← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 75

Sashe 28

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kama ta yayi yana É—an murmushi sabida jin sunan da ta kira sa dashi, domin har yanzu ita bata bambance su sabida kamannin su, in har ba ta gansu wuri É—aya bane, kuma dama can ba wani sanin su tayi ba,
Ɗaukar ta yayi daƙyar; ya taho inda su Ammee suke zaune,
Zama yayi a kan sofa before ya kira sunan Ammeen fuskarsa a sake

Ta amsa shi tana murmusawa da faÉ—in, "kana can kana ta barcin ka abun ka, Aunty tace baka da lafiya ne?"

Amsa mata yayi before ya gaishe ta

Ta amsa tana tambayarsa jikin nasa?

"Na ji sauƙi Aunty."

Yusaira itama gaishe shi tayi,
Ya amsa ta a takaice yana kallonta

Ammee tace, "ga shi nan duk ka rame SHAREEF, gaba ɗaya ka sauya kamanni, Ni farko ma ban gane ka ba wlh; ka zama ustazun ƙarfi da ya ji wato?"
Ta ƙare da ƴar dariyan ta

Momy kuwa taɓe baki tayi tace, "kema dai kin faɗa, ya ɗaura ma kansa abun da ya fi ƙarfin sa, kullum a kwance yake yana fama da kansa."

Kallonsa Ammee tayi tace, "SHAREEF wai yaushe ne ita yarinyar zata gama karatun ne?"

Shiru yayi, sai kuma yace, "i don't know Aunty."

"Kana nufin baka sani ba?" Tayi maganar da mamaki

GyaÉ—a kansa yayi batare da ya kalle su ba, idanunsa a kan Na'ilah da ya É—aura a jikinsa tana jan masa gemu,
Ba wai bai sani bane; bai son su ja zancen ne tunda ba ya son maganar

"Hmm lallai! To Allah ya kyauta."

Momy tace, "Amin dai, dama kin dena biye masa a kan abun haushin nan, don Ni kwata-kwata ba na son a yi maganar yarinyar, yayi ta zama a haka har Mahadi ya bayyana, akwai ma maganar da zamu yi; bari Dadyn su ya fito sai mu zauna muyi magana."

Daga haka suka ci gaba da hiran su a tsakanin su,
While Yusaira tuni ta mike ta wuce kitchen wurin su Maryamu

Yayinda SHAREEF yana zaune a wurin yana É—an wasa da Na'ilah, jefi-jefi yana biye mata a kan surutun da take mishi,
Har zuciyarsa kuma tunanin yarinyar da ya gani É—azu yake yi; don ta tsaya mishi a rai

Lokacin kuwa sai ga Maryamu ta fito tana yarfe hannayenta,
Kamar an ce ya É—ago kai suka haÉ—a ido da ita,
Tsira mata ido yayi, while itama hakan ne wacce ta kafe sa da nata manyan idanun suna kallon-kallo a tsakanin su,
Kamar shuÉ—ewar seconni biyar tuni ita tayi saurin janye nata idanun tana mayar wa a kan su Ammee,
Yayinda ta tako a hankali ta nufo wurin kanta tsaye cikin takun ta mai fizgar hankali

SHAREEF kuwa ya kasa dauke ido a kanta duk da yana tunanin kamar gizau take mishi, gani yake yi kamar ita kamar ba ita ba, sai da ya ji Momy ta ambaci sunan ta before ya gasgata abun da zuciyarsa ke hasasowa,
Take ya sake ware madaidaitan idanunsa a kanta

A lokacin itama ta sake kallon inda yake, karaf suka haÉ—a ido dashi, wani kallo ta watsa mishi kafin ta janye nata idanun luuu kamar zata yi fari cikin wani irin yanayi mai É—aukar hankali

Wanda sai da ya ji gabansa ya faɗi; jikinsa yayi wani irin yamm har sai da yayi zillo kamar zai tashi tsaye; sabida yanda ya ji wani irin abu ya tsikare sa tun daga tafin ƙafansa zuwa ƙwaƙwalwan sa, take ya lumshe idanunsa yana sake bude wa a kanta, sai dai tuni ya ɗauke idanun ya sake rufe su sabida son gasgata abun da idanunsa suke son nuna masa,
Shiru yayi yana sauraron Ammee wacce take magana yanzu

"Maryam É—auko min wayata a É—akin Aunty, na baro ta a cikin Jakana kar a kira ni."

"Ok." Tayi maganar tana yin gaba zuwa steps

Ɗago kai SHAREEF yayi direct ya bi bayanta da kallo, wanda bai san lokacin da zuciya ta rinjaye shi ya mayar da ido a kanta ba, cus surar jikinta ba ƙaramin mugun fizgarsa tayi ba, wanda hakan yasa ya kasa danne abun da yake ji ya ɗaga kai yana faman bin ta da ido; cike da mamakin sauya mishi da tayi fiye da tunanin sa

Daga Momy har Ammee duban SHAREEF suke yi, domin dukkansu suna son su ga halin da zai nuna idan ya ganta, tabbas ba ƙaramin mamaki suka sha ba da suka ga yanda ya kafe ta da idanu ko ɗauke su ya ƙi,
Sai da suka kalli juna cike da mamaki suka sake mayar da idanunsu a kansa,
Basu yi masa magana ba har sanda suka ga yana shirin jiyowa a sa'ilin da Maryamun ta ɓacewa ganin sa,
Da sauri suka dauke ganin su a kansa suna kama wani zancen

Shi kuwa tuni ya lumshe idanunsa yana jin yanda zuciyarsa ke luguden bugawa,
Wai anya yarinyar da ya raina ne ta zama haka a ɗan ƙanƙanin lokaci; ko kuma wata ce?
Zuciyarsa ta kasa yarda da cewan ita ce don ba ƙaramin mugun sauya mishi tayi ba a ido, abun da bai sani ba rashin kallonta da bai yi ne a baya yasa yake ganin kamar an sauya ta, shi a baya baƙar fuskar kawai yake iya hangowa da kuma ƙauyancin nata, amma lokaci guda ga ta ta zama santaleliyar budurwa abun sha'awa, uwa uba yanda ta haɗa ƙira mai matukar fizgar sa, domin ba ƙaramin yanayi ya shiga ba tsaban yanda yake ganin tana tafiya komai nata na rawa, har ji yake yi kamar ciwon sa zai tashi,
Take a nan ya miƙe zumbur yana sauke Na'ilah a kan jikinsa, ya nufi hanyar steps ɗin da nufin bin bayanta, don a yanda yake ji bazai iya dakatar da kansa da kwadayin tozali da ita ba

Baki sake suka bi sa da kallo, don babu wanda yayi yunƙurin tsayar dashi,
Sai da suka ga ya haye saman before suka bushe da dariya, domin ba ƙaramin mamaki halin da SHAREEF ya shiga ya basu ba, tun yanzu ji be yanda ya koma daga ganin Maryamu

"Wai Aunty kin ga abun da nake gani kuwa? tun ba a je ko'ina ba mutumin namu yana son afkawa, ko dai gizau abun ke min? Ban zaci haka ba wlh."

Momy dariya tayi tace, "lallai namiji bai da ta ido, tun ba a je ko'ina ba kenan ya fara bamu mamaki, ai ban taɓa tunanin zamu iya ganin sauyi a nan kusa ba, ki ce komai zai zo mana a sauƙi kenan."

"Wlh Aunty na ji daɗi sosai da na ga wannan yanayin da ya nuna, alamun nasara kenan, bare ƴar namu tubarakallah Masha Allah! Na tabbata babu namijin da zai kalle ta bai faɗa tarkon ta ba, ba ƙaramin tausayinsa nake ji ba musanman yanda na ga ya rame ɗin nan, Allah yasa dai kar ya ci gaba da mana taurin kai, Ni a ganina in har ya nuna yana son zama da ita kawai ta tare; da mu rasa shi."

Girgiza kai Momy tayi tace, "ai bazai ma yiwu ba, ko ya nuna yana so wlh sai Maryam ta gama karatun ta, babu gudu babu ja da baya, ya je can ya nemi wata ko ya je wurin ɗaya Matar tasa, Ni fa ba ƙaramin burge ni Maryam tayi ba da ita ta iya kame kanta a gaban shi, ban taɓa tunanin haka ba, lallai Maryam tayi hankali."

Ganin su Yusaira sun fito daga kitchen; shiyasa suka sauya hiran nasu.
***

_____Cikin zafin nama Maryamu ta ƙarisa saman ta shige cikin ɗakin Momy, sai da ta shiga ta rufe ƙofan before ta jingina bayanta da ƙofan tana sauke ajiyar zuciya, hannunta a saman ƙirjinta ta runtse idanunta, numfashi kawai take sauke wa kamar wacce tayi tseren gudu,
Ganin sa ba ƙaramin famo mata da zuciya yayi ba, a tunaninta ta birne soyayyarsa na har abada, amma ganin sa, ganin sa sau ɗaya tak ya ruguza mata dukkan wani natsuwa nata, ba ƙaramin dauriya tayi ba wurin cije wa har ta iya kama kanta ta kasa mishi kallo na uku, har yanzu akwai soyayyarsa da ke matuƙar wahalar da ruhin ta, sai dai yanda ta ɗauki alkawarin baza ta taɓa nuna wa a fili ba, hakan yasa ta danne komai ta binne tunaninsa a ranta, amma koyaushe yana cikin zuciyarta, domin soyayyarsa tamkar wata rubutacciyar ƙaddara ce da babu yadda za a yi ta cire ta na har abada,
A yau kallon fuskarsa tamkar ya famo mata gyambon ta ne, fuskarsa kawai take iya hango wa a cikin idanunta,
Buɗe idanun tayi tana jan numfashi kamar zata shiɗe, ƙoƙarin daidaita kanta take yi amma yanda jikinta ke rawa gabanta na matuƙar buga wa; sam natsuwa ta gagare ta, ƙafafuwan ta sun yi mata nauyi wanda yasa ta kasa motsa wa a wurin, rufe idanunta ta sake yi yayinda fuskarsa ta ƙara bayyana a cikin ƙwayar idanunta, ba ƙaramin sauya mata yayi ba, kamar ba SHAREEF ɗin da ta sani ba,
Tsawon mintina biyar tana a wurin ta kasa kataɓus, sai da tayi matukar jarumta before ta daidaita kanta ta nufi wurin Jakan Ammee ta dauki wayan, sai ta tsaya tana sauke numfarfashi a kai -a kai tare da furta, "calm down mana Maryamu, ki natsu don Allah, kin yi alkawarin baza ki taɓa bari ya gane akwai soyayyarshi a cikin zuciyarki ba, kin yi alkawarin za ki kama kanki ki zama Mace mai aji, yanzu ba Maryamun da ya sani bane da, ki kwantar da hankalin ki kin ji ko? Ki kama kanki ba na son shiririta."
Tayi maganar a fili kamar tana maganar da wani,
Sai kuma ta saki ƙayataccen murmushi tare da cije laɓɓanta,
Direct ƙofa ta nufa zata fice

A lokacin SHAREEF na tsaye a bakin ƙofan, tun hawan sa ya zo ya tsaya a wurin ya ƙi gaba ya ƙi baya, burin sa kawai ya sake sanya ta a ido, tunaninsa ma ba ya jikinsa bai san abun da yake shirin aikata wa ba, kawai dai umarnin zuciyarsa yake bi

Tana buɗe ƙofan suka kusa cin karo don bata taɓa tunanin zata tarar da mutum a wurin ba, kawai fitowa tayi gadan-gadan amma sai tayi saurin jan burki kamar wacce ta ga abun tsoro ta zaro manyan idanuwanta waje tana kallonsa
Chapter 28 · 0% Book details