← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 75

Sashe 22

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana koma wa É—aki ta kira Nana video call,
Cikin damuwar da ya bayyana a kan face É—in ta tace, "Nana, please understand me, Ni dai bazan iya bayar da Iyayena ba, ke ne kika saka ni a cikin ku ba tare da amincewa na ba, and yanzu kuma sai ku ce dole sai na bada iyayena a kan me? I can't gaskiya, but you choose kowaye nayi alkawarin zan baku ban da my parents."

"Wani killer smile Nana ta saki before tace, "kin san mutanen da muka sadaukar a kan cikan burin mu ne baby? Dukkanmu babu wanda bamu bayar da Æ´an uwa da Abokanmu ba, wannan shi ne sharaÉ—in kungiyar, kuma idan har kina so ki ci gaba da kasancewa cikin farin ciki to dole sai kin bi abun da aka ce miki, just iyayenki za ki bayar fa, ko ba ki bada su ba zasu mutu wata rana, think babyna yanzu da dayanzu ba É—aya bane a cikin rayuwarki, i know yanzu kin gane abun da nake nufi da ke, ke kanki baza ki so ki rasa komai ba a yanzu."
Sai tayi dariya ta ƙara da faɗin, "baby ko ba ki amince ba dole za ki rasa ɗaya daga cikin su, gwara tun wuri before time ya ƙure ki yanke hukunci, after parents you can give everyone in your family wanda ku ka fito ciki ɗaya."

Gabanta ne ya faɗi sabida jin abun da tace, kenan zata iya sadaukar da ƴar uwanta Haajara? No ina bazai yiwu ba! Dukkan su tana son su baza ta iya ba, shiyasa kamar zata yi kuka tace, "Honey wlh bazan iya ba, su ɗin duniyata ne, ina matuƙar sonsu, bazan iya sadaukar da iyayena da kuma ƴar uwata guda ɗaya ba, na shaƙu dasu, su ne komai nawa, tun farko ba Ni na kawo kaina harkan ba, ke kika saka ni, meyasa baza ki taimake Ni ki cire Ni ba? domin bazan taɓa bada jinin iyayena a sha ba, No I can't bazan iya ba wlh, zan iya bada kowa ban da su, meye jin daɗin to babu su a raye?"

Dariya Nana tayi tace, "Ni yanzu i have something to do, Ni dai na faÉ—a miki ki yanke shawara É—aya before mu je meeting, domin a cikin su dole za ki bada É—aya, idan kuma ba haka ba ke za ki mutu baby, Ni kuma bazan bari ki mutu ba."
Sai tayi wannan shu'umin murmushin nata mai fassara da dama, take ta kashe kiran bata jira cewar Haseena ba

Wadda tabar ta cikin zullumi da tashin hankali, tunda ta ambaci meeting shiyasa ta ƙi yarda ta kwanta sabida ta san cewa da zaran ta kwanta dole zata ganta a can, domin sau da yawa hakan ke faruwa da ita sai dai komai ya faru da ita kamar a mafarki ta ganta a cikin su, bata taɓa takawa ta je da ƙafafunta inda suke ba, sai dai idan ta kwanta barci tayi mafarki, kuma har ga Allah a wannan lokacin bata da kwanciyar hankalin da zata yarda tayi wannan barcin, bazai yiwu ta bada iyayenta ba,
Wannan abun ne yasa gaba ɗaya Haseena ta shiga cikin wani hali da sam walwala ya ƙaurace mata

Su kansu su Umma sun fahimci halin da take ciki, amma koda suka tambaye ta sai tace musu, "kawai gajiya ne, ba ta jin daÉ—in jikinta."

Umma tace, "ta je ta kwanta mana tunda kwanciya tace zata yi but ta fito."

Amma ta nuna sam a'a, a wurin ta kwanta saman dogon kujera sabida kar barci ya ɗauke ta, tana ta saƙe-saƙe a cikin ranta don samun mafita, ita dai ta jefa kanta ga halaka, at most of the time tana yin dana-sanin zuwan ta karatun nan, wani lokacin kuma sai hankalinta ya gushe musamman da ta soma jin daɗin rayuwarta tare da sauyin da ta samu a tattare da ita, takan rasa mai ke damunta wani time ɗin, idan zata yi tunani mai kyau sai kuma zuciyarta ta ƙeƙashe tunaninta ya sauya gaba ɗaya, bata san meyasa ba, amma a yanzu tana dana-sani don wlh baza ta taɓa bada iyayenta ba ko mai zai faru, tayi alƙawari duk wanda suke so a faɗin duniyar nan zata iya mallaka musu amma banda iyayenta da ƴar uwanta ɗaya tilo

Tana nan kwance kiran SHAREEF ya shigo wayanta,
Amma tsaban damuwa yayi mata yawa ta kasa É—auka sai ma saka ta a silent tayi, yayi ta kira bata san ma yana yi ba sai da Haajara ta kawo mata nata wayan, ta faÉ—a mata, "SHAREEF ne ya kira yana nemanta."

Bata ce komai ba ta amshi wayan ta wuce É—akinta.
[03/04, 10:48 AM] نفيسة OumƊahira: 🌱🌱🌱🌱🌱

       *SHAREEF*
           _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱

_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*Littafina na kuÉ—i ne, ki biya ki karanta, zaku iya samu na a kan wannan numban wayan. 07065334256.*

__________
*BOOK2*
_______________*PAGE12*
_____Tun before ta shiga É—akin nata ta amsa call É—in, sannan ta shiga ta zauna a saman bed É—in ta tana yin shiru da sauraron abun da yake furta wa

Daga can other side SHAREEF kamar zai yi kuka yace, "Sweetheart What's going on? I called you and you did not pick up the phone, or there is a problem?"

Sai da ta lumshe idanu ta buÉ—e, tana daidaita yanayin ta before tace, "No dear, kawai ina kwance ne sabida gajiyar hanya, kuma wayan tana silent ne that's the reason."

"Hmm har kin sa na ji sanyi a raina, so ya kike? I hope komai normal ko? Na so ina kusa da sai in saukar miki da gajiyar, I didn't get to come, ina fata ba ki yi fushi ba?"

Murmushin gefen baki tayi tare da kwanciya a saman gadon, a cikin jan hankali ta ba shi amsa, "No ban yi fushi ba, ai ba na fushi da kai dear, ka wuce wannan a wurina, i don't care da zuwan ka bcus na san zaka zo ne."

"Yauwa sweetheart Thank you for believing me, I will come after Isha prayer, sai ki tanada min abu mai daÉ—i da tsarabana."
Yayi maganar cikin kashe murya cike da ƙaunarta a rai

in ten minutes they talked on the phone and ended up in love,
Bayan sun gama sai Haseena ta kwanta a nan bata fita ba duk da ba barci take yi ba. Amma kuma ta kasa tashi sabida mugun nauyin da jikinta yayi mata; tamkar ana danne ta, tun ba ta jin barcin har wani nannauyan barci ya zo ya sure ta batare da ta shirya ba,
Sai tsintan kanta tayi cikin ƙungiyar su tana gurfane gaban Ogansu da ke zaune a saman dogon kujerar sa,
While sauran member suna tsaye sun yi musu ƙawa sun zagaye su sanye da jajayen kaya,
Daga ciki har da su Nana sun yi cirko-cirko suna kallon Haseena da ke faman zare ido

Ogan su da ke cike da fushi yake kallon wurin da Haseena take, cikin tsawa da amon murya yake furta maganar da turanci, "saƙon ki ya iso gare mu, sai dai kina gab da ki amshi mummunar hukunci in har kika nuna bijirewa a tare damu, don haka ki yi gaggawar yanke hukunci yanzu domin bamu da lokacin ɓata lokaci, wa kika zaɓa a cikin su?"

Gaba É—aya jikin Haseena rawa yake yi sabida kiÉ—ime wa da tashin hankali, jikinta na rawa sai dai girgiza kanta take yi domin har a lokacin ba ta jin zata iya bada wani nata a kashe mata shi, never baza ta iya ba

Kece wa yayi da dariya yana kaɗa sandan hannunsa, "kina ɓata mana lokaci Haseena, ba wai zamu tsaya muna sauraron ki bane a nan, idan kika yi mana gardama zamu halakar da ke yanzun nan, sai dai kina da zaɓi da dama na wani lokaci, ki yi gaggawar sanar mana da wanda kika zaɓa, domin kuwa muna buƙatar shan jinin sa a yanzu."

Jin Haseena ta ƙi yin magana har yanzu, sai faman girgiza kanta take yi tana kuka tana son magana but ta gaza,
Tuni Nana ta isa wurin ta tana duƙa wa a gabanta tare da faɗin, "please Haseena choose one, ba ki da lokaci da za ki ɓata mana time, akwai buƙatar a sha jinin nan yanzu if not; za ki fuskanci gagarumar matsala, kuma ba na son in rasa ki. Look Haseena."
Ta kamo hannunta cikin lallami tana sake cewa, "Please ki zaɓi ɗaya shikenan fa. Hurry up, please don't waste time, you will slowly forget everything, baza ki yi maraichi ba, ki duba daulan da kike ciki Haseena, you need to be happy, everything will pass tamkar ba a yi ba."

Daƙyar Haseena ta iya buɗe baki ta zaɓi ɗaya, shima sai da ta ga Ogan nasu ya fusata an soma juya ta za a gana mata azaba, shiyasa bata da zaɓi face miƙa wuya, kawai sai ta miƙa ƴar uwanta Haajara

Nan take Ogan ya fashe da dariya, sai ga wani hayaƙi ya soma fitowa ta cikin bakin sa, muryansa mai fita bibbiyu ya ba Nana umarnin ta miƙa mata sweet ɗin da zata ba Haajara ta sha a yau din nan, ta tabbatar tayi aikin nan kafin mintina goma su cika

Daga nan Haseena ta farka a gigice ta haɗa zufa kashirɓan kamar wacce aka tsamo ta a cikin ruwa, babu inda jikinta ba ya rawa tsaban kiɗima da zallan tashin hankali,
Tana duba hannunta ta ga sweet É—in ajiye,
Wani irin kuka ne ya kufce mata tana furta, "Na shiga uku Ni Haseena, me nake yi haka? Wacce ƙaddara ce ta sa na shigo duniyar nan? Wlh bazan yarda ba, bazan iya ci gaba da kasancewa cikin mutanen nan ba, bazan iya ba, duk yanda za a yi sai na fita, ƴar uwata baza ta mutu ba, babu wanda zai mutu a cikin su."
Kuka kawai take yi tana sambatu kamar zata shiÉ—e,
Bata san cewa kukan nata yana fita da sauti sosai ba
Chapter 22 · 0% Book details