Sashe 73
Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da Likitan ta zo ta tarar da Hanif cikin É—akin yana tsaye gaban gadon Amran yana mata sannu, duk ya gama diririce wa daga shi har ita sun fice a hayyacin su,
Dayake ta gane sa tunda a nan yake kawo Amran awo; kuma ita take duba ta, don haka ta kira sunan sa tana tambayar sa halin da ta shiga?
Nan ya fayyace mata komai yana sanar mata, "shima ya tashi ne ya ganta a wannan yanayin, but bai san lokacin da ta soma naƙudan ba."
Likitan sai ta bukaci, "ya fita zuwa waje zasu duba ta."
Dole ya fita ba don ya so ba, yana ta sintiri a bakin ward É—in har sanda ya ji kiran wayan Dady, da ya duba ya ga shi ne sai ya amsa call É—in ya sanar masa inda suke
Ba a fi minti biyar ba suka ƙariso wurin shi da Momy, hankalin su a tashe yake gaskiya don haka suka hau tambayarsa halin da Amran take ciki?
Ya sanar musu, "an shiga da ita ana duba ta."
"To Allah ya raba lafiya, amma hankalin mu ya tashi Allah ya sauke ta lafiya, baka sanar da Mahaifiyarta ba ko?"
A cewar Momy da ke maganar cikin tsantsan damuwa
Shi kuma yana share gumin fuskarsa yake gyaÉ—a mata kansa, yace, "a'a, ban sanar musu ba, Dady kawai na samu damar fada mishi."
Dady yace, "to kira maza ka sanar da Mamansu, gwara su zo nan su san halin da Æ´arsu take ciki ko zasu taya ta da addu'a."
Hakan ne yasa Hanif yayi kiran numban Mama ya shaida mata, "suna asibiti yanzu haka Amra zata haihu."
Kusan mintina ashirin sai ga likita ta fito duk fuskarta a dame, da alamun akwai matsala koda suka hangi face ɗin ta, ilai kuwa nan take shaida musu, "gaskiya naƙudan yayi nesa da yawa, akwai sauran awannin da yakamata takai before ta haihu, amma ta rigada ta galabaita already jininta ya zuba da yawa, kuma ana buƙatar ta samu ƙarfi gaskiya idan ba haka ba baza ta iya haihuwa da kanta ba, don haka za a ƙara mata jinin yanzun nan."
Sosai suka ƙara shiga tashin hankali, dukkansu salati suke yi zuciyoyin su na cike da tausayin Amra
Hanif ne yayi saurin cewa, "idan da hali; a je a duba nasa in zai yiwu a ɗiba a ƙara mata."
Likitan tace, "to ba damuwa su je."
A tare suka tafi dashi da ita
Ko kafin su dawo su Mama sun zo ita da Afra da Salma dukka suka taho, suma kansu hankalin su ba ƙaramin tashi yayi ba, musamman da suka zo Momy take musu bayanin halin da ake ciki, "yanzu ma haka an je gwada jinin Hanif ne za a ƙara mata, mu ci gaba da taya ta da addu'a Allah zai sauke ta lafiya Insha Allahu."
A can kuwa É—akin haihuwar Nurse É—aya aka bari tana kula da Amra wacce duk ta gama fita a hayyacin ta, Nurse din sai mata sannu take yi tana É—an danna mata ciwon don ta samu relief
Ita kuma ciwo da azaba ya hana ta sukuni, don ji take yi tamkar za a ɗaɗɗake mata bayanta da Kwankwason ta, numfashinta daƙyar yake fita, bata kuka amma hawaye sai gudun tsere yake yi a idanunta, tayi waja-waja ta jigata tamkar wacce tayi kwana biyu tana naƙudan, a ranta ji take yi tamkar baza ta iya kaiwa anjima da rai ba, yadda take jin ciwon na sukanta tana jin kamar mutuwarta ya kusanto ta ne, burinta kawai ta sanya Hanif a idanunta, tana son faɗa masa wasu kalmomi da ke ranta sai dai babu bakin magana, hakan ne yasa ta fashe da wani irin kuka mai cin rai sabida babu halin ta sanar da Nurse abun da take so,
Can kuma sai ta ɗago tana kallon Nurse bayan da ta ji ciwon ya ɗan lafa mata, daƙyar take iya ganin ta ma sabida hawayen da ke gudu a idanunta, nan ta soma mata bayani da hannu tana nuna mata tana son abun rubutu, sai kwatanta mata da hannu take yi cikin kuka
Ita kuma Nurse bata gane ba sai faman tambayarta take yi, sai kuma daga baya kamar ta gane tace, "rubutu kike so ki yi?"
Da sauri ta jijjiga mata kanta tana ƙoƙarin miƙe wa, duk da daƙyar take iya motsa jikinta saboda azaba
Da sauri ita kuma Nurse din ta ciro memo a jikin aljihun riganta, Allah yasa akwai har da Bairo sai ta taimaka mata ta tashi zaunen; ganin tana ƙoƙarin zama ne, sannan ta miƙa mata tana sake mata sannu
Daƙyar ta riƙe Bairon ta soma rubutun cikin rawan jiki, gaba ɗaya kuka kawai take yi tana rubutun zuciyarta a karye take sabida a halin da take ciki, tana jin a ranta baza ta iya rayuwa ba, tana buƙatar barin ma Mijinta wasiyya, don haka ta rubuta, "don Allah Mijina ka yafe min, ba na jin ciwon nan zan iya tashi sabida yanda nake ji a jikina, amma in har ban fito da raina ba ka yafe min abubuwan da nayi maka, na so nayi rayuwa da kai mai tsawo sabida in saka maka da abun da kayi min, amma.." sai ta yanke daga nan ta ƙara da faɗin, "idan na haifi abun da ke cikina ya rayu, don Allah ka bama ƴar uwata Afra kyauta domin na mallaka mata halak malak, kuma don Allah ka aure ta ta cike maka gurbina cikin zuciyarka, ina sonka Yaya Hanif."
Daga nan ta dakata da rubutun sabida ya ci ƙarfinta, mika wa Nurse din tayi sai dai bata da bakin da zata iya mata bayanin wanda take so ta bata
Ita kuma kamar ta sani sai ta soma tambayarta tana lissafa mata wa za a ba? Iyayenta ta soma ambata amma Amra ta girgiza kanta, tana cewa, "Ko Mijinki zan ba?"
Da sauri ta gyaɗa mata kanta cikin halin ciwo tana riƙe ƙugunta
Hakan ne yasa Nurse ta tusa takardan a aljihu tana mai riƙe ta ta ci gaba da mata sannu
Babu jima wa Likitan ta zo tare da wata Nurse da ke rike da ledan jinin guda biyu,
Nan aka soma ƙoƙarin ɗaura wa Amran
While itama kuma wacce ta ba takardan sai ta fita da sauri don ta duba Hanif ta miƙa mishi takardan, ganin babu shi cikin su Dady dole ta dawo cikin dakin suka ci gaba da taimaka wa Amran,
Tunda a lokacin Hanif É—in yana É—akin da aka É—iba mishi jinin,
Likitan tace masa, "dole sai ya É—an huta before ya taso."
Shima SHAREEF yana cikin su don a yanzu ya ƙariso, dole a yanzu ya taho yabar Maryamu tunda already tana gidan su Momy a yanzu, itama cikinta ya shiga watan haihuwa, kuma akwai su Yusaira sun zo hutu, don haka ya barsu a tare ya zo asibitin,
Duk suna waje sun yi cirko-cirko babu wanda ya jirga a wurin; sai Dady da ya je yayi sallan asuba ya dawo
Su Momy kuwa sai daga baya ne ma suka je suka yi tunda sun ji shiru har yanzu ba a fito musu da wani bayanin ba
Gaskiya ba ƙaramin wahala Amra ta sha ba a wannan halin da take ciki, haihuwa ya ƙi zuwa duk ɗiba mata wannan awannin da suka yi, kuma shiru kamar an shuka dussa, sannan ga shi duk da jinin da aka ƙara mata dogon naƙudan yasa duk ta gama galabaita nishi ma dakyar take yi bare tayi wani yunkuri,
Abun ya É—aga wa kowa hankali, tun asuba ake abu É—aya ga shi har kusan la'asar yanzu, sumanta uku sai numfashin ta ya É—auke sai ya dawo can kuma,
Su Dady ne kaɗai suke fita asibitin su je su dawo, don shima SHAREEF koma wa wajen Maryamu yayi tunda ta kira sa ta ɗaga mishi hankali, tana ta kukan shagwaɓa wai, "dole sai ya kawo ta ta ga Amra."
Ya rarrashe ta ta ƙi haƙura, shiyasa ya tafi can wajen ta
Hanif kuwa ba ya jirga wa a asibitin ko kaɗan, yana nan yana ta faman yi mata addu'a hankalin sa ya fi na kowa tashi a wajen, har hawaye yake zubar wa a ɓoye sallah kaɗai ke tayar dashi
Daga karshe dai likitocin sun nemi a sanya hannu a yi mata aiki, tunda suna ganin hakan shi ne maslaha, dama already haihuwar fari yawanci yana kawo matsala da dama, wasu rashin buɗe wa ne da kuma wahalar da suke gamuwa dashi wanda ya fi ƙarfin tunanin su, ga tsoron da ke tattare da su, shiyasa sai su kasa haihuwa da kansu, don haka Amra dai ba sa tunanin zata iya haihuwa da kanta gaskiya,
Shiyasa suka nemi Mijinta ya sanya hannu za a shigar da ita É—akin Theatre
A lokacin da aka basu damar su ganta gaskiya sun tausaya mata matuƙa, don ba ta iya bambance ma mutane sabida wahalar da take sha, kallonsu kawai take yi tana motsi da bakinta tana hawaye, amma kwata-kwata ba ta a cikin hayyacinta
Su Afra sai kuka suke yi sabida halin da suka ga yar uwansu, don har su an shiga da su sun ganta,
Kowa sai addu'a yake mata yana fatan a fito da ita lafiya
Hanif kamar bazai sake ta ba daƙyar ya bari aka kaita ɗakin da za a yi mata aikin, yana nane da ita har sai da aka tashi yin aikin before a ba shi umarnin fita
A sannan ne Nurse din nan ta zo ta ba shi takardan da Amra ta rubuta, don ita kanta ta manta kai ya É—auki zafi sai yanzu da ta ganshi, don haka ta rugo a guje tana mishi magana,
Bayan ya tsaya take ce mishi, "kai ne Mijin Matar nan ko?"
Kai ya É—aga mata idanunsa sun yi jazur sun fice a hayyacinsu, don a lokacin yanda yake ji a ransa bazai iya yin mata magana ba, shi kansa ji yake yi kamar Amra zata tafi ta bar shi, don jikinsa yayi sanyi a halin da ya ganta, ciwon nata yayi worst