Sashe 66
Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ni bazan iya barin ta ba, babu wanda ya isa ya hana Ni taraiya da ita, domin ita Matata ce, na aure ta bazan sake ta ba, ina sonta ina ƙaunarta tun tana ƙaramarta, don haka bazan iya barin ta ba, domin idan aka ce za a raba mu komai zan iya yi."
Sai ta ja numfashi tana ci gaba da haki numfashin ta na ɗauke wa kamar zata shiɗe, tana ɗaga ƙafanta ɗaya da diddigen ya kumbura
Girgiza kansa yayi yana jinjina ƙarfin halin sa, sai kuma yace, "yanzu faɗa min waye yake son cutar da ita? Ko akwai wasu ne bayan kai a jikinta?"
"A'a babu wasu, domin kowa ya san Ni ne Mijinta bazan taɓa barin wani ya shige ta ba, kuma bazan taɓa bari a cutar da ita ba, shima Mijinta don na ga tana matuƙar ƙaunarsa ne shiyasa na bar shi, domin na so cutar dashi amma na gagara ganin halin da take shiga a kansa, amma kuma sabida yanzu za a kashe min ita, kun shammace ni kun yi mata aure batare da sani na ba, amma idan wani abu ya faru da ita daga shi har wacce take son kashe min ita don shi; sai na kashe su bazan bar su ba, a taimaka a cire min wannan ƙarin da ke ƙafana, ana cutar dani da ita, idan ba a cire ba zata iya rasa ranta."
Shi Malam ma sai lokacin ya kula da ƙafan, haka suma su Momy, amma hankalin su yayi matuƙar tashi duba da abin da Aljanin ke faɗa, to mai hakan ke nufi? Waye yake son cutar da ita saboda SHAREEF ɗin su?
Shi kansa SHAREEF duk ya É—imauce don jin abun da ke faruwa, har jikinsa ya É—auki rawa sabida tashin hankali da tunanin waye ya aikata hakan duk sabida shi?
While Malam tuni ya ɗago ƙafan yana kallo, sai kuma yace, "wannan ciwon mene ne? Zamu so mu san ciwon mene ne sabida mu san mai za a yi mata? Ka faɗa mana abun da ka sani akai da wacce take son cutar da ita in har ba kai ka aikata mata hakan ba?"
Kuka ta fashe dashi, sai tace, "don Allah ku taimaka ku cire mana muna azabtuwa, ƙarin Kunama ne da cizo, an yi ne don kashe ta amma nayi ƙoƙarin ceton ta wanda aka ɗana min a madadin ta, nayi alƙawari idan ku ka cire min zan faɗa muku wace ce domin tana da hatsarin gaske."
Jin hakan yasa Malam ya koma duba ƙafan yana kallo, gaba ɗaya ta kumbura tayi suntum har yatsun sun shige sun zama kamar babu yatsu,
Sosai abun ke basu tsoro sabida ganin yanda ƙafar take hauhawa kamar flower,
Dole Malam yace, "sai an yi mata alluran ƙarin cire Kunama kuma an bata magunguna, don haka a hanzarta a kira Likita."
Dole SHAREEF ya É—auki wayansa yayi kiran Doctor Abbas, don shi kaÉ—ai ne zai iya taimaka musu yanzu ya nemo musu maganin sai yayi mata alluran,
Don haka ya kira sa a waya yayi masa bayani tare da kwatancen inda zai same su
Shi kuma Malam ya ci gaba da tofa wa wurin addu'a duk wani taimako ya yi ƙoƙarin bata, har an ɗaure ƙafan sabida yana yin gaba yana hawan mata can saman ƙafa
Doctor Abbas da ya iso shi yayi mata alluran har guda uku, a nan take,
Sannan aka bata wasu magungunan ta sha
Daga nan kuma sai ta soma barci bata sake sanin inda kanta yake ba
Tabbas sun shiga damuwa kuma sun tausaya mata,
Bayan ganin haka sai Malam yayi musu bayani da cewa, "akwai abun da ke son cutar da ita ne amma Allah ya tsare, don haka gaskiya dole kuyi taka-tsan-tsan a kula da ita wurin taimakon ta da addu'o'i, don irin hakan zai iya bada damar da ciwon ta zai dawo sabo ya riƙa tashin mata sabida halin da ta shiga, kuma idan hakan ta kasance zata sha wahala ne, kun ji abun da Aljanin ya faɗa duk yanda aka yi akwai wacce take son cutar da ita, dole a ɗauki mataki idan ba haka ba abun zai yi muni, Allah ya tsare gaba a kula da ita sosai, akwai addu'o'in da zan bata ta riƙa ƙoƙarin yi sannan da wanda za a shafa mata a wurin, insha Allahu zai saɓe sai a haɗa mata dana asibitin har Allah yasa ta samu lafiya."
Doctor Abbas shi dayake yayi musu sallama ya tafi, su kaÉ—ai suka rage a wurin Malam na kora musu bayani, sannan ya haÉ—a musu da magungunan ya sallame su
Dady yayi ta mishi godiya, daga ƙarshe ya ba shi ladan aiki tare da wanda za a yi wa almajirai sadaka a ci gaba da taya su addu'a
SHAREEF shi ya É—auke ta ya mayar da ita cikin mota, sannan suka tafi zuwa gidan su,
Tunda can Dady yace, "ya wuce da su kawai sabida a kula da ita."
Ƙarshe dai shima SHAREEF a can ya kwana,
Dayake tun a daren suka yi waya da Hanif ya zayyane masa komai, don ya kasa hakura ya bari sai da safe, abun ya tsaya mishi a rai sabida tunanin wanda yake son cutar mishi da Mata, shi dai bai san wa zai zarga ba
Amma tashin farko Hanif sai yayi tunanin ko dai Haseena ce, don zuciyarsa ita take zargi, don haka yace masa, "wlh Ni ina kyautata zaton Haseena ce zata yi maka haka, duk wani zargi ya nuna ita ce, ita ce take son cutar da ita sabida soyayyar da take maka, duk da zato zunubi ne amma babu mahalukin da zai maka haka sai ita, bare dama mun fara zargin koda sihiri a tattare da ita da take maka; sai ga shi abu ya fito fili."
Shi kansa SHAREEF ya amince matuƙa da zancen Hanif, sai yanzu tunanin sa ya basa haka, amma in ko haka ne tabbas zai ɗauki mummunar mataki a kanta, bai ma taɓa tunanin haka take ba sai yanzu da take ƙoƙarin bin sa da sharri, lallai dole su san abun yi
Dayake dare ya tsala sosai, dole suka yi sallama basu gama tattaunawa ba, yayinda Hanif yace masa, "zai shigo da safe sai su san abun yi."
Shi kuma SHAREEF kasa haƙura yayi ya nemo numban Haseena wanda yasa a Blacklist, sai ya cire ya kira ta
Ring ɗaya sai kuwa ta ɗauka tunda tana a farke ba barci take yi ba, suna abun da suka saba, a tunanin ta shirin su ne yasa ya kasa haƙura sai da ya kira ta, don haka cikin yanga da kisisina tace, "dear, kai ne a daren nan? Kamar ka san ina kewarka na gaza sukuni ina jiran amsar ka."
Takaici da baƙin cikin maganganun ta yasa shi daka mata wani irin tsawa yace, "rufe min baki muna-fuka, ashe dama haka kike mai bak'ar zuciya mara imani da tausayi? Ban san yaushe kika sauya ba Haseena amma ba haka kike ba, asirin ki ya kusan tonuwa sabida tunanin cewa dole sai kin mallake Ni, haba abun da mamaki a yanda na kasa natsuwa zuciyata take son min yawo da hankali duk a kanki, ashe da dalili tunda ba ki bar Ni haka ba, but ki ji duk abubuwan da kike shirya wa a kaina kike son cutar min da Mata, kin yi ƙoƙarin ki kashe ta sabida ina tare da ita don mummunar nufin ki a kaina." Cikin fushi da ɗaga murya ya ƙara da cewa, "idan har kika kuskura kika cutar min da Maryama, na rantse da Allah sai na wulaƙanta miki rayuwa, kuma duk abun da kike shirin aikata wa ki ci gaba da aikata wa bazan taɓa ƙyale ki ba duk ranan da dubun ki ta cika."
Sai ya ja tsaki ya kashe wayan yana wurgi dashi,
Yayinda ya kasa zaune ya kasa tsaye yana tunanin matakin da zai dauka, lallai duniya abun tsoro ne, dole ya san yanda zai yi ya ceci kansa daga sharrin ta, don idan ta gusar masa da hankali komai zai iya aikata wa bai sani ba, tunda a yanda yake jin ƙaunarta ɗazu zuwa yanzu kuma ya ga bambanci, dole ne akwai wani abu, addu'a shi ne takobin sa domin tsira da mutuncinsa; musamman a kan mummunar ƙudirin ta a kansa,
Don haka bai ga ta zama ba sai ya tashi ya shiga toilet ya ɗauro alwala, abun da tunda yake bai taɓa cewa ga ranan da ya tashi sallan dare ba, Ibadan da bata dame shi ba sai yanzu da ya soma dawowa hayyacinsa, ya san cewa shi ne takobin sa, duk wanda ya tsaya ga Allah ɗaya tak ya koma gare sa da ibadu, babu wani mahaluki da ya isa ya cutar dashi, kuma babu abun da zai nema ya rasa in har ya miƙa buƙatar sa ga Allah, a wurin sa kaɗai zai nemi taimako a kan wannan mummunar yanayin da bai san ta inda za a farmake sa ba.
🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆
Yayinda a wannan daren Haseena ta shiga tashin hankali tsantsa sabida jin furucin SHAREEF, abun da É—aure kai, ko in ce sun sha mamakin yanda aka yi ya gane Haseena nan take, har kuma da maganar kokarin kashe masa Mata, to taya ya kenan hakan ta faru?
Daga ita har Nana tambayar da ya shige musu duhu kenan,
Kuma hakan na nuni da cewan har yanzu tana raye bata mutu ba, don haka ko a nan dole akwai babban al'amarin da ya wakana har take raye bata mutu ba
Take a nan suka yi amfani da ƙarfin tsafin su suka bincika komai, duk da basu san ya aka yi ba amma sun gane Maryamu tana raye
Hankalin Haseena idan yayi dubu to ya tashi, yayinda ta ɗauki alwashin wlh in har bata samu SHAREEF ba, to babu wata Mace da zata same shi, in har bata ci galaba a kansa ba sai dai ta sadaukarwa da Ƙungiyarsu shi, daga shi har Matar tasa da ta kasa kashe ta,
Kamar yanda ta ɗauki alwashi tun farko to sai ta aikata, sai dai su mutu dukka amma kishi bazai barta tana gani SHAREEF ya zauna da wata bayan ita ba, ko mene ne sai tayi don ƙwato shi.
[09/05, 6:53 PM] Ù†Ùيسة OumÆŠahira: 🌱🌱🌱🌱🌱