Sashe 40
Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
To Abbanta ma ya goya mata baya tunda shi bai damu ba in har zata je karatu ne, dama tun farko ita ta matsa aka yi auren, to yanzu shi da kansa ya yarje mata ta tafi, idan ta gama sai a yi bikin auren su,
Da kansa ya kira Abokin Dady; Doctor Umar da kuma babban Yayan su Momy, waÉ—anda su suka zo suka nema wa SHAREEF auren ta, don haka su ya samu ya faÉ—a musu halin da ake ciki yanzu, a cewar sa, "idan ta je tayi master's É—in ta ta dawo sai ta tare, in zai iya jira to ya jira ta, domin shi a wurin sa bai da burin da ya wuce ya so abun da Æ´arsa take so."
A lokacin da suka je wa Dady da maganar, yayi shiru ya kasa ce musu komai, amma abun ya ɗaure masa kai kuma ya sha mamaki matuƙa,
Shi yasa da kansa ya samu SHAREEF ya sanar mishi yanda aka yi, tunda Haseena bata faÉ—a masa komai ba har ta koma can Australian
Hankalin SHAREEF ba ƙaramin tashi yayi ba, ya kasa ma ƙwaƙƙwaran motsi bare ya san mai zai yi a lokacin, zuciyarsa kamar zata faso ƙirjinsa don zafi da tuƙuƙin da take mishi, ga zufa na keto mishi jikinsa sai rawa yake yi ransa yayi matuƙar ɓaci, wai mai Haseena take nufi dashi ne? Mai take so a gare shi wanda bai mata ba ko kuma bazai mata ba har ta sauya mishi haka? Taya ya zai iya jure wa kuma ya sake jiran ta har ta gama wasu shekarun before ta tare?
Dady yace mishi, "tun farko abun da muke nuna maka kenan amma ka kasa gane wa, Ni a ganina har da rashin yin mana biyayya shiyasa komai naka ya taɓarɓare haka, ita wacce kake so ga shi ba takai take yi ba, hankalin ta yana can wani wurin, to Ni bazan zura maka idanu kayi abun da kake so ba, ko ka nemo wata matar a ɗaura auren tare dana ɗan uwanka, ko kuma ka amshi zaɓin mu, shawara ya rage naka, ka je kayi tunani, amma ba yanda za a yi mu zuba maka idanu ka ci gaba da zama babu aure alhalin kullum cikin ciwo kake, daga ƙarshe in ka kamu da wani mummunar ciwon dole mu zamu yi jinyar ka, SHAREEF a yanzu umarni nake baka wlh idan har baka yi ɗaya daga cikin abun da nace maka ba, ranka zai yi mummunar ɓaci, zan nuna maka wane ne Ni a wannan lokacin, kallona kawai kake yi baka sanni ba tunda baka san abun da yakamata da kai ba, ita kuma yarinyar tunda baza ta zauna da kai ba, ka sake ta don ban ga amfanin ci gaba da zama da auren ta ba.
Ka tashi ka ɓace min a nan."
Ya daka masa tsawa ransa a mugun ɓace
Da sauri SHAREEF ya tashi ya wuce dakinsu, sabida tashin hankali ma ba ya iya ganin gabansa tafiyar kawai yake yi tamkar zai kifa don sauri, ikon Allah ne kawai ya kaisa cikin dakin su.***
Dayake babu Momy a wurin ta shiga É—aki ta dawo, koda ta dawo Dady ya zayyane mata abun da ke faruwa na zuwan su Doctor Umar da abun da suka faÉ—a mishi, da kuma hukuncin da ya yanke a kan SHAREEF
Ita kanta bata ji daɗin abun ba domin ranta ya ɓaci matuƙa, amma sai tace, "wlh koda SHAREEF ya amince da Maryam baza ta taɓa tarewa ba, tunda tun farko mun nuna mishi abun da ya dace ya ƙi bin umarnin mu, don haka a yanzu ba yanda za a yi mu tauye mata haƙƙinta, yanda take karatun ta cikin kwanciyar hankali haka zata ƙare shi ya je can da tsiyan sa, ita yarinyar da ya zaɓa ya je can ya ci gaba da jiran ta. Ato Ni dai baza a tauye wa Maryam haƙƙinta ba, karatu kuma baza ta bar shi don yanzu ya rasa wacce yake so ba."
"To yanzu mai kike so a yi ne Deeja? Idan ya nuna da ita zai zauna ya haƙura sai kuma mu hana sa Matarsa? To mene ne amfanin zaman da take yi da auren sa wai?"
Shiru tayi tana tsuke fuska, sai tace, "Ni a ganina SHAREEF bazai amince da ita ba har wannan lokacin, abun nufin kawai a raba auren tunda babu lallai babu tilas sai sun zauna tare."
Da mamaki Dady yake kallonta, "haba Khadijah ya za a yi ki ce a raba auren? Taya ya na ɗauko yarinya daga gaban iyayenta sun amince da Ni har suka ba ɗana auren ta, duk tsawon wannan lokacin basu san mai ke faruwa ba, sannan kuma a yanzu in je musu da batun ya sake ta, da wanne idon kike so in kalle su? Ai bazai ma yiwu bane, domin a auren nan babu saki an yi shi kenan, SHAREEF bai isa ya watsa min ƙasa a ido ba, abun da yasa tun farko ban matsa mishi dole sai ya zauna da ita ba, don kawai na ga ita yarinya ce bari nake yi tayi karatun ta ko secondary ne ta gama, ba wai na ƙyale sa haka kawai bane, don haka ki dena tunanin ma auren nan za a raba shi, tunda aka yi shi Insha Allahu sai SHAREEF ya zauna da ita ko ba ya so wlh."***
Kuka SHAREEF ya fashe da shi a time ɗin da ya shiga cikin ɗakin su ya zube a Falon, yayinda ya haɗa kai da gwiwa cikin tsananin ɓacin rai da baƙin ciki ya kasa jure abun da yake ji, hakan ne yasa kukan ya kufce mishi ya kasa dakatar da kansa daga raɗaɗin da yake fama dashi
Hanif na bedroom yana barci, kukan SHAREEF ya farkar dashi, daga inda yake yana jin shashsheƙan kukan sa, wanda hakan ne ya ba shi mamaki da sauri ya sauko ya nufo Falon don ya ga wane ne ke kuka?
For surprise SHAREEF ya gani zaune a ƙasa ya haɗa kai da gwiwa yana gunjin kukan, abun ya mugun ɗaure masa kai, kuma hankalin sa yayi tsananin tashi, da gudun sa ya isa inda yake yana zube wa a gabansa, hannunsa na rawa wajen ɗago kansa da faɗin, "Bro, mene ne hakan? Me ya faru ne? Don Allah ka sanar min ko wani abun ya samu su Momy ne? Why are you craying?"
Ɗakyar SHAREEF ya ɗago kansa yana duban Hanif, idanunsa sun yi wani irin girma ga hawaye yanda suke shatata sun kasa tsaya wa, haka shi kansa ya kasa yin magana sabida yanda jikinsa ke rawa haka laɓɓansa, wani abu ya tokare mishi maƙogwaro ya kasa buɗe baki bare ya yi wa Hanif bayanin da yake son yin masa
Wanda shi kuma hankalin sa ƙara tashi yake yi duk ya bi ya dame sa da tambayoyi, gaba ɗaya ya ruɗe domin tunda yake bai taɓa ganin SHAREEF yana kuka wi-wi haka ba, gabansa buga wa yake yi don babu abun da bai bijiro masa a cikin zuciya ba, so yake yi ya tashi ya je ya duba su Momy ko wani abun ne ya same su, amma kuma ya kasa sai tambayar SHAREEF yake yi hankalin sa a matukar tashe
"Hanif ban san yanda zan yi ba, Haseena ta cuce Ni ta gama dani." Sai yayi shiru ya kasa ci gaba da maganar illa rufe idanuwansa da yayi har yanzu suna tsiyayar da ruwa
Da mamaki Hanif kuma yake kallonsa, sai yace, "i don't understand you Bro, mai Haseenan tayi kuma?"
Ɗakyar ya buɗe bakinsa da suka yi masa nauyi laɓɓansa suna kerma; har ya iya koro masa labarin komai
Yayinda tausayin sa ya cika zuciyar Hanif, amma sai ya maze yace, "to mene ne abun damuwa Bro? Wai sabida hakan ne ka zo kana wannan kukan; haba Brother da girman ka? Ina ga ai kamar yau ne zata ƙare karatun ta kuma dawowa gare ka. Sai ka jira ta kawai."
Wani kallo SHAREEF ya watsa mishi wanda yasa dole yayi shiru yana murmushin gefen baki,
Sai kuma ya taɓe baki yace, "ai gaskiya na faɗa maka."
Jiki a sanyaye SHAREEF yace, "I know gaskiyar su Momy ne, abubuwan da suke faÉ—a min, a yanzu dai na san cewa Haseena ta dena so na, ba na gabanta."
Sai ya ɗago jajayen idanunsa ya zuba wa Hanif da shima ya ƙure sa da kallo, cikin takaici da ɗacin zuciya yace, "but har yanzu ina jin ta a raina, soyayyarta a kullum ƙaruwa yake yi na kasa haƙura da ita, please help me bro I don't know how to remove her from my heart, I want to forget her forever, please help me."
Yanda ya ga yana tsiyayar da hawaye ba ƙaramin tausayin sa yake ji ba, da sauri ya kama hannayensa biyu ya haɗa da nasa ya dunƙule su, yayinda suke kallon idanun juna, murya a sanyaye Hanif yace, "addu'a kawai zaka riƙa yi har Allah ya yaye maka soyayyarta, a yanzu dai babu amfanin ci gaba da sonta, wurin Allah zaka nemi taimako Bro tun kafin lokaci ya ƙure maka, ka sani cewa idan ka ci gaba da zama a haka kana ɓata wa Iyayenmu baza ka taɓa ganin dai-dai ba, You know a koyaushe ina faɗa maka har alhakin Maryam zai iya bibiyan ka muddin baka gyara tsakanin ku ba, ita ce wacce ta dace da kai, da ita yakamata ka zauna don ita ce masoyiyarka na haƙiƙa, soyayyar da take maka har ta iya sadaukar da wani abu mai muhimmanci a gare ka, amma ka kasa fahimtar zuciyarta, kayi tunanin yanda kake jin ƙuncin nan; haka itama take fama dashi, kai namiji kenan a yau ga shi kana kuka a kan wata, to bare Ita Mace mai rauni, Bro koda baza ka so ta ba don Allah ka cire ƙiyayyarta a zuciyarka, mai ta taɓa maka da zafi da har kake jin zaka muzguna mata don kawai ta nuna maka ƙauna?"
Sai yayi shiru yayinda idanuwansa suke ci gaba da yawo a cikin na SHAREEF