Sashe 69
Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Koda suka shiga suka tarar da Maryamu a kwance a ƙasa ta rikito, sauran Nurse's din sun yi ƙoƙarin kama ta amma sun gaza sabida yadda take fizga tana wani irin ƙara kamar wata mai farfaɗiya, idan tayi miƙa ɗaya sai dukkansu sun kasa dawo da ita dai-dai sun kasa nanƙwaya ta, tana son miƙe wa amma ta gaza sabida ƙafanta, sai wani irin ihu take yi mai firgitar da mutane
Tunda suka ga haka sai Dady ya É—auki waya da sauri jiki na rawa ya kira Malamin da ke duba ta, ya ba shi information na abun da ke faruwa tare da faÉ—a masa asibitin da suke a yanzu haka,
Bayan ya gama wayan sai ya nufi inda suke ana ƙoƙarin ɗaura Maryamun a kan gadon amma sun gaza, har da SHAREEF shi ya riƙe ta gam ya ƙi sakinta,
Dady yace, "please doctor a samu a yi mata taimakon gaggawa before Malamin da ke duba ta ya zo, ina tunanin ciwonta ne na aljanu suka tashi don dama tana da matsalar, idan ya zo sai yayi mata koda addu'a ne."
Jin hakan sai Likitan ya haÉ—a wani allura da ke sa barci, ya zo dai-dai wurinta ya saka SHAREEF ya buÉ—e mata cinyanta, after ya buÉ—e ya tsira mata alluran zuwa jikinta
A ɗan ƙanƙanin lokaci ta dena mutsu-mutsun da take yi, sai numfarfashi da take faman yi ta nanƙwaye kanta ta sama ta sanƙare a jikin SHAREEF ɗin, still har yanzu jinin da ke zuba a hancinta yana ɗiga a yanzu kaɗan-kaɗan, sai shaƙuwa take yi idanunta suna koma wa fari kamar ranta zai fita, sai kuma baƙin idanun su dawo dai-dai haka suke yi, duk fuskarta zuwa jikinta ya ɓaci da jini, duk wanda ya riƙe ta sai da ya samu jinin ya ɓata shi, musamman SHAREEF da farar rigansa tayi sharkaf
Likitan yace mishi, "ya É—auke ta zuwa kan gadon ya É—aura ta."
Hakan kuwa yayi daƙyar ya ɗauke ta, amma abun tausayin duk jikinta ya kanannaɗe, yatsun hannayenta sun yi kamar na kuturwa bakinta a karkace, haka kafafunta a nanƙwaye har da mai ciwon,
Duk yanda suka so su miƙar da ita sun kasa,
Ƙarshe dole suka barta a hakan har suka jira Malamin ya zo, ita kuma har lokacin barcin bai ɗauke ta ba tana nan a yanda take tana nishi da fitar da ƙara mai ƙarfi, sai ta saka ƙara sai kuma can tayi lagwab ta koma fitar da gurnani
Ba su Momy kaɗai ba, hatta Likitocin hankalin su ya tashi da ganin halin da take ciki, sun tausaya mata matuƙa don daga gani tana matuƙar jin jiki; har da masu zubar mata da hawaye, abun gunun tausayi
Sai da Malamin ya zo sannan aka samu aka sauko da ita tunda shi ya bada umarnin a mayar da ita ƙasa,
Sannan ya zauna dukkansu suma suka samu wuri suka zauna suna kallon yanda ya soma mata karatu, a wannan halin ya jima yana mata karatu yana tofa mata addu'o'i waÉ—anda suka soma tasiri a jikinta
Nan take ta fashe da kuka tana ƙara mai firgitar wa, jikinta ya ci gaba da kanannaɗe wa kamar kuturwa
Malamin ya saka aka riƙe ta ya ci gaba da mata karatu tsawon lokaci,
Tukun suka samu ta soma magana bayan Aljanin kanta ya hauro kanta
Cikin kuka take sambatu da maganganu cikin tsananin wahala da wani irin gurnani, ta soma zayyane musu abun da ke faruwa, a cewar Aljanin, "wacce take son kashe ta suna son shanye mata jininta ne, amma sun kasa cin galaba a kanta, yanzu haka suna can suna tsaface-tsafacen su zasu kashe ta, amma bazai bar hakan ba, idan ba a taimaka an ceci Maryamu ba a koyaushe zata iya mutuwa in jininta ya ƙare, zasu kashe ta."
Hankalin kowa a ɗakin ya yi ƙololuwar tashi musamman su Momy da suka fi sanin me ke faruwa, kuma a yanda suka ga ta jigata tana wani irin kuka da gurnani a yanzu jinin nata na zuba sosai
Sai Malamin yayi saurin cewa, "don Allah ya faÉ—a musu komai domin su san ta yanda zasu yi su taimaka mata kar su ci galaba a kanta, su waye suke son aikata hakan a gare ta?"
Nan fa Aljanin ya soma koro musu bayani tsab ya tona asirin Haseena da abun da take shirin aikata wa a yanzu
Zuciyar kowa buga wa take yi sun tsorata da abun da Aljanin ke faÉ—a, abun tamkar almara,
Amma Malamin tuni ya ci gaba da mata wasu addu'o'i ya dafe kanta yana ci gaba da tofa mata,
An É—auki lokaci kafin ya samu jinin ya tsaya kuma a nan take ta dena motsa wa sai dai numfarfashi da take sauke wa,
Malamin ya sanya aka samo mishi ruwa ya ci gaba da tofa addu'o'i a ciki tsawon lokaci, sannan ya sanya SHAREEF ya shafe mata kaf jikinta da shi,
A hankali komai nata ya soma dawowa daidai sai kuma kamar barci ya ɗauke ta; ta ci gaba da sauke nishi mai ƙarfi har da munshari,
Malam yace, "ku ɗauke ta a mayar da ita gida don babu amfanin zamanta a nan; tunda an san matsalarta, abun da yakamata muyi yanzu mu san yanda zamu yi mu hana ita Matar aikata abun da take ninya, tunda ƙungiyar asiri ne a koyaushe zasu iya cin galaba a kanta su kashe ta, addu'o'in da nayi mata zasu taimaka mata sosai wajen tsare ta baza su taba cin galaba a kanta ba, amma insha Allahu yanzu zan koma gida akwai tanadin da zamu tashi musu tsaye domin ganin bayansu, dole ne a tarwatsa su idan ba haka ba zata cimma manufarta, ku ɗauko ta mu tafi."
SHAREEF shi ya É—auke ta sannan suka fita har da Likitan ya bi bayansu,
Aka bar sauran Nurse's din da suke wurin cike da al'ajabi da tausayin Maryamun, don dukkansu sai da suka zubar mata da hawaye, basu taɓa ganin abu makamancin irin hakan ba koda wurin masu aljanun ne, lallai wannan yarinyar tana shan wahala, jikinsu yayi sanyi matuƙa, kenan a koyaushe za a iya kashe ta tunda tsafi ake son yi da ita, lallai duniya abar tsoro ce, hankalin su ya tashi matuƙa jikinsu ya sake yin sanyi
Har wurin Mota Likita ya raka su sannan yayi musu addu'ar samun lafiyarta yana sake ce ma Dady, "idan ta samu lafiya a kira sa a faÉ—a masa don Allah, ko don hankalin su ya kwanta, duk yanda ake ciki a faÉ—a mishi."
Malam a gaba ya zauna tare da Driver, su kuma suka shiga baya suka wuce gidan,
Bayan sun kai gidan; Drivern ya É—auki Malam a bisa umarnin Dady ya wuce dashi gida,
Su kuma suka shigar da ita cikin gidan aka kwantar da ita a saman Kujera,
Dukkansu sun yi jugum sun kasa ma magana sai kallon Maryamun suke yi,
Sai kuma Momy ta matsa ta ci gaba da mata addu'o'in tana tofa mata
While SHAREEF na gefe idanu sun kaɗa sun yi jazur; ya kafe Maryamun da idanu amma a ransa baƙin ciki da tsanar Haseenan ne ya cika sa, yana son tashi ya je ya ɗauki mataki a kanta amma ba ya son jirgawa wurin Maryamu, domin gani yake yi kamar in ya tashi za a iya kiransa a ce mishi Maryamu ta mutu,
Don haka yana nan manne da ita ya gaza jirgawa
Ana haka sai ga Hanif ya zo gidan gaishe ta, ya zo ya tarar da wani tashin hankalin da ya fi wancan, don Momy ta ba shi labarin abun da ke faruwa hankalin sa ya tashi matuƙa, yace, "gaskiya Dady a san abun yi kar yarinyar nan ta hallaka Maryam, ƙungiyar asiri kuma? Wannan ai babban tashin hankali ne komai zasu iya aikata wa, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!"
Ya hau salati cikin ruÉ—u
Yayinda su Dadyn suke taya shi zuciyoyin su cike da ƙunci,
Dady yace, "basu da matakin da zasu ɗauka a kanta amma komai zai zo ƙarshe insha Allahu, su jira Malam ya dawo su san mai za a yi, tunda ya faɗa musu za a iya karya ƙadarin ƙungiyar da ƙarfin addu'a, za a iya ganin bayansu."
Sai ga driver ya shigo a lokacin ma, da saƙon Malamin da ya tsayar da shi ya ba shi wani magani a kwalba mai ƙamshin gaske, yace mishi, "a shafa mata yanzu a dukka jikinta."
Malamin ma sai ga kiran nasa ya shigo a wayan Dady, bayan ya amsa ya sake mishi bayani sosai sannan yace, "su kasance da addu'a dukkansu, itama su ci gaba da mata suna tofa mata, yanzu haka ya tara almajirai da wasu malamansu zasu tashi tsaye wurin musu addu'a don ganin bayansu, insha Allahu kafin dare komai zai zo ƙarshe, in har basu bar yarinyar ba dukka sai sun shiga bala'i don baza su taɓa samun sukuni ba, zasu rusa ƙungiyar tasu".
[11/05, 9:10 PM] Ù†Ùيسة OumÆŠahira: 🌱🌱🌱🌱🌱
    *SHAREEF*
      _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱
_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_
*Littafina na kuÉ—i ne, ki biya ki karanta, zaku iya samu na a kan wannan numban wayan. 07065334256.*