Sashe 25
Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_____Zuwa washe gari aka yi jana'izar Haajara aka kaita makwancin ta, wadda mutuwar ba ƙaramin girgiza ahalin ta yayi ba in ka cire Haseena a cikin su, tabbas mutuwar farat ɗaya abun kokawa ne, bare kuma budurwa ƙaramar yarinya like her
Haka aka ci gaba da karɓan gaisuwa koyaushe su SHAREEF suna zuwa gidan,
Dalilin da yasa ma basu bi takan mutanen da Mahmud ya tabbatar musu a halin yanzu suna hannu bA
Ƙarshe dai Hanif ne ya je wurin su shi da Mahmud suka tuhume su a kan laifin da suke tuhumar su dashi,
Da farko basu samu abun da suke so ba sai da suka gana musu azaba sannan suka faÉ—a musu gaskiya,
Hanif yayi musu video a lokacin da suke maganar, sannan ya tura ma SHAREEF
Sai da SHAREEF ya gani ya duba ya tabbatar sun samu abun da suke so, sannan yace, "su miƙa su wurin ƴan sanda su shigar da ƙara, shima yana nan zuwa before su wuce."
Bai bar wurin ba sai da ya samu ganin Haseena domin ya ga halin da take ciki, don ya damu da ita sosai, tun ranan sau É—aya suka sake haÉ—uwa; ga shi har yau kwana uku kenan, ko wayanta ba ya samu ko ya kira ba ta É—auka, dalilin da yasa yake damuwa kenan duk da yana mata uzuri sabida halin da take ciki,
Amma koda ya ganta yau ya ji daÉ—i sosai don bai zaci zai ganta ta washe sosai ba, kamar ba ita ba, har farin cikin sa ya yalwata yana ta jin daÉ—i
Dayake akwai mutane a falon Abban nasu, bai ja lokaci ba yayi mata sallama ya wuce, a cewar sa; "zuwa gobe zai sake dawowa."
Daga nan station ya wuce a can ya tarar da su Hanif, lokacin sun gama shigar da ƙaran suna tattaunawa da DPO,
SHAREEF yace, "ba ya son a ɗauki lokaci mai tsawo don suna da hujja a hannunsu, a gaggauta danƙo su Alh. Inuwa a miƙa su kotu, a can zasu biya abin da suka yi."
A ranan kuwa aka je har gida aka taho da Honourable Ja'e, don shi kaÉ—ai aka samu a gida, Alh. Inuwa ba ya nan yana Abuja,
Don haka suka tura masa saƙon dawowarsa nan kusa sabida ƙaran da aka shigar a kansu
Duk da hankalin su ya tashi da jin wanda ya shigar da su ƙara, but basu wani ɗaga hankali sosai ba, sabida sun san babu ta yanda za a yi su bari SHAREEF ya ci galaba a kansu, suna da hanyar da zasu bi wajen ganin bai samu nasara ba,
Ko kusa basu yi tunanin an kama mutanen da suka saka aiki ba, don haka a washe gari Alh. Inuwa ya dawo garin,
A ranan kuma aka je aka taho da Shuraihu da wasu mutane biyu da suka yi ɓarnan; masu aiki a Companin SHAREEF, tunda sunan su duk ya fito a bayanan mutanen da aka kama,
Nan fa ido ya raina fata don basu taɓa tunanin har haka SHAREEF ya samu hujja ba,
Sai dai a cikin su babu wanda ya amsa gaskiya sun ƙaryata bayanan da mutanen suka faɗa
Inda aka shigar da maganar kotu zuwa gobe za a yi zama kamar yanda SHAREEF ya buƙata
Duk wannan abun Dady bai da labari sai da Hanif ya sanar mishi da komai a yau,
Yayi mamaki da al'ajabin maganar, kuma hankalin sa ya tashi matuƙa da ya ji dalilin da yasa suka yi asarar kayan,
Sai yace ma Hanif, "ya kira SHAREEF yanzu ya zo ya same shi."
After ya zo Dady yace, "wai dama abun da ke faruwa kenan SHAREEF baka taɓa faɗa min ba? Why?"
Shiru SHAREEF yayi bai ce komai ba
"Kenan ta sanadiyyar samun gwangilan nan ne har suka ƙona mana kaya muka yi asara? Meyasa tun farko ka dauki abun nan da zafi tunda har sun nuna suna son hannun jari a ciki; why baka basu ba?"
"Dady, ba Ni na hana su hannun jari ba, already mu aka siyarwa daga baya suka shigo cikin maganar, and Ni a ganina kowa yana bukatar ci gabansa; don me zan ɗauki ɗaukakan mu in ba wasu after all bamu rasa kuɗin da zamu iya siyan hannun jarin ba? Mutanen nan suna adawa da mu ne ba sa son ci gabanmu, duk inda suka ga zamu ƙaru sai sun shigo ciki, don me zan bar su ina gani suna son komar da mu baya bazan ɗauki mataki ba?"
Girgiza kansa Dady yayi duk da ransa ya ɓaci sosai, sai yace, "amma SHAREEF ba a yin haka a Kasuwanci, ka kasance mai haƙuri da so wa ɗan uwanka abun da kake so wa kanka, idan da ace tun farko ka ɗauki wani abu daga ciki ka basu; da duk hakan bata faru ba, hakan bazai rage ka da komai ba SHAREEF, shi yaƙi ɗan Zambo ne; haka kasuwanci ɗan haƙuri ne, akwai faɗuwa akwai samu, ka ga sabida haka ga abun da suka aikata mana, nan gaba bamu san mai zai faru ba, a hakan da kake ganin ba komai ba sai ka riƙa tara maƙiya; daga ƙarshe su kaika su baro, Ni yanzu ban san ma me zance ba sabida abun yayi muni da yawa, tun farko da na sani zan ce mubar su da Allah ne kawai, duk abun da Mutum yayi ya yi wa kansa ne, ka dena cewa sai ka rama komene ne aka yi maka, ka zama mai yafiya SHAREEF, don Allah ka sauya wannan halin naka ba na son kana ɗaukan zafi a kan irin wannan matsalolin na rayuwa; wanda mun san cewa babu wanda ya fi ƙarfin Allah ya jarrabe shi, babu wanda yake wuce ƙaddaransa,
Kai kuma har da kai ka biye masa Hanif; ina ganin ka da ɗan sauƙin kai, ban ji dadi ba wlh, kar ku sake yin abu makamancin irin wannan kuyi shiru baku sanar min ba, waɗannan mutanen manyan mutane ne, yanzu idanun duniya zasu dawo kanmu, ba na so kun ji ko?"
Gaba ɗayan su gyaɗa kansu suka yi; duk da shi SHAREEF bai ji daɗin yanda Dady ya ƙi goya musu baya ba, a ganin sa ai haƙƙin su ne, idan ba a koya ma ire-iren waɗannan mutanen hankali su shiga taitayin su ba; to nan gaba abun da zasu yi sai ya fi haka, yanda suka shuka tsiyan su dole su girba, ba su zasu yi asara ba; su da suka assasa gobaran su zasu girbi abun da suka shuka, kawai su biya su shine kwanciyar hankali
Dady shi kuma nasiha ya dinga musu sabida shi har ga Allah bai ga amfanin abun da su SHAREEF suka yi ba, ai duk wanda ya cuce ka shi da Allah ne, ba ga shi ba duk da asaran da suka yi basu faɗi ƙasa ba, Allah na buɗo musu ta hanyoyi da dama, ba wancan dukiyar shi ne kaɗai abun da suke dashi ba, tunda daɗin abun akwai inda zasu biya wata rana, kowa bazai shuka mugunta sannan yace hakan ya tafi a banza ba, dole zai girbe sa ko a gaban Allah; ko wani iftila'in ya faɗo musu.***
A washe gari aka yi zaman kotu aka gabatar da tuhumar da ake musu, sun so musawa amma ganin videon nan, da kuma koro jawaban da mutanen nan suka sake yi, hakan yasa dole su Honourable Ja'e suka amsa laifin su, kuma suka faÉ—i dalilin da yasa suka yi haka
Babu ɓata lokaci Alƙali ya yanke musu hukunci kamar yanda suka saka su asarar duk kayan da suka rasa, zasu biya su a nan take babu jingirta wa,
Sannan da kuma taran da aka ci su sabida gobaran da suka assasa haka kawai, idan da a ce Allah bai tsayar da abun a haka ba; da ba a san halin da ake ciki ba a yanzu, maybe ma har a rasa ran wasu mutanen,
Don haka ba ɓata lokaci aka basu damar su biya shi
Cikin baƙin ciki da takaici haka su Honourable Ja'e suka biya maƙudan kuɗaɗen nan da basu dashi a wannan lokacin,
Tunda sun bayyana basu da halin biya
Yayinda SHAREEF ya miƙe ya basu damar, "zasu iya siyar da hannun jarin su, shi kuma zai siya babu ɓata lokaci, in sun amince yanzu a yi ciniki."
Haka kuwa aka yi, komai ya tafin ma SHAREEF yanda yake so, sai jin daɗi yake yi yau ya samu abun da yake so, ya ci galaba a kan maƙiyansa, mai ya fi wannan daɗi?
A kullum farin cikin kasancewar sa mai Nasara, idan har zai yi nasara a kan maƙiya ya ga baƙin cikin su, hakan ya fi masa komai daɗi, ga shi kuwa yau ya saka su sun yi nadamar abun da suka yi, musamman yanda idon mutane yake kansu duk wani mai ganin su da mutunci; manyan mutane da alhazzai suna ganin abun da ke faruwa,
Yaro Karami ya gama da su, ya ci musu mutunci ya tozarta su a bainar duniya, wanda basu taɓa tunanin hakan ba, tabbas SHAREEF ya shammace su.
[06/04, 12:16 PM] Ù†Ùيسة OumÆŠahira: 🌱🌱🌱🌱🌱
    *SHAREEF*
      _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱
_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_
*Littafina na kuÉ—i ne, ki biya ki karanta, zaku iya samu na a kan wannan numban wayan. 07065334256.*
__________
*BOOK2*
_______________*PAGE14*
_____Tun sati ɗaya da rasuwar Haajara; Haseena ta so ta tafi, sabida tamkar a ƙaya take jin ta, baza ta iya dogon kwanaki babu Nana a tare da ita ba, baza ta iya zama a nan babu ita ba sabida tsananin kewa da buƙatar ta, domin ita kanta Nanan kullum sai ta dame ta a kan ta dawo,
Har cewa tayi ma, "in har bata dawo ba zata biyo ta nan."
Amma sai Haseena ta dakatar da ita tace mata, "zata dawo nan kusa ta bata lokaci."
Bata sanar da iyayenta zata tafi ba a washe gari bayan kwana bakwai, sai da ta haÉ—a kayanta sannan ta sanar musu zata wuce, bayan tayi musu karyan, "ana neman su da gaggawa ne a kan karatun su."