← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 75

Sashe 51

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Sai ta fashe da dariya, domin maganar nasa ba ƙaramin dariya ya bata ba, musamman da ta tuna abun da ya faru ɗazu; yadda ta ga tsoro ƙarara a cikin idanunsa

While SHAREEF tsira mata ido yayi yana kallon yanda take ɓaɓɓaka dariyan babu ko ƙauƙauta wa, ba ƙaramin burge sa tayi ba, musamman da ya ga halittun dimples ɗin ta sun fito sosai zak irin nasa, sun yi mata mugun kyau, bai san lokacin da yakai hannunsa saman kumatun ta yana saka yatsansa ɗaya a ciki ba

Hakan ne yasa ta dakatar da dariyan nata, yayinda suka zuba wa juna ido babu wanda ke ƙyafta wa a cikin su, still hannunsa na a cikin dimples ɗin ta har yanzu,
Kamar shuÉ—ewar wasu seconni suna a wannan yanayin,
Yayinda Maryamu ta ƙyafta idanunta before ta saka nata hannun ta janye nashi,
Idanunta a cikin nasa a yanzu ta yarfar da hannun tana mai sake haÉ—e fuska,
"Kabar nan wurin, kar ka zo ka takura min ina aiki."

Fuskarsa ya matso da ita sosai kusa da nata, a hankali ya furta, "zan taya ki ne, sabida in wanke kaina daga zargin da kike min a kan Ni mugu ne; azzalumi, ba na son kalman."

"Ba ka so ko?"

"Eh."

"Ai kuwa kai mugu ne azzalumi, bazan taɓa manta abubuwan da kayi min ba, babu yanda zan yi ne nake zaune da kai cikin inuwa ɗaya a wannan gidan, baka tausaya min ba sabida ba ka so na, amma meye laifina? Don na nuna maka soyayya?" Sai ga hawaye sharr suna zuban mata, shiru tayi tana zare mishi idanu da cije laɓɓa sabida yanda take jin mugun haushin sa

Ba ƙaramin mamaki take ba shi ba, yanzu sam ba ta shakkar gaya masa magana, sosai ransa ya sosu da furucin ta, amma ko a fuska bai nuna ba, sabida ba ƙaramin karaya yayi ba da ya hangi hawayen ta, tabbas a yanzu yana mata uzuri sosai domin yana ganin duk shi ya ja,
Ganin ta juya zata ci gaba da aikin nata, sai ya sake matso wa sosai kusa da ita yana shinshina ta

A fusace ta juya tana ture shi, "kai wanne irin maye ne? Kana takura min fa nace, meye haÉ—in ka da Ni?"

"Sabida Ni Mijinki ne, ina buƙatar sauke haƙƙina da ke kanki."

Wani kallo ta watsa mishi kamar idanun zasu faɗo ƙasa, cikin takaici tace, "wanne haƙƙin naka? Oh! Kana tunanin akwai wani abun da zaka samu a wuri na ne? Don ka ga na zama Mutum wato? To idan ka manta zan tuna maka, Ni ce dai sakaryan yarinyar nan ƴar ƙauye Bagidajiya, jahila ko? Ni ce Maryamu mai bak'ar fuska da ka tsana kake wulaƙanta ta, Ni ce dai ban canza ba..."

Hannu yasa ya rufe mata bakin ta, sai ta buge masa hannun ranta a mugun ɓace take bin sa da mugun kallo,
Before tayi magana ya rigata da faɗin, "kin canza mana, kin mugun canza wa, a yanzu ke abar so ne da sha'awar kallo, bazan iya zura idanu ina kallonki a haka ina cutuwa ba, abun da nayi miki a baya just ki manta, mu haɗa kanmu kin ji? Ina matuƙar buƙatar zama da ke, Please ki sauya daga yanda na sanki a baya mai nuna min soyayya ba irin wannan ba."

Baƙin cikin maganar nasa ne ya cika ta, cikin ɗacin rai a fusace tace, "Ka san wani abu kuwa? Kuskuren da zaka yi shine kayi kokarin takura wa rayuwata a gidan nan, baka san me zan iya aikata maka ba, har yanzu baka san wace ce Ni ba, a baya kallona kake yi kawai sabida a lokacin soyayyarka ta rufe min ido, ta sauya Ni fiye da tunani, amma a zahiri ban canza ba, kawai dai ban nuna maka halina bane, wlh ban da mutunci, zan iya maka duk abun da na ga dama in har baka fita daga rayuwata kabar Ni ba, abun da kake nema baza ka samu ba."

Lokaci guda ta ga ya fashe da dariya, abun da tunda take bata taɓa ganin sa yana yi ba, in fact ma ko murmushin sa ne bata taɓa ganin yayi ba,
Saurin ɗauke kanta tayi a kansa sabida ba ta son ta ci gaba da kallon fuskarsa musamman yanda yayi mata kwarjini; tsantsan kyawun sa ya sake bayyana da fararen haƙoransa suke waje,
Bata son ta nuna mishi lagon ta ya gane cewan maganarta kawai burga ce

Hannu yasa ya juyo da kanta, idanunsa ya zuba mata cikin nata fuskarsa da murmushi yace, "Today I understand who you are, I know I was wrong in the past, but now I'm asking for your forgiveness for the things I did to you, bazan iya ganin laifin ki a komai da za ki yi min yanzu ba, zan lallaɓa ki sabida ina bukatar ki a rayuwata."
Sai ya haÉ—e fuskarsu wuri É—aya yana goga hancinsu,
Tuni ta rufe idanunta; shi kuwa yana kallon nata face É—in ne, "Thank you for all the things you have done for me in my life. I couldn't understand you before, but now I understand you more. Kar kuma ki ce I need something from you, Maryam, please be patient and forgive me."

Eyes ɗin ta ta buɗe tana kallonsa cike da mamakin maganganun sa, bata taɓa tunanin da sauri haka SHAREEF zai iya sauya mata ba, bata taɓa tunanin zai iya ɗaukar ta wata aba a ƙanƙanin lokaci ba,
Idanunta a kansa har ya juya yabar kitchen batare da ya sake ce mata komai ba, yayinda ta bi bayansa da kallo har ya fice,
Anya shi ne? Tana kokwanto, ji tayi hawaye suna son cika mata ido, sai tayi saurin rufe face ɗin ta da tafukan hannunta, "amma ya cutar dani, taya ya zan iya yafe masa cikin sauƙi haka? Har yanzu ina jin haushin sa kuma ina jin soyayyarsa a wannan lokacin, ko dama soyayya da ƙiyayya suna haɗe wa wuri ɗaya?"
Buɗe idanuwanta tayi, sai ta kama aikin da take yi amma ranta babu daɗi kuma wani gefen tana jin farin ciki, tana ji kamar zata iya manta abubuwan da yayi mata ta dawo da soyayyarsa, wai yau SHAREEF ne yake bata haƙuri, addu'o'in da ta dinga yi don ya fita a rayuwarta sai ga shi Allah ya sauƙaƙa mata komai, maganar sa gaskiya ne da yace So ba ya sauya wa, bakin da ya furta so; ko ya dawo ya bayyana ƙi ba gaskiya bane, soyayyarsa ita ce lagwonta kuma ƙaddaranta, baza ta taɓa sauya wa a zuciyarta ba, ko dai zata iya ba shi wani damar ne?
Girgiza kanta tayi, a ranta tana tunanin har yanzu bai ce yana sonta ba, amma zahiri ya sauya mata, yanzu babu tsanar nan nata a idanuwansa, itama dole zata sassauta mishi ta ga iya gudun ruwan shi ko wani buri daga cikin zuciyarta zai cika

Har sai da aka kira sallan magriba bata gama abun da take yi ba, sai da aka shiga Masallaci sannan ta gama komai takai saman dainng, after ta gama sai ta ɗibi nata abincin ta shige dashi ɗaki ta datse ƙofan ta

Koda SHAREEF ya dawo sallah, jin shiru babu kowa a falo, yana ganin abincin a saman dainng ya san ta gama, don haka kai tsaye ɗakin ta ya nufa, but yana taɓa ƙofan ya ji a rufe, sake murɗa wa yayi ya ji gam alamun an rufe ta ciki,
Kiran sunan ta ya soma yi a hankali yana cewa, "ta buÉ—e mishi kofan."

Amma Maryamu tana jin sa sarai ta ƙi buɗe wa, tana zaune a saman gadonta tana cin abincin ta da hannu hankali kwance, har ya gaji da buga wa yana faman kiran sunan ta but tayi banza dashi
Chapter 51 · 0% Book details