← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 75

Sashe 27

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru yayi ya sunkuyar da kansa ya kasa cewa komai, to mai zai ce? bai da bakin magana, yanzu Haseena ta sare mishi gwiwa, abun da take mishi yana matuƙar ƙona mishi rai, bai taɓa tunanin zata ci amanarsa ko ta nuna mishi halin ko-in-kula irin wannan ba, abun baƙin cikin kuma ba ya son kowa sai ita, ba ya jin zai iya zama da wata Mace bayan ita, bare wancan yarinyar da ya tsana, tun farko bata yi masa bane, hasali ma ba shi da ra'ayin Mace baƙa irin ta, ga kuma abubuwan da tayi masa, a ganin sa sam bata da kamun kai tunda har zata iya nuna soyayyarta a gare shi bayan ba shi yace yana sonta ba, bata yi masa ba sam, zai iya zama da kowacce Mace ban da ita,
Shiru yayi kawai yana sauraron Momy wacce ta dage sai faÉ—a take mishi amma bai ce uffan ba, don yanzu magana ma wannan wahala take mishi, halin da yake ciki ya ishe shi,
Bai ce mata uffan ba har ta gama suka sauya hiran su ita da Hanif, yana zaune tamkar wanda yake sauraron su amma hankalin sa kacokan ba ya wurin su, ya mayar da kansa ya kwantar idanunsa a buÉ—e ya tsira wa sama ido yana faman tunani

Sadiq kuma na gefe saman one sitter yana ta faman latse-latsen laptop, shima hankalinsa ba ya gare su, ta aikin gabansa kawai yake yi

Sai da aka kira magriba sannan suka tashi gaba É—ayansu suka É—aura alwala suka wuce Masjid

Sai bayan magriba shima Dady ya dawo gidan,
Bayan sun je sun yi sallan isha'i suka zauna hira but ban da SHAREEF kamar koyaushe, shi ya soma zuwa ya ci abincin sa sannan yayi musu sai da safe ya wuce É—akin su

While su kuma suka zauna hira sai kusan ƙarfe tara before su hau kan Dinnig su ci abinci,
A lokacin ne ma Momy take sanar musu da zuwan Maryamu sati mai zuwa idan sun samu Hutu, zasu zo gaba É—aya har da su Ammee.
*** *** ***

_____Bayan su Maryamu sun samu Hutun su, gaba ɗaya suka tarkato sai ga su sun dira a Kano da ƙarfe biyu na ranan Alhamis.
[08/04, 5:20 PM] نفيسة OumƊahira: 🌱🌱🌱🌱🌱

       *SHAREEF*
           _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱

_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*Littafina na kuÉ—i ne, ki biya ki karanta, zaku iya samu na a kan wannan numban wayan. 07065334256.*

__________
*BOOK2*
_______________*PAGE15*
_____A ranan SHAREEF bai je ko'ina ba, tunda yanzu bai cika zuwa aiki ba sai jifa-jifa sabida yanayin jikinsa, don a yanzu bai cika lafiya ba,
Yana kwance a É—akin sa yana sharan barci, duk bidirin nan da aka yi na zuwan su Ammee bai da labari,
Lokacin har su Aunty Zainab sun zo sun tafi ma bai sani ba,
Yana kwance sai kusan ƙarfe huɗu sannan ya tashi,
Jiki a mace ya miƙe ya wuce cikin toilet, wanka ya soma yi before ya ɗaura alwala, ya fito ya shirya kansa cikin baƙin wando da jan t.shirt wadda ta ɗan sakin masa bata kama sa ba; kuma tana da kauri da dogon hannu, wurin mirror ya nufa ya tsira wa kansa ido yana kallon yanda ya koma, yanda ka san wanda yayi jinyar watanni haka ya koma, don ma gashin da ke face ɗin sa ya rufe masa ainihin raman da yayi, sajen sa ya fito sosai yayi tsawo, haka ma gemun sa kamar wani Balaraben Ustaz haka ya koma, fuskarsa tayi jazur haka laɓɓansa sun yi jazur kamar wanda ya shafa janbaki tsaban ja, yayinda idanunsa suka shige sosai suka ɗan tasa sai haske da suka ƙara tarwai da su, gashin kansa ya bi da kallo yana faman shafa gefen kumatun sa da hannunsa ɗaya, gaban gashin kansa yayi tsayi sosai kamar wanda za a ƙitsa, ƙeyansa kuma babu komai sai ɗan gashi kaɗan da ya toho,
Ɗan numfashi ya ja yana mai lumshe idanunsa before ya buɗe yana sake kallon kansa, shiru yayi na tsawon lokaci yayinda yake faman kitsa hanyar da zai bi don magance matsalar sa, har yanzu ba ya samun sukuni daga azabtuwar da yake yi na soyayyar Haseena, komai ya ƙi ya sauya, yau rabon su da suyi waya kwana uku kenan, yana matuƙar kewarta da kewar jin muryanta,
Ɗan juya wa yayi yana kallon wayansa da ke ajiye a saman gado, yayi shiru yana tunanin ya ɗauka ya kira ta ne ko a'a? sabida ya daukar wa kansa Alkawarin in har ba ita ta kira sa ba bazai sake kiran ta ba, cuz ko ya kira ƙarshe ɓata mishi rai zata yi ta ƙi basa lokacin ta, dole sai ita ta kira don kanta sannanne zai iya samun time ɗin ta,
Janye idanunsa yayi yana nufan wurin takalmansa ya zura slippers green colour; sannan ya fice a dakin ba tare da ya dauki wayan ba,
A hankali yake taka matattaƙalan benen yana sauka, idanunsa ne suka faɗa a kan bayanta; wanda bai samu ganin fuskarta ba sakamakon juyawan da tayi riƙe da plates a hannu zata kai kitchen,
Tsayawa yayi cak yana kallon bayanta sabida ba ƙaramin tafiya dashi tayi ba, yanda mazaunan ta suke juya wa cikin baƙin siririn skirt ɗin da ta sanya ya tsuke ta, ya fitar mata da ainihin shape ɗin ta mai ban sha'awa da ɗaukar hankali

Sanye take da milk color din riga wanda aka yi sa da lace, an yi design mai shoki na gefe ɗaya, rigan bata da tsayi iya ƙugunta ta tsaya, sai dai shokin da aka yi ne na gefe ya sauka har wurin gwiwarta, sai siririn baƙin skirt ɗin da ke jikinta,
Kanta kuma sanye da hulan turban; wanda aka yi da lace É—in rigan

Yanda bayanta ya ja hankalinsa ya kasa ɗauke ido a kanta har ta shige cikin kitchen ɗin, a ransa kuma yana mamakin wace ce wannan mai irin wannan sura mai ban sha'awa? har bayanta ya ɗauke masa hankali ina ga ta juya gabanta, ji yayi har cikin ransa yana bukatar tozali da ita domin ƙare wa wannan kyakkyawan jikin nata kallo,
Ya kasa ci gaba da tafiya yana tsaye a tsakiyar benen, yayinda ya É—aura idanunsa yana zagaye ilahirin falon da kallo babu kowa sai sauran plates da aka ajiye a tsakar falon

While Maryamu koda ta ajiye plates É—in a kitchen, sai ta juya da nufin kwaso sauran,
Dayake plates É—in da suka ci abinci ne har da waÉ—anda su Aunty Zainab suka ci suka tafi, while su Momy sun shiga yin Sallah,
Ganin ita kaÉ—ai ta rage tunda ba ta sallah shiyasa ta fito ta soma kwashe kayan da nufin ta wanke before su Aakifa su fito,
Koda ta fito falon bata kula da SHAREEF da ke tsaye a kan bene ba, hankalinta yayi gaba wajen kwaso sauran plates É—in

Inda a nan take idanuwansa suka yi masa tozali da wacce yake kallo, har ga Allah a farko bai gane ta ba tunda bazai iya tantance kamannin Maryamu ba, cuz a baya ba kallonta yake yi ba sabida yanda ya tsane ta, bare yanzu da tayi fresh duhun skin dinta ya ragu sosai, ta koma kamar irin dack Choco colour din nan mai ban sha'awa da É—aukar ido,
Idanun nan nata sun ƙara tarwai dasu masu zubin ƙwai girmansu ya ƙara fitowa sosai, musamman da ta saka tozali,
Tayi light makeup a fuskarta wadda yayi tsari da zubi na fuskarta; ya kuma ɓoye mata kamannin ta

Tun daga sama har ƙasa yake kallonta, ba komai ya fi daukar hankalinsa ba irin kyakkyawar surar jikinta da yayi matukar fizgar tunaninsa ya sanya shi a wani irin yanayin da ya kasa fassara shi, har wani haɗiye miyau yake yi tsaban yanda surar jikinta ke rawa a idanunsa, tabbas Allah yayi halitta a wurin nan,
Yanda ka san maye haka yake bin ta da kallo har sanda ta sake shigewa kitchen ya kasa É—auke ido a kanta,
Sai da ya ji motsi a gefe guda sannan ne ya mayar da hankalinsa a kan Aakifah da ta fito daga É—akin Maryamu

Itama irin shiganta sak da na Maryamun, domin su uku aka yi musu É—inkin,
Tana kokarin wuce wa kitchen ne ta hange sa a wurin, shiyasa da murnanta ta kira sunan sa tana washe masa baki

Sai lokacin ya gane ita ce, amma yayi mamakin ganinta tunda bai san da zuwan nasu ba, in fact ma bai da labari,
A hankali ya soma takowa zuwa ƙasan yana bin ta da kallo har ya sauka

While ita kuma tace, "Yaya SHAREEF, tun É—azu muka zo muna ta neman ka aka ce kana barci, ina wuni?"

"Lafiya, ke da wa ku ka zo?"

Cike da murna tace, "mu da su Ammee ne, sun shiga yin Sallah basu fito ba. Bari in kira maka su Yusaira suna É—aki suma."

Guntun murmushi yayi yace, "no bar su, bari in je in yi sallah zamu gaisa in na dawo."
Yayi maganar yana wuce wa batare da ya jira amsar ta ba, sai dai har yakai bakin ƙofa yana kallon hanyar kitchen ɗin ko zai ganta ta fito, sabida har lokacin bai fahimci wace ce ba, amma ganin Aakifah sai yake tunanin ko dai Yusaira ce? Amma bai yarda a ransa ita bace tunda ita tana da haske ba kamar wannan da ya gani ba, duk da haka yana zaton maybe wata bakuwar ce, har ga Allah bai taɓa tunanin Maryamu bace tunda bai taɓa kawowa a ransa zata iya koma wa kamar wannan ba, in fact ma da tsawo da jiki duk wannan ta fi Maryamun da ya sani, kuma bazai iya tantance ta ba tunda ba ya kallonta, bai da lokacin ta ma balle ya santa

Sallan yayi ya dawo, a lokacin su Ammee sun fito falo suna zaune

Aakifah da Maryamu kuma suna kitchen suna wanke-wanke

Da gudu Na'ilah ta ƙarisa wurin sa tana faɗin, "oyoyo Yaya Hanif. Sannu da zuwa."
Chapter 27 · 0% Book details