata ruwa a kofi tana ajiye mata, tare da furta, "wai yaushe kika shigo kauyen ne? Nima fa sai jiya na ji labari a wurin Shatima da ya zo gidan nan, yake faɗa min kina gidan Iya Samira kin kusa zuwa, wlh na zata ƙarya ne sai da na tambayi Aunty Ummita."

"Tab! Ai kwana na biyu a can wurin ta, na matsu ne in zo shiyasa na gudo na ƙi zama, amma zan jima ai tunda a nan zan yi Hutu, zan koma can ma."
Tayi maganar tana ɗaukar ruwan tare da ƙoƙarin sha, sai kuma ta tsaya tana duba wa before ta ajiye tana taɓe baki

Bintu da ke faman kallonta tace, "lafiya?"

"Babu komai, kinga ba fa dadewa zan yi ba sabida dare ya soma yi, na kasa hakura ne wlh nace sai na zo na duba ku, kawai zan tafi gobe zan dawo, sai mu yi hiran yaushe gamo."

Bintu tace, "kai don Allah ki tsaya mana, ga abinci ma ina yi idan na sauke mu ci tare, amma daga zuwa kuma ki ce za ki tafi? Ko kin je har gidan su Yaya Naziru ne?"

Before tayi magana sai ga sallaman Bashir ya shigo gidan yana kwaÉ—a kiran ta

Tashi tayi da sauri ta fita,
Bintu ma ta bi bayanta tana amsa sallaman

"To leda mai yawon banza, ashe kina nan ne ana neman ki? Daga zuwa gari kin soma yawo, ashe kina nan da halin ki wato? To mu je gida Baba na kira."

Hararansa tayi tace, "Ni fa ba na son takura, daga zuwa zaka zo ka fara damuna, yaushe na zo gidan ne?"

Kunnenta ya murɗe yana faɗin, "ƴar banza, dama Ni kaɗai ne ban yi kewar ki ba don bakin nan naki na rashin kunya, kin dawo kenan, wlh ba ƙyale ki zan yi ba nima hali na yana nan tafka za ki sha, ina tunanin kafin ki koma inda kika fito sai na ƙara ma bakin nan tsini."

Hannunsa ta buge sabida zafin da ta ji, lokaci guda ta tsuke fuska tana cewa, "Allah ya isa mugu azzalumi, wai kai meyasa halin mugunta ka iya kodayaushe?"
Chapter 11 · 0% Book details