Sashe 46
Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A washe gari kuma aka tashi da biki gagarumi,
Karfe sha É—aya aka É—aura auren Hanif da Amra
Kayan da Maryamu ta saka duk Momy ta saka a ɗinka mata, duk da a ƙurarren lokaci ne amma kasancewar akwai kuɗi nan da nan aka samu ɗinkunan, da safen ranan bikin aka kawo su kusan kala biyar,
Haka ta dinga saka wannan ta fita wannan dolen ta tunda su Aunty Najwa ne masu shirya ta,
Har makeup É—in nan na zamani aka yi mata sai É—aukar pictures ake yi kala-kala da su Momy,
Itama Maryamu saboda ta ba ire-iren su Aunty Salma haushi waɗanda kallo ɗaya kayi musu zaka ga rashin walwalan su a fili, shiyasa ta saki jikinta tana ta farin ciki komai aka ce tayi sai tayi shi, sabida har a ranta ta ɗauki ɗammaran babu sauran nuna baƙin ciki bare har ta shiga damuwa a kan auren nan, yanda ta shirya wa zuciyarta na ɗaukar fansar abubuwan da SHAREEF yayi mata, Hmm kawai Allah-Allah take yi a kaita ta soma abun da ta ƙulla
Ƙarfe daya bayan an yi sallan azahar, wasu suka ragu suka tafi gidan Maryamun, har da su Inna waɗanda zasu ga gidan kamar yanda Dady yace, "su je su duba komai su saka albarka."
Bayan sun tafi ne aka kira masu kiɗan ƙoroso mata suka yi ta cashe wa
Da wuri-wuri aka shirya tafiya da Maryamu, bayan su Inna sun dawo aka kaita har wurin su suka yi mata nasiha, Umma ce kawai tayi mata faÉ—a amma Inna bata ce komai ba sai fatan zaman lafiya da tayi musu,
Haka aka zagaya da ita wurin dangin Momy suka yi nasu daga ƙarshe aka kaita ɗakin Dady tunda yana gidan,
Sun jima yana mata nasiha sosai before aka fito da ita,
Kaf Æ´an Matan sai da suka bi Æ´an kai Amarya, domin su Aakifah su ne gaba-gaba,
Har aka fice Maryamu babu É—igon kuka ko na kewa a kan fuskarta,
Haka aka tafi da ita gidan ta da ya haÉ—u sosai Dady yayi aiki ba kaÉ—an ba,
Anguwa daya suke da gidan Hanif, sai dai akwai tazaran tafiya don ba kusa bane gaskiya,
Kuma daga Maryamun har Amra shi yayi musu kayan É—aki, set É—in kujeru har biyu, gaskiya gidajen yayi musu na gata ne
Su Mubeena da suka je don ganin ƙwaƙwaf, haushi kamar ya kashe su, haka suka yi ta zagaya gidan suna kallon abun haushi,
Basu baro gidan ba har bayan magriba sannan aka zo aka tarkata su gaba É—aya, sabida ba a son a kwanan mata tunda yanzu an dena wannan yayin
Aka bar Maryamu ita kaɗai babu ɗar bare damuwa don an tafi an barta, tana ganin ma kowa ya watse ta rufe ƙofan ɗakinta ta murza mishi key,
Ta É—auki wayanta ta soma latse-latse, daga nan bata sake jin motsi ba har tayi barci kuwa.***
Shima SHAREEF shi kaɗai ya shigo gidan, don ya ƙi yarda Abokansu su rako su sai dai suka bi Hanif gidan sa,
Kai tsaye É—akin sa ya nema ya shiga, dayake É—akuna biyu aka saka gado, yana duba wa ya ga mai furnitures ya shiga ciki,
A daren ya kira Sadiq ya kwaso masa wasu daga cikin kayan sa ya kawo masa,
Yana tafiya yayi wanka ya saka kayan barci, har ya fita ya duba ɗakin da Maryamu take ciki, ganin a kulle tunda ya taɓa sau ɗaya sai ya juya ya koma ɗakin sa yayi kwanciyar sa, tunda akwai gajiya a jikinsa shima nan da nan barcin ya ɗauke sa, yana mai cike da mafarkan yanda komai ya sauya mishi da kuma yanda zasu zauna da Maryamu.
***
_____Washe gari wurin ƙarfe sha ɗaya su Aakifah suka sake zuwa gidan, har da su Ammee
Suna tafiya shima Hanif yakai Amra gidan su,
Dayake Momy tace mishi, "ya kawo ta su Inna zasu tafi zasu ganta."
Tunda lokacin har sun shirya jira kawai suke yi su ga Amra sannan su tafi, har sun yi sallama da Dady ya sallame su da alkhairai mai yawa,
Motan da zata tafi dasu ma tana cikin gidan an kawo ta,
Bayan sun ga Amran sun sanya mata albarka sannan suka tarkata suka tafi
Sai gidan ya zama daga Momy sai Amra da Hanif É—in,
Don shima zaman sa yayi suna ta hira da Momy,
Amra kuma na zaune a ƙasa tana sauraron su, idan sun yi abun dariya ta murmusa fuskarta rufe cikin Hijabin ta
Sai kusan sallan la'asar su Aunty Hidayat suka dawo gidan,
Shiyasa Momy tace, "in zasu wuce kawai su tafi da Amra gidan su; su Hajiya su ganta."
Tunda babu wacce ta zo bikin, tsufa ya hana su fita ba ko'ina suke zuwa ba
Bayan sun yi Sallah sai suka tafi haraban gidan, Momy ce ta riƙo hannun Amran ta sanya ta a Motan da su Mubeena suka shiga
Bayan sun tafi sai ta koma ciki tace ma Hanif, "idan anjima yayi sai ya je ya É—auko ta su wuce gida.
Kar ya ƙara kawo ta har ta saba da gidan ta tukun zasu sake fita."
Shi dai Hanif dariya kawai yayi, yana zaune suna ta hira, sun jima tare sai da su Aunty Fatima suka dawo gidan sannan ya fita zuwa haraban gidan yana waya da SHAREEF,
Tsokanarsa yake yi yana cewa, "ya ba shi labarin daren su na jiya, Allah yasa dai yana cikin farin ciki komai ya wakana?"
Tsaki SHAREEF yayi yace, "kai fa banza ne, ba na son irin haka wlh."
Dariya Hanif yayi yana shafa ƙeya yace, "to mene ne a ciki? Kawai fa tambaya nayi."
Tsakin ya kuma ja yace, "to babu abun da ya faru don ubanka."
"Lallai, to mai ka tsaya yi? Kai da kake jiran wannan ranan Bro? Yakamata dai a haɓɓaka sunna don Ni tuni na wuce wurin, ka ga sai Matanmu su haihu a lokaci ɗaya wlh, mu saka musu Hassana da Hussaina, ko Hassan da Hussain. Allah ina baka shawara Bro yanzu komai ya wuce damar ka ne, ka daure kayi abun da yakamata."
Shiru SHAREEF yayi masa yana ta zuba, har sai da ya gaji ya kashe wayan sa yana jan tsaki,
Sai dai a ransa shima yana jin bazai iya É—aukan lokaci mai tsayi bai je ga Maryamu ba, don haka shima dole ya angwance a wannan ranan,
Yana É—akin sa a wannan lokacin ya rufe kansa, duk hayaniyar da su Ammee suka yi kafin su tafi yana ji, sai da suka bar gidan sannan ya fita yayi sallan la'asar, already azahar a cikin É—akin yayi don ba ya son ya fita su gansa,
Bai sake fita ba sai da aka kira magriba sannan ya fito,
Motocinsa guda biyu suna nan a fake a gidan kasancewar Sadiq ya kawo mishi,
Fita yayi ya nufi masallacin anguwan yayi Sallah, bayan ya idar yayi zaman sa yana ta faman zikirori da addu'a, tunda a yanzu ya yi wa kansa faɗa sosai, musamman tun sanda ya sauya ya soma addu'a yana roƙon Allah a kan soyayyar Haseena, ya ji dama-dama a yanzu babu ƙuncin da ke tare da shi, duk damuwar da yake yi da ita ya ragu sosai, dalilin da yasa ya ƙara natsuwa kenan ya kama Allah a yanzu ya dena wasa da Sallah ana kira yake yi a kan lokaci, in har ba wani abun yake yi mai muhimmanci ba; ba ya barin lokaci ya ƙure mishi, to Alhamdulillah ya ga sauyi sosai,
Koda ya fito daga Masallacin; har ya shiga gida kuma sai ya ɗauki Mota ya fita, inda suka tsaya a daren jiya Hanif yayi siyayyan Kazan shi, a nan shima ya faka ya siya yau, tunda a jiyan ya ƙi siya kamar yanda Hanif da su Habib suka takura masa, amma yayi banza da su ya ƙi siya a haka suka bar wurin
Bayan ya gama siyayyan ya wuce wani shago ya siya drinks sannan ya nufo gida,
Sai da ya rufe gate ɗin sannan ya shiga cikin gidan riƙe da ledojin a hannunsa, yana shiga Falon nan ma ya garƙame ƙofan sannan ya juya ya nufi cikin Falon.
[25/04, 7:17 AM] Ù†Ùيسة OumÆŠahira: 🌱🌱🌱🌱🌱
*SHAREEF*
_SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱
_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_
*Littafina na kuÉ—i ne, ki biya ki karanta, zaku iya samu na a kan wannan numban wayan. 07065334256.*
__________
*BOOK2*
_______________*PAGE24*
_____Maryamu tuni ta gama shirin barcin ta; ta sanya sleeping dress riga da wando masu taushi kalan lemon green, ta ɗaura hulan zaren lilo baƙi a kanta, tana kwance tana latsa waya ta ji bugun ƙofa,
Hakan ne yasa ta dakatar da abun da take yi tana duban wurin ƙofan, ta san dai bazai wuce SHAREEF bane tunda ta san su kaɗai ne a gidan, kuma tana jin fitan Motansa da dawowarsa, shiyasa ta ja dogon tsaki ta ƙi miƙe wa bare ta buɗe ƙofan, haushi da takaici ya cika ta; a ranta tana tunanin abun da zai yi mata har yake iya buga mata ƙofa,
Jin ya ƙi dena wa sai ta miƙe a fusace ta nufi ƙofan, tsaya wa tayi a wurin ta ɗaga murya tana cewa, "wai waye ne?"
Shiru SHAREEF yayi kamar bazai yi magana ba, sai kuma yace, "ki buÉ—e ki ga waye."
"Bani da lokacin ka, mene ne kake buga min ƙofa ka hana Ni saƙat bare nayi barci?"
"Ki buÉ—e sai ki ga mene ne."
A tsiwace tace, "bazan buɗe ba, ka ga; na fa san mai kake biɗa a wurina, to bari ka ji duk maitan ka da nacin ka wlh baka isa ka samu abun da kake so ba, domin Ni Maryamu na fi ƙarfin ka sai gani sai hange, kabar ganin an kawo Ni cikin gidan ka kayi tunanin zaka mayar da Ni abun biyan buƙatarka tunda ban san abun da nake yi ba, to ka cire tunanin nan a ranka har abada baza ka taɓa samun abun da kake so ba, kai baka ji kunya bama? Wacce ka tsana kake ƙyamata kashi ma ya fi ta a wurin ka; amma don rashin imani da rashin tausayi ka zo nan domin neman buƙatar ka."
"Ni kike fada wa wadannan maganganun?"