← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 75

Sashe 33

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

suka bar Maryamu a wurin tana kumbura tana sacce wa, yayinda ranta yayi mugun ɓaci sabida abun da SHAREEF yayi mata, sam a yanzu bata ji tausayinsa ba duk da ta ga halin da yake ciki, sai ma kwantar da kanta da tayi idanunta sun cika da hawaye ta hana bayyanar su a waje,
Wai wanne irin ƙaddara ce ta sanya ta sanin wannan mutumin? Sam bai da tausayi bai da ragowar sa, duk da ada ta shanye wulaƙancin sa, a yanzu kuwa sam baza ta iya ba, ko me zai faru zata jure binne soyayyarsa domin itama ta nuna masa ƙiyayya ƙiri-ƙiri kamar yanda yake nuna mata, baza ta taɓa bari ya ƙunsa mata baƙin ciki ita kaɗai ba, dole shima sai ya ɗanɗana, wlh baza ta ji tsoron sa ba in har bazai fasa wulakanta ta ba, a yanzu ta wuce wulaƙanci domin jin ta take yi dai-dai da zamanin sa,
A fili ta furta, "SHAREEF sai na koya maka hankali wlh, mugu azzalumi mara imani, sam baka da imani."
Sai kawai ta fashe da kuka sabida tuƙuƙi da baƙin cikin har yanzu tana jin soyayyarsa a ranta,
"Ya Allah ka cire min wannan bawan naka a zuciyata, ban san wanne laifi na aikata ba ya Allah ka jarabbe Ni da wannan mummunar ƙaddaran da zai zama ajalina, ina dana-sanin sanin bawan nan naka, ya Allah nima ka rama min irin abun da yayi min."
Kuka sosai take yi kanta na saman cinyanta,
Sai da ta É—auki lokaci before ta sanya hannu ta soma share hawayenta sabida alkawarin da tayi wa kanta ta dena zubar da hawaye sabida shi, bai cancanci tayi mishi kuka ba tunda bai da imani,
Sai da ta gyara face É—in ta sannan ta sake kwanciya tana jiran isowar su, yayinda a zuciyarta tunani ne fal tayi shiru tana sauraron bugun numfashin ta.
***

_____A can ciki kuwa; SHAREEF shi kaÉ—ai ya shiga cikin office din don kar Sadiq ya san mai zai yi, yace masa, "ya jira sa a nan."
Ya shiga ya samu Doctor É—in a ciki yana faman aiki

Yana ganin sa shima ya ajiye bairo din hannunsa tare da kiran sunan sa

Zama SHAREEF yayi daƙyar yana faman cije laɓɓa

"S. Ahmad kar dai a ce ciwon ne kuma?"

"Yes Doctor, ya matsa min ba na samun sukuni yanzu ko kaÉ—an, haka kawai yake tashi min, magungunan ma da nake sha ba sa min aiki, Please help me ka taimaka min da wasu masu karfi da zai sa na rabu da wannan jarabar."

Kallonsa yake yi cike da tausayinsa, sai yace, "solution ɗaya ne fa nace maka S. Ahmad, shine ka nemi Mata kayi aure wannan ne hanya ɗaya da zaka rabu da wannan cutar, domin a kullum ƙaruwa take yi idan kana yawan ciwon nan karshe zai haifar maka da wata matsalar ne na daban, ciki kuwa har da na rashin haihuwa, ba a son sha'awa yana kwantar da Mutum sabida nan gaba abun yana zama wani ciwon daban ne, ina ga ka nemi Mata kawai kayi aure tunda Allah ya hore maka, kana da ni'imomin da kowacce Mace a duniya zaka iya samun ta cikin sauƙi."

Shiru SHAREEF yayi yana faman cije laɓɓa, ya san cewa Doctorn bai san da yana da Mata ba a yanzu haka, amma bata da amfani tunda ta ƙi farin cikin sa, kuma bazai iya faɗa masa ba, shiyasa ya gyaɗa kansa a lokacin da ya gama ba shi wasu shawarwarin daban, yace, "zan yi insha Allahu, amma yanzu ka duba Ni ka bani wasu magungunan wanda zasu yi min Please."

"Ok ba damuwa."
Likitan yafaɗa yana miƙe wa tare da zagayowa wurin sa,
Duba sa ya soma yi before ya É—auki waya ya kira wata staff

Bayan ta shigo ta risina tana gaishe da Doctorn, idanunta a kan SHAREEF duk da ba ya kallonta; amma tuni kyawun sa ya É—auke mata hankali har ba ta jin ma mai Doctorn yake cewa,
Sai da ya kira sunanta tukunna ta mayar da hankali a kansa da sauri tana cewa, "na'am Sir."

Harara ya watsa mata yana cewa, "common zo ki amshi wannan takardan ki amso min magungunan ciki."

"Ok sir." Ta amsa da sauri tana nufan inda yake,
Takardan ta amsa sannan ta nufi hanyar fita tana sake satan kallon SHAREEF da bai san tana yi ba.
Bata É—auki lokaci ba ta dawo da magungunan da ya rubuta mata, tare da allurai guda uku,
Ta miƙa masa cikin girmamawa,
Har wannan lokacin idanunta a kan SHAREEF, musamman yanzu da ya ɗago face ɗin sa tana kallonsa sosai, ba karamin fizgarta kyawun sa yayi ba, ji take yi kamar ta tsaya ta ci gaba da kallonsa tsaban burge ta da yayi, balle yanda ta ga yana yamutsa fuska kamar sai yi kuka sai cije laɓɓa yake yi; ba ƙaramin kyau hakan yayi masa ba kamar wani shagwaɓaɓɓen Yaro,
Ba don ta so ba ta fice a cikin office É—in tana jinjina baiwa da kyawu irin nasa, tana jin dama ita ce da wannan tabbas da ta more Miji
(Bata san kyan ɗan maciji bane😏)

Doctor miƙa masa magungunan yayi wanda ya zuba su a leda ya zari allura ɗaya, yake cewa, "ga magungunan nan sai ka riƙa sha safe da dare, but ka bi ƙa'ida S. Ahmad don suna da karfi sosai, and yanzu wannan alluran zan yi maka shi zaka ji relief in short time, akwai biyu a ciki gobe za a yi ɗaya haka ma jibi, insha Allahu zaka ji sauƙi babu wata matsala, sai dai ina ƙara baka shawara ka yi aure don Allah, idan abun yayi karfi babu maganin da zai yi masa wlh."

Jinjina kansa kawai SHAREEF yayi, yayinda ya rufe idanuwansa ya jinginar da kansa a jikin kujerar da yake zaune, shi kaÉ—ai ya san irin azabar da yake ji na game da ciwon nan

Tasowa Doctorn yayi ya buƙaci ya ba shi hannun sa,
Batare da ya buɗe idanu ba ya miƙa hannun har aka yi masa bai motsa ba,
Daga nan ya ci gaba da ba shi wasu shawarar yana tausan sa a kan hanya mai ɓille wa

Bai san SHAREEF jin sa kawai yake yi ba, shi kansa damuwarsa kenan ya rasa yanda zai yi da matsalar Haseena, tabbas lokaci yayi da zai nema wa kansa mafita, amma zai ƙara ƙasƙantar da kansa ko zata amince da bukatunsa yanzu.
Sai da ya É—auki tsawon mintoci before ya tashi suka yi sallama da Doctorn,
Yayinda yake jaddada mishi, "ya nemi abinci da zaran ya koma gida ya ci, sabida alluran."

Fitowa SHAREEF yayi yana duba inda zai ga Sadiq, sai dai babu shi a wurin, sai da ya soma tafiya har ya kusa barin side É—in, before ya hango Sadiq É—in ya taho da sauri ya nufo sa,
Saurin riƙo sa yayi yana mishi sannu,
Kansa kawai ya ɗaga mishi yana ci gaba da tafiyar a hankali sabida har yanzu maransa a ƙulle take, duk da ya soma jin salama, maybe maganin ne ya soma aiki,
Wurin motan suka nufa Sadiq ya buɗe masa ƙofa ya shiga,
Sannan shima ya zagaya ya shiga ya kunna Motan

Maryamu na jin motsin su amma sam ta ƙi ɗagowa bare ta kalle su, tana kwance a kan kujerar ta rufe fuskarta da gyalen jikinta, tana jin Sadiq na kiran sunan ta amma sam ta ƙi tanka masa,
Har suka ƙarisa gida sai da ta tabbatar da yayi packing Motan; before ta miƙe zaune tana buɗe kofan, ledojin siyayyanta ta kwasa ta fita ta rufo motan, ko juyawa bata yi ba tayi cikin gidan ta shige

Sadiq kuma shi ya zagayo ya buɗe wa SHAREEF ƙofan sabida ganin ya ƙi fitowa, yace, "zaka iya tafiyan ko in taimaka maka?"

Sai lokacin ya buɗe ido, wanda ya rufe su tun shigansa cikin motan, sun ɗan kaɗa alamun yana cikin wani hali, kansa ya girgiza masa alamun a'a, yayinda ya zuro ƙafafunsa waje ya ƙarisa fice wa, ledan maganin yana hannunsa ya nufi cikin gidan

While Sadiq kuma sai da ya tsaya daukar masa Jakansa da wayansa, sannan ya haÉ—a da nasa ledan na siyayya; sannan ya bi bayansa

Babu kowa a falon da SHAREEF ya shiga, don haka kai tsaye sama ya haura ya wuce dakin su

Shima Sadiq ya bi bayansa da jakansa, bayan yakai masa ya saka shi ya dauko mishi ruwa,
Amsa mishi yayi ya fita zuwa downstairs, da Momy ya ci karo ta fito daga É—akin Maryamu,
Da sauri yace, "Mom Yaya SHAREEF fa bai da lafiya wlh, daga asibiti ma muke tare muka dawo gida."

"Subhanallah..! Ok bari in duba sa." Tayi maganar tana nufan saman fuskarta cike da damuwa

Shima Sadiq ruwan ya je ya É—auko masa har robber biyu, kana ya nufi É—akin da É—an gudun sa

A falo Momy ta tarar dashi kwance a dogon kujera idanunsa a rufe, kiran sunan sa tayi tana ƙarisa shigowa idanuwanta a kansa

Jin muryan Momyn ne yasa ya buÉ—e shanyayyun idanunsa yana kallonta, sai kuma yayi yunkurin tashi a hankali ya zauna

Zama tayi gefen sa tana kai hannunta saman wuyansa, da damuwa a tattare da ita tace, "me ke damunka SHAREEF?"

Shiru yayi yana kallonta, ganin sun haɗa ido hakan ne yasa ya sunkuyar da kansa, in a cool voice yace, "Mom, zazzaɓi ne kawai, but I'm feeling better."

With dissatisfied tace, "ban yarda ba, ko dai ciwon naka ne ya tashi kake ɓoye wa? SHAREEF ba ka jin magana ko? Ka fi son kullum ka riƙa sanya mu a damuwa? Kai kanka baka huta ba muma bamu huta ba, ka ɗaura wa kanka wahala da kanka sabida rashin jin magana, shikenan iyakan namu addu'a ne tunda baza ka ji magana ba, amma ka sani wlh ko don rashin mana biyayya Allah bazai ƙyale ka ba, dole sai ya jarabbe ka, in zaka canza tunani ka canza, in kuma baza ka canja ba ya rage naka, iyakan mu bi ka da addu'a, Allah ya yaye maka, muna nan muna jiran lokacin da zaka cire girman kanka ka dawo kan hanya."
Sai tayi shiru da ta kawo nan a zancen ta,
Bata sake yin magana ba sabida ganin Sadiq ya shigo cikin dakin
Chapter 33 · 0% Book details