← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 75

Sashe 71

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai kwanan nan bayan an rufe su tsawon lokaci ana gana musu azaba kala-kala, wanda ya jawo mutuwar rayuka da dama, kwatsam...! sai suka É—aura wa sauran video kowacce tana bayani da kanta da dalilin shigowarta harkan, da kuma abubuwan da suke aikata wa a ciki,
Wanda ciki har da Haseena da ita tana raye bata mutu ba,
Nana kuwa tun gana musu azaban da ake yi wani irin ciwo ya kama ta na tsananin wahala, daga nan kuma sai wasu tsutsotsi suka dinga fito mata a ƙasanta sakamakon rashin samun biyan buƙata kamar yanda suka saba, ciwon yayi mata tsanani ga azaban da ake basu, lokaci guda zuciyarta ta buga ta mutu a nan take, sai warin ta aka ji,
Sauran ma suna a cikin yanayin da take ciki,
Dukkansu tsutsotsin suke fita a cikin jikinsu ga wari da suke fitarwa, rashin samun junan su ne yasa hakan take faruwa, wanda wasu har sun yi dabara sun soma biyan buƙatar su tunda a haɗe suke,
Da jami'an suka sani sai suka raba su kowacce da É—akin ta, suka kuma ci gaba da gana musu azaba kala-kala

Kwatsam..! hiran da aka yi da su da nuna fuskokin su, ya jawo hankalin jama'a da ƙasashe da dama, wanda nan take labarin ya yaɗu har cikin Nigeria wasu daga cikin waɗanda suka san Haseena da yawa sun gane ta kuma sun santa, musamman ƴan uwanta,
Bare labarin da ta bayar tana yi tana kuka, da yanda ta kashe Æ´ar uwanta da mahaifiyarta

A BBC News an haska babu iyaka, wanda yasa har gidan su SHAREEF sai da suka ga labarin, sun yi matuƙar mamaki abun ya ɗaga musu hankali, duba da yanda rayuwarta ta koma babu kyan gani, ga halin da take ciki, a cikin su babu wanda ya ji tausayin ta barin ma SHAREEF, wanda shi hankalin sa a tashe yake da baƙin cikin kasancewar ya taɓa auren ta, tunda yanzu kowa zai kalle shi da abun ne waɗanda suka sanshi, sabida har a labarin nata ta saka shi a ciki komai na rayuwarta sai da ta bayyana

Mutane sun yi turr da ita matuƙa, tunda har lokacin ita kanta baza tace ga dalilin aikata abinda ta aikata ba, wacce ta sanya ta a bala'in da kuma ƙawayenta su Herin duk sun mutu, kowa laifin Haseena yake gani da kuma mugun abun da ta aikata, babu kunya babu tsoron Allah, ga shi asirin su ya tonu, abun baƙin cikin ma tana ƴar Musulma Bahaushiya amma ta je wata ƙasa ta haɗe da wasu ƙabilu tana aikata abun da ta ga dama

Sanadin hakan yasa Abba ya yanke jiki ya faÉ—i, tun ganin labarin abun ya firgita shi ya faÉ—i a nan take, aka yi dashi asibiti cikin halin ciwo.
Komai yayi farko dama zai yi ƙarshe, karshen masu aikata saɓo kenan, wasu tun a nan duniya Allah ke nuna musu ikonsa.
*****

A yanzu dai za a iya cewa jikin Maryamu da ɗan sauƙi ba kamar baya ba, amma kuma yanda itama take amai a koyaushe, hakan ne yasa aka kira Likita ya duba ta don su tabbatar da mai yake damunta,
Kuma tashin farko aka gane tana da shigan ciki kusan watanni huÉ—u

Abun ya ɗaure musu kai kuma ya saka su farin ciki, ai sai kuma baƙin cikin su yakau damuwa ta yaye farin ciki ya yaɗu, musamman Goga SHAREEF babu wanda yakai shi murna da ɗoki,
Allah da ikonsa kenan! Mai yanda ya so da kuma miƙa kyauta a sanda ya so, ga shi a halin da Maryamu take ciki ashe har da ciki a jikinta, kuma duk wannan abun bai zube ba bare ya samu matsala,
Wannan dalilin ne yasa suka ƙara bata kulawa na musamman, duk da a yanzu komai Alhamdulillah za a ce don hankalin ta ya dawo jikinta, ashe zafin laulayin ne itama yasa har yanzu tana jin jiki sosai, sai kuma kanta da koyaushe ƙorafinta kenan ciwo yake yi,
Yanzu kafarta ta warke musul har taka wa tana yi wani lokacin in jikinta da ƙwari,
Tun fara ciwonta shima SHAREEF ya dawo gidan da zama, a É—akin da take kwana a nan yake kwana yana kula da ita, komai take so shi yake mata har wanka da duk wani kula shine mai yi, sai wani lokacin ne Momy take taimaka mishi amma ba ya jirga wa, aikinsa kuwa tuni ya ajiye sa ba ya zuwa, don ma Companin Dadyn su ne; da tuni an kore shi

Hanif ne kawai yake zuwa, shima yanzu komai normal a wurin su tunda Amra ta samu lafiya ta koma gida sai godiyar Allah sai kuma abun da baza a rasa ba.

          Bayan wasu lokuta jikin Maryamu ya murmure sosai, cikinta har ya fito yayi girma, yanzu komai alhamdulillah za a iya cewa tunda a halin yanzu jiki yayi kyau matuƙa, duk da har yanzu ba kasafai wani lokacin take samun lafiya ba, kan nan nata yana matuƙar matsa mata, shi ne dalilin da yasa har yanzu ake mata magani, amma sarai ta warke, don har gida ake kiran wata Likita Mace tana duba ta sabida cikin nata

Kasancewar SHAREEF akwai zafin kishi, don haka da kansa ya nemo Mace ita take kula da ita, sai kuma Malamin da ke bata magunguna ana shafa mata ko ta sha wasu, yanzu haka burinsa kawai Maryamu ta koma gidansa, amma su Momy sun hana sun ce, "ya barta a nan har ta haihu."
Shi kuma gaskiya yana takura don yana son bata kulawa matuƙa, amma ba ya samun damar hakan, yawanci Momy tana wurinta ko kuma a fita da ita Falo suna zaune tare a can, ga idon jama'a tunda ana yawan zuwa gaishe ta musamman ƴan uwan Momyn, kwata-kwata bai samun yanda yake so, burinsa ya bata kulawa ya ririta ta kamar ƙwai,
Don haka ya nace wa Momy dole sai an ba shi Matarsa

Momy tace, "to ka É—auke ta tunda baka da kunya, babu inda Maryam zata koma har sai ta haife abun da ke cikin cikinta lafiya; sannan kake da damar daukar ta, ya za a yi cikinta ya soma tsufa kuma ka É—auke ta ka kaita inda babu kowa?"

Fuska ya kwaɓe yana cewa, "Mom, Ni ba mutum bane wai? Ni bazan iya kula da ita bane? Duk abun da take so Ni zan yi mata, kawai ki bani ita mu tafi gaskiya bazan iya jira har wani lokaci muna nan ba."

Ware idanu Momy tayi a kansa tana kallonsa don ta kasa magana tsaban mamakin sa

Yayinda Maryamu kuwa tana shan fruits ne, ƙafafuwanta a saman Centre table tana ta dariya

Hakan ne yasa SHAREEF ya harare ta yace, "ke wai da wa kike yi ne ina magana kina min dariya?"

Fuska ta taɓe itama tana buɗe mishi idanunta, sai tace, "Ni ba da kai nake yi ba fa, kallo nake yi."
Sai ta tura baki gaba tana É—age kanta zuwa kallon TV, yayinda ta ci gaba da shan fruits É—in ta da Spoon

Tasowa yayi ya dawo inda take, yana kamo hannunta É—aya tare da marairaice fuska yace, "Baby ko ke ba kya son mu koma gida ne? In kika saka baki Momy zata yarda tunda kin ce min kina son zuwa, ke da bakin ki fa kika faÉ—a min haka."

Jin haka sai Maryamu ta dube sa, sai kuma ta kalli Momy da ta zuba musu ido tana jiran ta ji abinda zata ce, sai kawai ta kwaɓe fuska tace, "wlh Momy Ni ban ce ina son zuwa ba, shine ya matsa min sai na faɗa miki mu koma wai za ki ji maganata, amma Ni ba na son koma wa nan ya fi min."

"Ƙyale shi Maryam, ai na sani sai dai shi ya zuga ki." Sai ta banka mishi harara tace, "to ka tashi ka wuce tunda baza ka samu abun da kake so ba, Maryam dai baza ta koma ba sai ta haihu duk nacinka SHAREEF."

Miƙe wa yayi duk ransa ya ɓaci sabida har yanzu ya kasa samun nasara, don haka yabar wurin yana kumbura baki, yana jin Maryamu tana masa dariya amma bai juya ba, kai tsaye saman ya haye ya je ya samu Dady a ɗakin sa, sai da ya shiga ya zauna before yace, "Dady please ka saka baki Momy ta bani Matata mu koma gidan mu, wlh Ni na gaji da zama a nan gani nake yi kamar ban yi aure ba, ta samu lafiya fa, kuma yanzu remain two months ko fiye da haka fa sannan zata haihu, gwara mu koma kawai."

Baki Dady ya riƙe sabida jin kalamansa

Shi kuma sai ya duƙar da kansa yana shafa ƙeya don sai yanzu ya ji kunya ta kama sa

Sai Dadyn yayi murmushi yace, "just two months kake ganin baza ka jure ba My son? ai Momyn ka ta faɗi gaskiya, gani kake yi zaka iya kula da ita, baka san cewa abun da wahala ba musamman yanzu da cikinta ya tsufa; kuma ita ba ƙoshin lafiya ta cika ba, kayi haƙuri kawai ka barta a nan don baza muyi wasa da lafiyarta ba."

"Dady, wai shi ba ga Hanif can da Matarsa a gida ba? Please Dady don Allah ka saka baki, i promise da zaran cikin ya shiga watan haihuwa zan dawo da ita, ina son gaskiya Matata a kusa dani kuma..." Sai kuma yayi shiru kamar zai yi kuka

Dady kuma sai yace, "eh na ga alamun da gaske kake yi, kar kuma mu hana ka a samu wata matsalar daban, shikenan ka je zan yi mata magana za a baka Matarka."

Dariya SHAREEF yayi, farin ciki yalwace a kan face ɗin sa don ya kasa ɓoye wa, yace, "thank you daddyna, Nagode sosai."

Shi kuma Dady dariya kawai yayi yana kaÉ—a kansa, before ya ci gaba da abun da yake yi tunda yana duba jarida ne,
After SHAREEF ya fita da É—an wani lokaci before shima ya tashi ya shiga toilet É—aura alwala, tunda an kira sallan Magriba
Chapter 71 · 0% Book details