Sashe 30
Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yayinda Maryamu sam bata san ma yana yi ba, domin a wurin ta abun farin ciki ne ma saboda rashin ganinsa da bata yi, har cikin zuciyarta itama ba ta son tana ganin sa sabida yadda take jin tana diririce wa damuwarta ta dawo sabo; haka ma soyayyarsa. Tayi tunanin zata iya jurewa ta cire soyayyarsa a rai, musamman yadda ta ɗauki tsawon lokaci bata ganin sa, amma ashe ba haka ba, juriya kawai take yi wajen kawar da kanta a gare sa har tayi kamar bata san da shi ba a rayuwa, amma a ƙasan zuciyarta tsantsan ƙaunarsa da tsananin son ganin sa ne yake addabar ta, tamkar zuciyarta zata fashe don azabtuwar da take yi wurin jin ƙuna da tuƙuƙi kamar ana hura mata wutan ƙaunarsa, ji take yi kamar ta dinga kurma ihu idan ta keɓe wuri guda babu mai ganin ta, amma sam ta gagara yin haka, sabida alkawarin da ta ɗaukar wa kanta a kan baza ta sake zubar da hawaye a kansa ba, hakan ne yasa abubuwan suka yi mata yawa a kullum jin ƙirjinta take yi kamar ana mata suya, wani abu ya dunƙule mata tare da raɗaɗi wanda tana jin kamar baza ta iya jurewa ba, musamman in ta ga gibtawar sa,
tana son zubar da hawaye ko don ta samu salama amma inaa; ta ƙi bari hawayen su zubo mata, yayinda take kokarin hana kanta kowanne irin tunanin sa ne, a zahiri zaka yi tunanin babu shi a ranta ne sam, domin rayuwarta take yi normal cikin walwala da farin ciki babu komai da ke nuni da ta damu dashi, amma a cikin zuciyarta ita kaɗai ta san azaban da take sha, bata da sukuni ko kaɗan,
Da yawan lokuta don shi take tashi tayi Ibadan dare, ada bata da burin da ya wuce tayi addu'ar da Allah zai amsa don ta same shi, amma a yanzu, burin ta kawai ta samu sauƙi daga makauniyar soyayyar da ta riƙe mata ruhi, Allah ya cire mata shi gaba ɗaya a ranta, addu'ar ta kenan a kullum Allah ya cire mata son bawan nan nasa ya maye mata da alkhairin sa,
Amma sam babu ci gaba kullum jiya iyau, sauƙin da ta samu kawai yanda yanzu ba ta iya bayyana soyayyarsa a fili kamar yanda tayi haukan sonsa a baya, yanzu tana iya shanye duk wani abu a cikin ranta ba tare da kowa ya san meye a zuciyarta ba,
Wannan shi ne ci gaban da ta samu
Har su Ammee suka gama hutun sati ɗayansu suna shirin tafiya, wanda a ƙarshen ziyarar su ne suka je gidan su can family house din su, shima wannan karon har da Momy ta bi su tunda gida ne, a can suka wuni sai dare Babban Yayan su Momy ya kawo su,
Don shi ne kaÉ—ai namiji a cikin É—akin su, shima bai cika zama a nan ba yana can Kaduna yana aiki, but Matansa guda biyu ne, É—aya tana zaune a nan Kano tunda ita ce Uwar gida tana da yara manya, kuma ta aurar da Mace É—aya da Maza biyu, É—aya kuma Amaryan wacce bata fi shekaru huÉ—u da auren ta ba, Yaron ta É—aya ita ce take zaune a Kaduna inda yake aiki
Alhamdulillah Familyn suna zaune lafiya, don in ka ga ahalin baza ka taɓa cewa akwai ƴan uba ba, suna zaune lafiya sun haɗe kansu kamar yanda tun farko Mahaifinsu ya koyar da su
Su Ammee suna gama hutun su suka wuce gaba É—aya, Maryamu kamar ta bi su don bata so su Aakifah su tafi ba,
Amma babu yadda zata yi kasancewar hutun sati Uku ne kacal, can ma zasu wuce dangin Abee É—in su ne suyi hutun a can shine dalilin da Ammee ta wuce dasu, amma ba don haka ba zata bar su ne suyi hutun gaba É—aya
Bayan tafiyar su; Momy tare da Maryamu suka shiga kitchen suka soma shirya abincin dare, suna yi suna taɓa hira Momy tana tambayarta a kan harkan karatun nata,
Nan kuwa ta zauna tana ta bata labari tunda Maryamu akwai son zance in ta samu wuri, bakin ta ba ya shiru,
Har labarin kammala koyon computern su take bata, don yanzu sun gama komai Abee yayi musu alƙawarin siya musu computer, yanzu kuma sun koma koyon makeup ne
Suna cikin girkin ne su Hanif suka dawo gidan,
Dama su Dady suna zaune a falon; shi da Sadiq da shi yake harkan karatun sa a cikin laptop,
Hanif ne ya wuto kitchen É—in after sun gama magana da Dady a kan aikin nasu, yabar SHAREEF a can suna ci gaba da zanta wa
Lokacin da ya shiga yake kiran sunan Momyn da cewan, "Weldon Mom, ashe kuna nan? Tunda na ji ƙamshi da ɓuruntu nace bari in taho."
Ya ƙarisa wurin yana duban tukunyan da ta buɗe tana juyawa
"Ina nan Hanif, muna aiki da Maryam, ai yanzu ma zamu kammala."
"Sannu da zuwa Yaya Hanif." Maryamu tayi maganar cikin fara'a tana dakata wa daga fere doyan da take yi
While shi kuma ya sanya hannu ya ɗauki wuƙan da faɗin, "an gaishe ki My sister, su Aakifah sun tafi sun bar ki da kewa ko?"
Dariya tayi tace, "wlh kuwa Yaya, amma tunda ga ku na san zaku maye min gurbin su."
Sai tayi saurin miƙa hannu zata amshi wuƙan da faɗin, "No Yaya kar ka ɓata hannun ka kawo don Allah."
Ɗan hararanta yayi yace, "wa yace miki ban iya ba wai? Tambayi Momy ki ji, tun ina ƙarami Ni nake taya ta ayyuka, a can England Ni nake komai ba na siyan abinci."
Murmushi kawai Momy tayi tana canza maganar da faÉ—in, "ina SHAREEF É—in?"
"Yana falo Momy."
Maryamu kama wani aikin tayi tabar masa wannan,
Suka ci gaba da ɗan taɓa hira tsakanin su, har Hanif ya gama fere sauran doyan,
Ita kuma Maryamu ta wanke ta zuba a tukunya ta É—aura a kan wuta
Hannunsa ya wanke sannan ya juya ya fita ya bar su,
Sai da suka gama before suka shirya komai a saman Dinnig, time É—in an kira sallan magriba ma,
Momy tabar wa Maryamu sauran ayyukan ta wuce daki yin Sallah,
While Maryamu kuma sai da ta gama kimtsa komai ta share kitchen É—in before ta wuce dakin ta,
Koda ta shiga, toilet ta afka tayi wanka ta fito, ta nemi riga da wando na fakistan masu sauƙin nauyi ta saka, wandon mai ruwan zuma ne burgujeje wanda za a iya saka mutum a ciki, sai milk color na rigan mai design ɗin kalan zuma,
Ɗankwalin ɗan karami ne, shiyasa bata yi amfani dashi ba, ta samu hula baƙa ta rufe danƙararren gashin ta wanda ya daskare sabida rashin kitso, domin har yanzu Maryamu ba ta ƙaunar abun da zai taɓa mata kan nan nata, da yawan lokuta Ammee take mata faɗan rashin gyara shi tayi kitso, amma da ta fahimci yadda take ciwo duk sanda aka taɓa mata, don haka shiyasa ta dena matsa mata,
Ita kanta Maryamun abun yana damunta yanzu, don tana son ta riƙa gayu da gashin nata kamar yanda su Yusaira suke yi, amma babu hali, da zaran ta taɓa kan da sunan gyara wa ya dinga mata ciwo kenan, sai ta kwana ta wuni tana zazzaɓi, wani lokacin har ta kwanta jinya tsaban azaban ciwo,
Duk da haka yanzu ba kamar baya bane, tana ƙoƙarin ta gyara jifa-jifa duk da ba a mata kitso, sai dai ta wanke kawai haka nan ta ɗan saka mayuka masu ƙamshi, dama can gashin ta akwai shegen ƙarfi, kuma ba shi da tsawo sai yawa, dalilin da yasa in ya cinkushe take shan bak'ar wahala kenan
After ta gama shirya wa ta saka slippers ta fice zuwa Falo
Su Dady basu dawo ba sai da aka yi sallan isha'i sannan suka shigo
While SHAREEF kuwa tunda aka yi magriba ya bi ta ƙofan baya ya koma ɗaki,
Bai fito ba sai da ya ji an kira sallan isha'i sannan ya koma masallacin,
Koda suka idar shine ƙarshen shigowa gidan
Tun da ya shigo Falon Maryamu tayi masa duba É—aya ta É—auke idanunta a kansa,
Sam ta ƙi kallon inda yake bare su haɗa ido, amma a ranta tana mamakin yanda ya sauya ya rame sosai kamar ba shi ba, ko zuwan su bai kai raman yanzu ba
Shi kuwa ganin akwai Maryamu a wurin, sai bai zauna ba ya wuce wurin Dinnig, da kansa yayi save ya soma cakalar abincin da sam ba ya masa dad'in ci, kawai turawa yake yi amma hankalinsa ba ya wurin, yana can duniyar tunanin da ya saba yanzu
"Dady zan je Katsina a kan gwangilan da na faɗa maka zamu karɓa, Ni zan je mun rigada mun yanke shawara da Bro."
A cewar Hanif da ke duban Dadyn wanda yake gefen sa
Dady yace, "Alhamdulillah, to Allah ya kaimu rai da lafiya ya nuna mana aron kwana."
Dukkan su suka masa masa,
Yayinda Momy take tambayarsa, "da yaushe ne zai tafi? Kuma kwana nawa ne?"
"Da safe ne zan wuce, just one day zan yi."
"To mai kake so in haÉ—a maka wanda zaka tafi dashi?"
"Mom babu komai, kwana É—aya ne fa, bazan jima ba ki bar shi kawai."
Dady da ke murmushi yace, "dama dai SHAREEF ne, shine wanda zai buƙaci wani abun, amma ba Babana ba, duk inda ya tsinci kansa yana ƙoƙarin yin rayuwa irin nasu.
Yauwa. nace ya maganar mu na baya a kan nemo Mata Babana, ka samu ko har yanzu ka manta da zancen ma?"
Dariya yayi yana sosa ƙeya cike da kunya, "No Dad, ina tune wlh."
"Ok akwai daddaÉ—an labari kenan? Don daga ganin bakin nan naka yana motsi akwai labari?"
Dariya kawai yayi bai iya cewa komai ba
"FaÉ—a mana muna sauraron ka, aina yarinyar take? Don ba na son a wuce dogon lokaci ban aurar da ku na huta ba, shi wancan Babban kawai din; ga shi da Mata har biyu amma har yanzu babu wata wacce ta tare."
"Dady yarinyar da muka taɓa taimaka mata ne wacce ka basu gida a Hotoro."
Da mamaki Dady yace, "wai yarinyar nan Kurma ko?"