← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 75

Sashe 7

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hakan ba ƙamarin mamaki ya ba Hanif ba, duk yanda aka yi akwai wani abu da ke damun Amra, wanda ganin wannan mutumin ya haddasa mata shiga ruɗani nan take, duk ta sukurkuce babu natsuwa a tare da ita, shiru ya ɗan yi na wani lokaci ya gaza tafiya, actually har cikin zuciyarsa ya damu da ita, a ɗan kwanakin nan da tunanin ta yake kwana yake tashi, ji yake yi tamkar ya soma sonta a cikin zuciyarsa, amma har yanzu ya kasa gasgata wa, idan har sonta yake yi taya ya zai fara isar da saƙon sa gare ta? Wanne irin soyayya zasu yi tana kurma? Ta ina zai fara? Gaskiya yana matuƙar jinta a ransa koda soyayyar ne bai san ta inda zai fara ba, shiyasa ya bama kansa lokaci don ya gane shin da gaske ne soyayyarta ne a cikin zuciyarsa; ko kuma tausayi ne kawai? Duk da natsuwarta da kamun kanta su suka ja ra'ayinsa gare ta har yake iya jin wani abu a tattare da ita, tana da shiga rai ne, komai nata yayi mishi domin ba ƙaramin burge shi take yi ba,
Motansa ya ja ya nufi hanyar gida ransa duk a jagule, da tunanin halin da zai shiga har ya bayyana ta a wurin Iyayensa, mai zai faru idan sun san tana da laluran rashin magana?
Har yakai gida tunanin Amra ya tsaya mishi a rai

Momy da Sadiq ya samu a falon suna zaune suna kallo,
After ya shigo sai da ya samu wuri gefen Sadiq; before ya yi wa Momy sannu da gida,
Sadiq shima yayi masa welcome back

Momy bayan ta amsa take cewa, "yau SHAREEF ya bar ka da aiki, ban san meyasa yau ya ƙi zuwa ba ya wuni a daki, a tunani na bai da lafiya ne yace min lafiyarsa lau, kawai bai jin zuwa ne, Dadyn ku ma ya yi masa magana amma ya ƙi zuwa, na san maybe ya faɗa maka ko wani abun ne ke damun sa?"

Kallonta yayi yace, "A'a Momy, bai sanar min ba, nima dai na zuba ido in ga ko zai zo but na ji shiru, amma na san lafiyan ce maybe gajiyan Australia ne bai huce ba."
Ya ƙare maganar da ɗan murmusawa

Inda Momy kuma ta taɓe baki tare da mayar da hankalin ta a kan TV, take cewa, "ta yiwu, tunda tun jiyan a haka ya dawo babu walwala, daga can ya samu matsalar sa zai juye mana shi a nan."

Dariya Hanif yayi yana miƙe wa ya nufi hanyar upstairs, "Momy ina Dady ne?"

"Yanzun nan ya fita wlh, ina tunanin wurin Doctor Umar ya tafi don da shi na ji suna waya."

"Ok." Yace yana wuce wa saman,
ÆŠakin su ya nufa ya tura kofan ya shiga da sallama

SHAREEF da ke kwance a saman dogon kujera, daga shi sai singlet da gajeren wando, idanunsa a rufe ya nannaɗe hannayensa a ƙirji kamar mai barci, sai dai jin sallaman Hanif ɗin ne yasa shi buɗe madaidaitan idanuwansa masu cike da damuwa; har sun kaɗa sun yi ja sabida tunanin da ya ƙwazzafi kansa dashi,
Bai amsa mishi sallaman ba illa bin sa da kallo da yayi kamar yana neman wani abu a jikinsa

Shi kuma zama yayi yana ajiye jakarsa tare da furta, "wash Allana! Na gaji wlh, aiki babu dad'i, shine ka ƙi zuwa ko?"

Ɗauke kansa yayi yana mai mayar da idanunsa ya rufe, tare da ƙoƙarin juya kwanciyar sa ya juya mishi baya

"Wai Bro baza ka cire damuwar yarinyar nan a tare da kai ba? Ban san meyasa ka damu kanka da ita ba, since ka gano wannan laifin mai girma duk da na san abun da ciwo, yanzu mataki yakamata ka ɗauka, ko rabuwa ko kuma kayi haƙuri ku ci gaba daga inda ku ka tsaya, tunda dai na san soyayyar da kake mata bazai sa ka rabu da ita ba ko?"
Ya ƙare maganar da son jin mai zai faɗa

Ai kuwa tuni SHAREEF ɗin ya tashi zaune yana faman kallonsa, fuskarsa cikin damuwa kamar zai yi kuka yace, "tabbas bazan iya rabuwa da Haseena ba, abun da tayi min ya matuƙar min ciwo cus ban taɓa expecting haka daga gare ta ba, amma kuma har yanzu bata kira Ni ba, ina ta zaman jiran kiran ta domin ta bani haƙuri amma shiru."

Dariya Hanif yayi, "wai kana nufin sai ta baka haƙuri sannan zaka haƙura? Mene ne amfanin hakan?"

Wani kallo SHAREEF ya watsa mishi before yace, "sabida girman laifin da tayi min mana, kana tunanin Ni zan bi ta duk da wannan laifin but Ni zan sake bibiyan ta? Duk da ina sonta sai na hukunta ta, wlh da zan iya rabuwa da ita da tuni na rabu da ita, domin zuciyata baza ta taɓa samun sukuni ba tunda na kama ta tana cin amanata, a ɗan wannan lokacin ji nake yi kamar zan mutu sabida baƙin cikin abun da tayi min, amma na kasa cire ta a rai, ina son Haseena! son da ba na tunanin zan iya ma wanin ta."
Sai ya buga tagumi yayi shiru idanun nan sun kaÉ—a sun yi jazur

Shiru Hanif yayi yana kallonsa, yayinda har a ransa haƙiƙa yana tausayin ɗan uwansa, wai wannan wacce irin soyayya ce? Shi a ransa sam ba ya son Haseena da SHAREEF; domin har ga Allah bai ga dacewar su ba, ya fi ganin dacewar su da Maryamu tun sanda ya soma ganin ta, ita ce zata fi dacewa da shi, ko don tausayinta da yake ji tana fama da dakon soyayyar wanda babu ita a gabansa, yana jin har abada in har akwai Haseena; tabbas bazai taɓa son Maryamu ba,
Kamar yayi mishi maganar ta haka yake ji, amma kuma sai ya fasa gwara ya bar sa da abun da ke damun sa, amma shi a ganin sa mai ya rage kuma, in har ya samu Haseena da wannan cin amanar bai kamata ya ci gaba da sonta ba, tunda zina ta aikata ta ba wani kanta bayan shi, ko don wannan ya ci ace soyayyarta ta fice daga ransa, amma kuma wai zaman jiran ta ba shi haƙuri yake yi, lallai kam! SHAREEF yayi nisa ba ya jin kira.

🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆

_____A cikin kwanakin nan SHAREEF ya zauna da damuwar jiran kiran Haseena kamar yanda yake hasashen zata neme shi ta ba shi haƙuri, amma abun mamakin shiru babu kiran ta

Ita kuma tana can cikin wani hali a lokacin, tun mafarkin da tayi na gane-ganen mutane; yanzu kuma abun sai ya zame mata jiki, abubuwan da take gani a mafarkin ta sun soma tsorata ta, tun tana ɓoye wa sabida abun yana ɗaure mata kai, sabida yanayin mafarkin da kullum ta kwanta sai ta ga mutanen suna shan jini ana yanka mutane a zuba jinin a basu; suna sha suna waƙe-waƙe da sirkulle, a firgice take a kwanakin, ga Nana da take gani a cikin mafarkin, itama tana tare da mutanen, ita take kamo ta koyaushe ta bata jinin nan ta sha, kuma bata taɓa mata musu ba,
Abun ya soma tsorata ta shiyasa ta kasa ɓoye wa ta sanar da Nanan abun da take gani a mafarkin ta

Nana kuma tayi murmushi tace, "zata faÉ—a mata sirrin da bata sani ba a yanzu."
Don haka ta zauna ta feɗe mata biri har wutsiya na sanya ta a ƙungiyar su da tayi na Secret society, a cewar ta, "sabida tana sonta da ƙaruwa, komai take so a ƙungiyar zata samu, hatta SHAREEF in har tana so ta sarrafa shi yanda take so, to wannan damar ta ne duk abun da take so zata mallake shi in har zata yi wa ƙungiya biyayya."

Haseena ta ruɗe ta kiɗime da jin bayanan Nana, hankalin ta yayi matuƙar tashi wanda yasa lokaci guda ta faɗi ta sume sabida tsananin firgici da jin abun da ya fi ƙarfin ta, ƙwaƙwalwan ta ta gaza ɗaukar halin da take ciki

Ita kanta Nana ta tsorata ganin yanda Haseena ta sume babu nimfashi a jikinta, amma sai ta daure ta zuba mata ruwa ta farfaɗo nan take, tana kallonta tace, "You should calm your mind, stop putting fear in your heart, nothing will happen to you, nayi haka ne don taimakon ki sabida ina sonki da ƙaruwa a cikin mu."
Sai ta riƙo hannunta tana murmusawa ta ƙara da faɗin, "haba babe, na san kina son ki ji dadin rayuwa, you will be happy to find yourself among us, whatever you will get you don't have to worry, just calm down."

A firgice Haseena take kallonta, idanunta har sun sauya launi tsaban tashin hankali ga hawaye sun cika mata idanu, cikin tashin hankali ɗakyar take iya maganar ma, don tsoro Nanan take bata, da sarƙewar murya tace, "No, a'a, ba na so, Ni ba na son wannan harkan, bazai yiwu ba, taya ya za ki saka Ni a cikin ƙungiya ba tare da amincewa ta ba? That may not be possible, I can't; just remove Me, I don't want to."

Smile Nana tayi tace, "already na saka ki a ciki yanzu kin zama ɗaya daga cikin mu, kawai haƙuri za ki yi amma baza ki taɓa iya fita ba, If you think you can leave, there is a condition".
[31/03, 4:32 AM] نفيسة OumƊahira: 🌱🌱🌱🌱🌱

       *SHAREEF*
           _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱

_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*Littafina na kuÉ—i ne, ki biya ki karanta, zaku iya samu na a kan wannan numban wayan. 07065334256.*

__________
*BOOK2*
_______________*PAGE5*
_____Da sauri ta haÉ—iye yawun tsoro; idanunta a dalale a kan Nanan É—akyar ta furta, "for what?"

Murmushi Nana tayi tace, "sharaɗin shine ba a fita a ƙungiyar mu sai dai mutuwa, in kin shiga kin shiga kenan, in kuma kina so ki fita sai dai ki mutu."
Chapter 7 · 0% Book details