← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 75

Sashe 61

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai Haseena tayi saurin cewa, "Umma a kan me zata tafi wani wurin a wannan tsohon daren? Ita fa baƙuwata ce, in har tabar gidan nan to tare zamu bar gidan but babu inda zata je."

Zuciya ce ta ɗibi Umma tsaban ɓacin ran maganganun Haseenan, ta nufe ta da sauri ta janyo ta ta soma jibga tana cewa, "Ni za ki gaya wa magana irin haka don ubanki? Au don ba ki da hankali ina cewa tabar gidan kike maganar za ki bi ta? Kashe ki kawai zan yi in huta domin baza ki jawo mana abun kunya ba Haseena."

Wani mari takai mata; amma sai Nana ta tare ta tana ture ta ta faɗi a ƙasa, cike da isa da taƙama tace, "Mom kar ki sake taɓa ta cus zan dauki mataki a kan hakan, bazan iya jura ba."
Sai ta mayar da hankalinta kan Haseena tana rarrashinta har da shafa mata fuska before ta sumbace ta tana rungume ta

Umma fa hankalinta ya ƙara tashi, ganin baza ta iya jure wa ba sai ta miƙe ta fita da saurin ta, kai tsaye kitchen ta nufa ta ɗauko muciya ta dawo babu zato tahau kansu da duka su dukka,
Haka take zagin su tana cewa, "yau zata yi maganin iskancin su, sai tayi ajalin su gaba É—aya, da dai Haseena ta jawo mata abun kunya gwara ta kashe su ta huta."

Daƙyar suka ƙwace muciyan, Haseena da kanta ta ture Umman don ranta ya ɓaci sabida abun da tayi musu, musamman haɗa su da tayi ta duka, cikin rashin kunya da fetsarewan ido tace, "wlh Umma sai kin biya dukan nan da kika yi, bazan yafe ba tunda ban miki komai ba, ai rayuwata ce Ni naga zan iya abun da nayi ninya, ina da ƴanci duk abun da nake so, haka kawai ki kama dukan mu?"

"Haseena Ni kike faÉ—a wa haka?"

"Eh Umma na faÉ—a É—in, baza ki hana Ni abun da nayi ninya ba, a kan Honey zan iya yin komene, don ba ki san yadda muke da ita bane, don Allah ki fice a É—akin nan tun kafin in miki mummunar rauni."

Cikin ɓacin rai itama Nana tace, "Babe abun da wannan Matar tayi min ba a taɓa min a rayuwata ba, idan ba ki ɗauki mataki ba Ni zan ɗauka, because I will never let her go."

"I don't care what you want to do to her, I won't say anything." Haseena tafaÉ—a tana cika tana batse wa

Kuka Umma ta saka abun takaici ya ishe ta, yau ƴar cikinta ne take mata wannan rashin kunya haka? Mai suka aikata wa Allah da ya jarrabe su da wannan iftila'in? Tabbas wannan mummunar rana ne da baƙin ciki zai kashe ta, yadda zuciyarta ke mata zafi ta kasa tsayuwa tana shirin faɗuwa, sai ta juya tana kuka ta nufi hanyar fita, har ta buɗe kofan kuma ta juya tace, "Haseena wanne irin laifi muka aikata miki da kika saka mana da wannan mummunar hukuncin? Shikenan bari Abbanki ya dawo tunda Ni na kasa ɗaukar mataki a kanki, in har mu muka haife ki ke jinin mu ne mu'amalar ki da wannan yarinyar in har ba ki datse shi daga nan ba; Allah ya isa ban yafe miki ba, kuma za ki ga mai zan yi akai."
Ta fita batare da ta É—auki wayanta da ta sake ta tun shigowarta na farko ba

Haseena kuwa ko a jikinta ta rufe musu ƙofa ta koma tahau ba Nana haƙuri; sabida ganin ranta ya ɓaci sosai

Nana tace, "kin san bazai yiwu mu bari ta fallasa mana asiri ba ko? Domin a cikin secret ɗin mu babu buƙatar a san mai muke aikata wa, hakan yana jawo wa ƙungiya matsala gagaruma, We don't think she knows this, so we have to take action."

Haseena was silent, then she said, "What do you mean now?"

Kallonta tayi, sai tace, "You know, what we should do, otherwise she will reveal the secret to us, and it will not be possible for anyone to hear more."

Ita kanta Haseena ta san da haka, tunda a yanzu ta fahimci cewa tun farko neman da Nana tayi mata duk cikon aikin ƙungiya ne, dole sai suna neman junan su, kuma hakan shine babban sirrin su wanda shi ke kawo musu ci gaba sosai a ƙungiya, ta hakan ne suke samun kuɗi da kuma ƙarfin tsafin su, babu daman su fasa wannan harkan, duk wanda yake ciki yana mu'amala da ko waye in har ya kwanta musu a rai, kuma a duk karshen wata ana samo yara irin ƙanana Ogan su yana amfani da su a kashe su sannan a sha jinin su, duk wannnan sirrin su ne, shiyasa ɓatan yara yake yawa sosai a duniya, don ko ina suna samo Yara domin cikan burin su, sannan idan suna aikata wannan harkan wani ya gansu hakan na ƙara rage wa ƙungiyar su ƙarfi, kuma abun na tasiri su samu matsala har asirin su ya tonu, shiyasa duk wanda ya gani hukuncin sa kawai kisa ne batare da sun bari ya sanar da wani ba; bare asirin su ya daɗa bayyana ga jama'a,
So Haseena ta san da haka, duk da sonta da Mahaifiyarta bata da wannan damar da zata hana a kashe mata Uwa, don ta san ko sun bar ta ita kuma Umma baza tayi shiru ba, sannan ƙungiya zata san da haka tunda zasu soma ganin matsaloli.
***

Umma bayan ta koma ɗaki sai ta nemi wayanta ta rasa, ta so a lokacin ta kira Abba ta faɗa masa, tuna inda tabar wayan sai tayi zaman ta a gefen gado tana ci gaba da matse hawaye, abun duniya ya bi ya ishe ta gani take yi kamar an sauya musu Haseenan su, Haseena baza ta taɓa yin abun da wannan tayi ba, lallai kam tura ƴarsu wata ƙasa bai musu amfani ba tunda ta kwaso abubuwan da ba a san ɗan musulmi dashi ba, abun ma ya fi ƙarfin ta wai lesbian Mace da Mace, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...! Wannan wanne irin bala'i ne? Wanne irin kuskure suka aikata haka? Tabbas akwai laifin su amma dole ne su ɗauki mataki, mummunar mataki kuwa, domin tseratar da ƴarsu,
Don haka ta miƙe ta shiga toilet zata ɗaura alwalan sallan isha'i da bata yi ba,
Ga dare yayi amma ba don haka ba da ta fita; koda Uncle É—in su ne ta sanar dashi, amma kuma da tayi tunani sai ta ga maganar ba na sanar wa jama'a bane, domin su zasu kwana a ciki tunda idan maganar ta yaÉ—u sun shiga uku, abun kunya ne wannan

Ta shiga toilet tana cikin alwalan ne, ta gama kama ruwa tana wanke hannu, sai ta ji cikinta ya murɗa, kamar wasa kuma abun ya soma fin ƙarfin ta, dole ta dakata ta riƙe cikin nata gam tana salati da sallallami,
Kafin wani lokaci jikin Umma ya ɗau zafi sai karkarwa take yi nan da nan ta zube ƙasa don ƙafafuwan ta sun gaza ɗaukar ta,
Kamar an ɗaure ta haka take ji; daga nan kuma sai numfashinta ya ɗauke abun kamar a mafarki ta tsinci kanta a wani baƙon wuri da ta kasa gane mai ke faruwa da ita, duniyar ta juya mata ta zamar mata sabuwa sai ganin wasu jajayen abubuwa take yi da ta kasa gane mene ne,
Jima wa kaɗan kuma sai ta soma jin maganganu but ba ta fayyace maganganun su waye, kuma bata san mai ake faɗa ba, tamkar an ɗaure ta komai nata ta kasa motsi dashi, kamar kanta ma a ƙasa yake ƙafafunta a sama shiyasa ba ta iya tantance mutanen wurin,
Sai kuma daga baya ta soma jin murya kamar na Haseena a kusa da ita,
Natsuwa tayi sosai ta tsayar da zuciyarta daga tsananin tsoron da ya addabe ta, domin tantance muryan Haseenan, don zak irin muryan take ji

"Umma, bani da yadda zan yi ne dole ne ta sa hakan, kin gano abun da ya fi ƙarfin ki, nima haka bazan iya taimaka miki ba, amma ina baƙin cikin ganin wannan rana da nayi sanadiyyar mutuwarki da ke da ƴar uwata Haajara."

Laɓɓan Umma suna motsi tana son yin magana amma ta kasa, komai na jikinta kamar ya saki ne baza ta taɓa iya amfani dashi ba, kuma sarai ta gama jin zantukan Haseenan da ke fitar mata bibbiyu amma ta gaza gane inda maganar ta dosa, to wai shin aina take ne? Daga shiga toilet kuma sai hakan ya kasance da ita? Mai ke shirin faruwa da ita ne?
Daga ƙarshe maganganu sun sake yin yawa ta kasa bambance mai ke faruwa, sai kuma ta ji kamar an ɗaura mata abu a cikinta, kamar kuma ya lume ne, a hankali ta soma ganin jini na ɓulɓulo wa ta hancin ta da bakin ta, kafin ta tantance mai ke faruwa rai yayi halin sa

Sai da suka gama tsaface-tsafacen su before a dawo da gawan nata a cikin É—akin nata,
Inda Haseena babu ko nadamar abun da ta aikata, domin zuciyarta a ƙeƙashe take musamman tun lokacin da ta fara shan jinin ƴar uwanta, bare yanzu kuma jinin mahaifiyarta shima ya shiga jikinta da ƙarfin tsafi, hakan yasa zuciyarta ta ƙara tauri babu wani ɓurɓushin imani,
Ita da kanta ma ta kira Abbanta ta zayyane mishi halin da ake ciki, bayan ta nuna tashin hankalin ta da kukan da ta saka mishi na ƙarya, ta faɗa mishi, "Umman bata da lafiya ta faɗi a ƙasa babu numfashi a tattare da ita."

Ba ƙaramin tashi hankalin Abba yayi ba, ya ruɗe gaba ɗaya yace mata, "tayi maza ta kaita asibiti. Ta ɗauki driver ya kaisu asibiti shima a daren nan zai dawo."
Bayan ya kashe wayan sai ya kira ƙaninsa ya sanar masa halin da ake ciki domin ya bi bayansu
Chapter 61 · 0% Book details