← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 75

Sashe 10

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hanif, ka dena min maganar yarinyar can, har abada ba ta gabana kuma bazan taɓa jin sonta ba bare har in ji sha'awarta, don haka kana wahalar da bakin ka ne, Haseena kaɗai nake so kuma ita ce a zuciyata, zan ci gaba da lallaɓa wa a haka ina shan magani komai zai wuce very soon."

To jin wannan maganar nasa shiyasa shima Hanif ɗin ya ƙyale sa, tunda a yanda yake gani SHAREEF bazai taɓa fahimta ba, already ya yi nisa ba ya jin kira.

🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆

_____Koda aka yi hutun second time; Maryamu bata dawo gida ba, a can Abuja tayi hutun ta, since Momy tace, "gwara ta zauna a can kawai tunda suna zuwa koyon computer, idan ta dawo kuma babu amfani."
Hakan ne yasa Ammee bata bar ta ta dawo ba tunda ga abun da Momy tace,
Ita kuma Maryamun bata damu ba, duk da ta so ta koma hutun domin a can Zaria ta fi so tayi, ba ta son ma zamanta a Kano ko don SHAREEF, since ba ta son abun da zai sa ta tuna shi a rayuwa bare ta famo gyambon da ta daÉ—e da warkar dashi a zuciya,
Tayi zamanta a can har suka ƙare hutun suka koma school

After sun yi hutun third time, dayake hutun da yawa shiyasa ta koma gida,
Ammee driver ta sanya ya kawo Maryamu har Kano

Ba ƙaramin farin ciki Momy tayi ba saboda ganin yanda ƴarta ta sauya gaba ɗaya, kamar ba ita ba har ɗan wani ƙiba ta kara, dama Maryamu ba baya ba wajen Kyawun jiki, sam bata da rama, sai ga shi ta samu hutu yanda jikinta ke buƙata; ta zama ƴar lukuta da ita har ɗan tsawo ta ƙara

Abun da su Hanif suke tsokanarta dashi kenan, don su kansu sun sha mamakin ganin yanda tayi tsawo kamar ba ita ba, tayi fresh abun ta, sai tsokanarta suke yi

Ita kuma ba abun da take yi sai murmushi, har ranta ta ji daɗin yanda suke nuna sha'awarta da ganin sauyawan ta, dama hakan take so, bare ita akwai iyayi da ficchi, tana son a yabe ta musamman yadda ta saka a ranta zata ba SHAREEF mamaki, sam-sam bata damu ta gansa ba don bata buƙatar tozali dashi, shiyasa tayi farin ciki da ta ji labarin ba ya ƙasar ma a wurin Sadiq, kwana ɗaya kenan da tafiyarsa wurin Haseena, kuma Sadiq ya faɗa mata, "gobe ne zai dawo."
Shi yasa ta damu Momy, "zuwa gobe tana son ta wuce Zaria."

Momy ta so hana wa, amma Dady yace, "gwara ta tafi kawai tayi musu hutun a can, daga can ma sai ta wuce, since tun sanda ta zo bata koma ba gwara ta tafi zasu ji dad'i Iyayen nata."

Maryamu kuwa sai murna da farin ciki, tare da Sadiq zasu je but shi a ranan zai dawo in ya kaita, shiyasa suka shirya tafiyan da sassafe

Washe gari suka wuce Zaria, gidan Iya Samira suka sauka, tunda dama sun san da zuwan su domin Dady ya kira ya fada musu, shiyasa tuni Iya Samira tayi musu girki

Maryamu farin cikin ta ba ya ɓoyuwa yau ga ta a garin su ta zo gida, a guje ta rungume Iya Samira kamar zata ka da ita don murna

Itama farin cikin yasa ta ƙanƙame ta tana cewa, "oyoyo.. oyoyo yau ga Meramun mu ta zo, Oyoyo Meramun Iya."

Sai dariya suke yi suna rungume da juna sun ƙi sakin junan su, while Sadiq da ke gefe ya tsaya yana kallonsu shima yana dariyan, yace, "Iya wai ita kadai kika gani ne ban dani? Ko dai in juya ne?"

"Haba Sadiqu taya zaka juya kuma? Ai bazan so haka ba, yi hakuri murnan ganin Meramu ne ya ruÉ—a Ni, ku taho mu je É—aki."
Tana riƙe da Maryamu suka shiga ciki,
Bayan sun zauna take tambayarsu iyayen nasu?

"Suna nan lafiya, sun ce a gaishe ki da kyau da kyau, ai ni a yau ma zan koma ba kwana zan yi ba, na dai kawo Maryam ne."

"Haba dai a yau kuma Sadiqu? Ai ka bari ka huta ko? Ko zuwa gobe ne mu É—an yi hiran yaushe gamo."

Dariya yayi yace, "ai Ni ban zo da shirin kwana ba Iya, yau zan tafi Insha Allahu."

Maryamu da ta tashi ta je ta É—auko furan da ta gani ajiye, sai ta zo ta zauna tana kwankwaÉ—a, sai da ta ji ya ishe ta sannan ta cire baki tana hamdala, tare da furta, "Iya ki kyale sa, kawo Ni kawai yayi, kuma suna da school ya kusa kammala karatu ba damar yayi fashi."

"To alhamdulillah, Allah ya dafa muku, bari in kawo muku abinci don na ga kamar da yunwa a tare da ku; tunda ga Maryamu nan har ta soma kwankwaɗe min fura, ga shi nan fa har girma kika ƙara."

Dariya suka yi gaba É—aya,
While Sadiq yana cewa, "ashe kema kin gani Iya? Wlh kuwa ta ƙara girma sosai har tsawo fa ta ƙara ashe da sauran tsawon ta."

"Yo ai dole ne duk wanda ya ga Maryamu ya san cewa ta sauya, musamman mu da muka daÉ—e bamu ganta ba, zaman can ya amshe ta ina tunanin Jikana SHAREEFU ya iya kiwo, har fa ajiye kumatu tayi; ka duba ka gani."

Sai dariya Sadiq yake yi yana cewa, "ƙwarai kuwa Iya, ga su nan kamar burodi."

Ita kuma Maryamu taɓe baki tayi jin an ambaci SHAREEF, yayinda ta sauya zancen da faɗin, "ita barci take ji ma, ba ta bukatar komai yanzu sai ta tashi."

Iya tace, "ta hau gadonta ta kwanta to, bari ta kawo ma Sadiq abincin ya ci."

"Nima Iya ba wani ci zan yi ba, amma kawo in sa albarka ko kaÉ—an ne."

"Yauwa Mijin, amma ai bazan ji dad'i ba har ka tafi baka ci abincin Matarka ba, gani zan yi kamar ban iya ba tunda ka ƙi ka yaba."
Ta miƙe ta nufi inda ta ajiye coolan abincin; ta ɗauko ta dawo dashi ta zuba mishi,
Yana ci suna hira cikin raha da dariya

Maryamu kuwa tuni barci ya soma fizgarta, tun tana jiyo dararrakun su da hiran su sama-sama; har dai ta dena ji barci ya É—auke ta

Sai da aka kira sallan azahar sannan Sadiq ya fita ya je yayi ya dawo,
Shima sai ya É—an kishingiÉ—a tunda Iya Samira ta matsa mishi ya kwanta ya huta before ya tafi,
Shi yasa shima ya kwanta babu jima wa barci ya É—auke sa

Sai karfe huÉ—u Iya Samira ta tashe su gaba É—aya,
Bayan sun yi sallah sannan Sadiq yace, "zai wuce."
Tare suka fita har Iya Samira ta raka su Babban gidan su suka gaisa da jama'a sannan suka fito, Sadiq ya hau mota ya tafi bayan sun yi sallama

Maryamu sai ɗaga mishi hannu take yi, har sai da ta ga ƙulewar sa sannan ta bi bayan Iya Samira da tuni ta shige gida.
***

_____Kwana biyu Maryamu tayi a wurin Iya Samira; ta wuce ƙauyen su, suma kwanaki biyun da tayi; tayi su ne tamkar a ƙaya, don Allah -Allah take yi ta ganta a ƙauyen su wurin Iyayenta,
Babu yanda Iya Samira ta iya dole ta barta ta tafi,
A cewarta, "zata sake dawowa tunda hutun nata da yawa, ba yanzu zata tafi ba."

Su kansu su Inna bakin su ya ƙi rufuwa da suka ga Maryamu, yanda ta sauya musu a fuska sai abun ya basu sha'awa

"Ikon Allah! Ashe da rabon za ki ƙara tsawo Maryamu, kinga yanda kika girma kamar ba ke ba? Anya ba taliyan birni kike ci ba ya ƙara miki tsawon ƙafa? wannan ma ƙiris ya rage ki kamo Ummita wlh."
A cewar Umma Jummai tana kama haɓa gunun mamaki

Ban da dariya ba abun da Maryamu take yi

Inna ma tace, "wlh nima abun da na gani kenan, har kumatu ta ƙara tayi ƙiba abun ta, ashe dai zata yi ƙiba."

"To ai kin san ita tun farko babu rama a jikinta, amma Ni kaina ban yi zaton zata yi jiki haka ba, ikon Allah! Kuma kinga duk ƴan gidan babu mai jikin Maryamu, ta fita daban dai kawai." Umma Jummai ta sake furta hakan tana miƙe wa ta fita a ɗakin,
Tare da cewa, "bari in kawo miki abinci ki ci kafin Baban naku ya dawo, kinga gidan ma shiru babu kowa."

Maryamu tace, "ai Umma ki bar shi kawai, gidan su Aunty Ummita zan fara zuwa, in je in zagaya su don dasu nake kwana musamman Bintu rabin raina, nayi kewarta wlh, bari in je in ga gida."

Inna tace, "dama mai hali ba ya fasa wa, daga zuwa za ki soma bin gidaje baza ki bari ki huta ba?"

Tura baki tayi tace, "kai Inna! Wlh na sauya sosai, nayi kewarsu ne gwara in fara zuwa in gansu."
Ta miƙe tana ɗaukar gyalen ta tare da ficewa

Umma da ke wajen kichen, take kallonta da faÉ—in, "to ai ba ki san gidan Bintun ba, sai dai in kin je ki saka Yaran Ummitan ko Indo su nuna miki, Allah ya kiyaye hanya kar ki jima fa kinga Magriba ta gabato, yanzu za ki ga Babanku ya dawo."

Amsa mata tayi tana yafa gyalen ta, tare da ɗaura igiyar takalmanta da ta zura su masu shegen tsini kamar yanda ta saba, tayi musu sallama ta fice tana tafiya cikin yanga da ƙwalisa,
Dama an samu abun da ake so ne, bare an zo ƙauye shiyasa iyayin nata ya ƙaru; tafiya ma kansa ɗakyar take yi kamar baza ta taka ƙasa ba, duk inda ta wuce kuwa sai an kalle ta, wasu kuwa ba sa gane ta sai tayi musu magana don iyayi su san ita ce, suyi ta mamakin wai Maryamu ne haka ta koma ƴar gayu?
Sai su saki baki suna bin ta da kallo kamar wacce ta sauya musu,
To hakan ne ma don gani suke yi kamar ba ita ba, abun ka da baƙauye haka labarin ya soma bazuwa nan da nan ana maganar Maryamun,
Ita dai tuni ta wuce gidan Indo don nan ta fara zuwa
Chapter 10 · 0% Book details