← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 75

Sashe 64

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi kuma Hanif sai ya samu damar ci gaba da zantukan sa yana ƙara ba shi shawarwari masu kyau,
Daga baya ya faÉ—a masa, "shima yanzu ya zo zai karisa wannan ayyukan da ya rage masa, daga nan zai wuce gidansu ya É—auki Amra tunda ya kaita wurin Momy, daga asibiti suke ya ajiye ta a can."

Dalilin da yasa SHAREEF ya zauna kenan yana jiran sa tunda yace, "zai bi shi su tafi tare."

Bayan ya gama aikin suka fita kowa ya hau nasa Motan, sun É—an jima ma tunda sun yi magana da wasu daga cikin ma'aikatan nasu,
Daga nan suka wuce can gidan su

Daga Amra sai Momy a zaune a falon suna ɗan taɓa hira kaɗan -kaɗan suna kallo

While Dady kuma sai ya basu wuri yana É—akin sa shima yana É—an dube-duben sa a computer

Bayan sun shiga da sallama, Momy ta amsa musu ta bi su da kallo face ɗin ta da murmushi, don yanzu ba ƙaramin sha'awa suke bata ba in ta ga sun taho tare, musamman yanzu kasancewar sun yi aure sun yi nesa da su, sai suke bata sha'awa in suka shigo a tare, farin cikin ta ma daban ne,
Bayan sun zauna ta amsa gaisuwar su da suka yi mata, sai take cewa, "Ina ka baro min Maryam kai baka zo da ita ba? Yakamata dai ka kawo ta mu gaisa tunda na ga alamun sai mun yi magana, tunda aka yi aure har yanzu kafarta bai shigo gidan nan ba, ai tayi haƙuri wlh da wannan ƙorafin nata, ga Hanif nan ya kawo nasa har sau biyu, kar dai a ce Matar kulle zaka zama da ita?"

Dariya suka yi su dukka har SHAREEF da ba kasafai yake yi ba,
Sai ya shagwaɓe fuska yana cewa, "kai Mom, wannan ƙorafi haka? But dukka-dukka yaushe muka yi auren? Ai Ni na fi Hanif hankali shiyasa ban kawo ta ba, baza ki haɗa mu tare ba."

Dariya suke yi har Amra wacce ta duƙar da kanta kamar ba ta a wurin

Mom tace, "eh ka fi sa hankali tabbas, na ga alama yanzu ka soma hankali."

Sosai SHAREEF ya kwaɓe fuska kamar zai yi kuka yana kiran sunan ta

While Hanif sai ɓaɓɓaka dariya yake yi, yace, "Momy kina so ki dawo da shagwaɓan wannan bawan Allan fa."

"Eh, ai abun da nake son gani kenan don na rabu da ganin shagwaɓan sa, gwara ya koma min SHAREEF ɗina mara jin magana in ɗan ja kunnen sa; don na yi kewar wannan halin nasa."

Dariya dukka suka yi,
SHAREEF kuma yana shafa ƙeya har yanzu da murmushin a kan face ɗin sa, sai dai ya ƙi cewa komai ne don akwai Amra a wurin shiyasa ya ƙyale su suka yi ta tsokanarsa,
Sai da abun yayi masa yawa ne ya harari Hanif yace, "ya ishe ka fa, kayi main shiru haka, in ba haka nan ba zan fasa bakin ka."

Fitowar Dady da maganar sa shi ya hana su ci gaba da hiran nasu, ya sauko da É—an jaridar sa a hannu, wayansa na gaban rigan jallabiyarsa, fuskarsa a sake yake cewa, "wai dariyan me nake ji ne ya cika min kunne? Mai ake tattaunawa ne babu Ni a ciki? To a dawo farko tunda gani na fito."

Har Amra sai da ta É—an dara sabida maganar Dadyn,
Dayake tana kusa da Momy ne; dalilin da yasa ta miƙe kenan ta koma ƙasa wurin ƙafan Mijinta tayi zamanta a wurin, still kanta a ƙasa ta rufe jikinta da hijab, kwata-kwata ta kasa ɗago kanta sabida kunya da kuma rashin sabo da su, but tana sauraron zantukan nasu da suka ci gaba da yi gunun ban sha'awa da burge wa irin na iyalai masu farin ciki,
Ita dai sai dai tayi murmushi babu bakin magana ko an sako ta,
Dayake Momy ne ma ko Dadyn suke sako ta a zancen nasu

Har Dady yana cewa, "ta saki jikinta sosai fa, nan ba a baƙunta don a yanzu ya ci a ce ta saba da su, ita ƴa ce a wurin su kar ta takura wa kanta."

Duk da sun san bata magana amma sai sun ja ta a cikin zancen nasu suna raha da dariya

SHAREEF ne ma daga farko bai cika yin maganar ba don ganin akwai baƙuwa a cikin su, amma kuma daga baya tuni ya ware ya manta da ita yana zuba zancen sa da shagwaɓar da ya saba yi wa Momy, don tun farko yana jin sa kamar shi ne Auta,
Bare yau ya samu abun da yake so ta biye masa ba kamar baya da ta É—auke masa wuta ba

Wannan hiran ne ya ja hankulan su; basu tashi ba har sai da aka kira magriba, wani ɓangare na zuciyar SHAREEF yana can ga Maryamu; don yau ne kaɗai ya samu fita har ya daɗe haka yayi nisa da ita, tun bayan shan Angoncin sa sai yau ne ya fita ya jima haka, ya san cewa dole tana can tana kewarsa, ya so kiranta kuma bai kira ba har suka yi sallan magriba zasu tafi

Bayan sun yi sallama da iyayen nasu suka É—an musu nasiha before suka fito,
Amra tuni ta shiga cikin motan Hanif, shi kuma ya tsaya da SHAREEF a wurin motan suna sake tattaunawa a kan matsalarsa,
Yana sake ba shi shawaran dagewa da addu'a komai zai wuce ya manta da ita

Shima dai SHAREEF ya yarda da maganganun Hanif da yake cewa, "ba haka ta bar shi ba, ta yiwu akwai abun da tayi masa."
Don haka har zuciyarsa ba ya jin daÉ—in abun da ya aikata yau, da kuma yawan tunaninta da yake yi, zai so ya rabu da ita na har abada tunda yana da Maryamu, ita kaÉ—ai ta ishe sa, bazai so ya juya mata baya ba, da É—an hankalinsa yanzu a jikinsa yana ji a ransa ci gaba da son Haseena ba alheri bane, bata da wani amfani a tattare da shi

A nan ma sai da suka ɗan ɓata lokaci kamar shuɗewar mintuna sha biyar, before suka rabu kowa ya hau nasa motan suka fice

Har a cikin mota SHAREEF addu'a yake yi ya kama hasbinallahu wani'imal wakeel, da la'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalumin, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Yana tayi a zuciya a haka har yakai gidan sa

Kwana biyu kenan da saka mai gadin su a bakin gate É—in, wani É—an magidanci ne wanda yake musu gadin,
Shi ya buɗe masa sannan ya rufe ƙofan, tun a bakin gate ɗin yayi masa gaisuwa sabida halin SHAREEF ne har yanzu bai canza ba, ɗabi'ansa ne na wulakanta mutane kowa ba kowa bane a wurin sa, kawai kayi masa aiki shine abun da ke tsakanin ku da shi, dole in ka zauna dashi a rana ɗaya sai ka gane halin sa na halin ko in kula da rashin damuwa da mutane, uwa uba wulaƙanci idan ka shiga gonansa,
Don haka tun ranan farko da mai gadin ya buÉ—e masa gate, sai ya bi sa har wurin mota yana masa gaisuwa da kirari

Nan kuwa ya haɗe fuska cikin nuna isa da gadara ya nuna masa, "ba ya son hakan, ba gaisuwa ya kawo sa yayi masa ba, aikin sa kawai zai yi, idan kuma yace zai riƙa takura masa zai kore sa a aikin ya kawo wani, bai son damuwa."

Ai tun daga ranan mai gadin ya yi wa kansa karatun ta natsu, dama kwaÉ—ayi ne da son samun gindin zama, tunda ana labarin wasu Iyayen gidan irin haka kuna girmama su sai ka ga sun É—auke ka da muhimmanci suna É—an maka ihisani, ashe ba haka bane a nan, don haka ya shiga taitayin sa, nan babu fuska bare ya samu na banza

Shigan SHAREEF cikin gidan sai ya rufe ƙofan, sannan ya nufi hanyar ɗakin Maryamu ganin babu kowa a Falon; A nan a yashe a tsakar ɗakin ta ya hange ta,
In quickly ya ƙarisa inda take yana kiran sunanta, gabansa ba ƙaramin faɗuwa yayi ba da ya ganta a hakan, hankalin sa lokaci ɗaya sai ya tashi ya ruɗe yana faman kiran sunanta da ƙarfi, yayinda tuni ya sanya hannayensa biyu ya ɗago ta and yana girgiza ta

Sai dai Maryamu babu inda nata ke motsi

Idan hankalin sa yayi dubu tabbas ya gama tashi a wurin, halin ruÉ—ewan da ya shiga a time É—in bazai iya faÉ—uwa ba,
Amma tuni ya ɗago ta ya miƙe da saurin sa zuwa waje, ko tunanin ma ya watsa mata ruwa bai yi ba, kai tsaye motansa ya koma ya saka ta ya shiga ya danna horn tun kafin ya isa bakin gate

Tuni Mai gadi ya fito daga ɗan ƙuryan ɗakin sa ya buɗe masa gate ɗin

Yayinda ya fige motan ya fice ya nufi da ita asibiti, yanda yake sharara gudu nan da nan ya isa asibitin,
Yana tsayar da motan ya soma ƙoƙarin fito da ita; yayinda zuciyarsa ke sake buga wa da ƙarfi tsoro ya cika sa sabida ganin halin da Maryamun take ciki, musamman da ya ji babu inda nata ke motsi jikinta yayi sanyi tamkar bata da rai a jikinta, wannan dalilin ne yasa duk ya ruɗe ya ruga da ita cikin asibitin yana faman kiran nurse's

Dayake asibitin su Doctor Abbas ya kawo ta, a time É—in ya fito kenan daga wani ward, ya hangi SHAREEF yana gudu da Maryamu a hannu, dalilin da yasa ya nufe sa kenan shima yana kiran sunan sa

Da sauri SHAREEF ya juya sabida jin muryansa, sai kuma ya isa gare sa yana cewa, "doctor, help me, help..."
Abun da yake furta wa kenan maganar nasa ta ƙi gaba bare baya

Doctor Abbas kallon yanda Maryamun ta nanƙwaye yayi; kanta yana kallon ƙasa kamar mara rai, sai nan da nan yace masa, "ya biyo sa zuwa office."

A baya ya bi sa ƙafa da ƙafa suka shiga office cikin sauri,
While SHAREEF tuni ya kwantar da ita a saman gadon mara sa lafiya yana tsaye a wurin
Chapter 64 · 0% Book details